
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu!
Cikin girmamawa gare ku shugabanni da Jami’o’in Lafiya na ƙasa ta baki ɗaya.
Na ɗauki alƙalamina ne domin na kiraye ku akan wani ganganci da kantafi da rayukan al’umma da na ga hukumar haraji ta Nkjeriya ta yi a wani asibiti mai zaman kansa a birnin Kano, wato ‘Best Choice Specialist Hospital’ da ke unguwar Gadon Ƙaya kan shataletalen Tal’udu.
Wasu daga cikin marasa lafiya da wasu iyaye sun kawo wa jaridar Alfijir labarai ƙorafi akan yadda jami’an hukumar tattara harajin suka zo tare da jam’ian tsaro da bindigogi su na musu barazana akan sai dole sun tashi sun fita daga cikin asibitin bayan bala’in da suke ciki na rashin lafiya, ga shi kuma sun yi yawo wurare da dama a Kano sun rasa inda za a iya samun gadon kwanciya musamman a ɓangaren larurar da ta shafi yara da jarirai sai nan ɗin!
Babban abin takaicin ma shine wasu daga cikin likitoci da ke Kano da ma wasu jahohin sun tsunduma yajin aiki akan haƙƙoƙinsu, maimakon hukumar ta yi aiki da hankali wajen taimaka wa al’umma domin jin-ƙan su, a’a sai ƙoƙari take wajen ƙara nakasa rayuwar waɗannan marasa lafiyar dake asibitin ko kuma ma hallaka su!
Matsalar haraji dake tsakaninku da asibiti matsala ce da ta shafe ku, ba abinda ya shafi waɗanda suka zo neman lafiya asibitin bane.
Don haka muke kira ga shugabanni na wannan ƙasa tamu mai albarka, da hukumar kare haƙƙin bil’adama kan wannan cin zarafin da aka yi wa al’umma da akawo musu ɗauki cikin gaggawa.
Ku kuma hukumar tattara haraji, ku dubi Allah ku canja hanyar da zaku bi wajen neman haƙƙinku, don inda haƙƙinku ya ƙare nan fa na wasu ya fara.
Idan da ƴaƴanku ne ke zuwa asibitin ba na talakawa ba, da ai ba zaku yi hakan ba!
Kukan Kurciya Jawabi Ne!
Daga
EDITAN JAJIDAR ALFIJIR LABARAI
Mai Biyayya A Gare ku
