N423b: El-Rufa’i ya musanta zargin ya na da hannu a rashawa, ya sha alwashin rantsewa da Ƙu’rani

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI

Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa’i ya tabbatar da cewa babban dalilin shigar sa harkar siyasa ita ce don ya yi wa al’umma aiki, ba wai ya sauya akalar dukiyoyinsu ba.

El-Rufa’i ya faɗi hakan ne a yayin wata hira a gidan Rediyon Freedom a Kaduna inda ya yi watsi da zargin sauya akalar kuɗaɗe a gwamnatinsa, ya na mai cewa a wadace ya ke kafin ya fara jagorancin jihar.

A kwanakin baya ne Majalisar Dokokin jihar ta zargi gwamnatin El-Rufa’i da sauya akalar kuɗaɗe da adadinsu ya kai Naira biliyan 423.

Saidai, tsohon gwamnan ya musanta zargin inda ya ce hakan wani nau’i ne na siyasa.

Ya kuma ce, a shirye ya ke ya rantse da Al-Ƙur’ani don tabbatar da bara’arsa ga zargin da ake masa.

Hakan na zuwa ne yayin da El-Rufa’i ya ƙudiri aniyarsa ta koma wa harkar siyasa yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

By Babaji