Buhari: Don Allah ka dakatar da Gwamnan CBN

Daga DAKTA ALIYU U. TILDE

Shawarar da Ɗan Majalisar Tarayya, Alhaji Gudaji Kazaure, ya bayar na dakatar da gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, tana da kyau sosai kuma tana bisa ƙa’ida. Kai, ma iya cewa ma ta zama babbar buƙatar ƙasa a yanzu.

Idan ba a ɗaga kaza daga makwancinta ba, ba za a san me fukafukanta suka boye ba. Don haka, ƙa’ida ce mai kyau idan za a yi bincike mai zurfi musamman idan wanda yake shugabantar wurin yana nuna tirjiya da ƙoƙarin danne gaskiya, to a dakatar da shi.

Shugaba Buhari ya sa Honarabul Kazaure aikin bincike a CBN saboda wani labari mai ta da hankali da ya ji. Ya ce kuma Hon. ya ba shi bayanin abinda ya gano kai-tsaye ba tare da ya biya ta kan wani jami’i ba.

Yanzu kwamitin Honarabul Kazaure ya gano wata badaqala ta Dalar Amurka biliyan $171 wacce ba a tava yin irinta ba a Nijeriya. Hon. ya ce kuɗi ne wanda aka ce na masu zuba hanun jari ne amma kuma majahulai. Kwamitinsa ya yanke cewa talakawa ake ta tatsa ta hanyar tara har aka tara su aka yi kwana da su.

Honarabul ya tattara bayanai ya doshi Shugaban ƙasa da su amma dogarin Shugaban ƙasa da aka haɗa shi da shi don iso wajensa ya hana ya gan shi. Jama’a, akwai rina a kaba.

Ya kamata yan Nijeriya su ba wannan magana muhimmanci sosai. $171 billion a zamanin yunwa da rugujewar tattalin arziki ba wasa ba ne. Kuma mun ci sa’a a zamanin Buhari ne. Don haka, dole a matsa a yi abinda ya dace. Kar mu zame kamar kazar da ta kwana a kan dami..

Muna ƙarfafa wa Shugaban ƙasa gwiwa a kan ya buɗe ƙofarsa, ya gayyaci Honarabul Kazaure, ya gan shi, ido da ido, kuma ya mika masa bayanan abinda ya gano, hannu-da-hannu. Abin da ɗaure kai a ce wasu na jikin Shugaba Buhari za su hana Honarabul isa wajensa har sai ya fito bainar jama’a yana roƙo.

Masu bai wa Shugaban Ƙasa shawara da na jikinsa ya zama dole su ba shi shawarar tinkarar wannan ƙazamin lamari da gaske. Magana dai ta fito, fiye da ta Dala biliyan $16 na Obasanjo a Mambila, ko ta $20 billion na Diezani da Jonathan. Ba wanda zai so mulkinsa ya kare da irin wannan badaƙalar a kwance. Dakatar da gwamnan CBN da kammala binciken da gaggawa ya zama dole.

Shi kuma Honarabul Gudaji Kazaure ya san cewa ya burge mu. Ya tabbata ɗanmu ne na asali mara tsoro, mai tsayawa a kan gaskiya da riqon amanar da aka ba shi. Allah ya saka masa da alheri, ya kiyaye mana shi.

Dakta Aliyu U. Tilde ya rubuto daga Bauchi.