Kyakkyawar Jumma’a….

Daga CMG HAUSA

A yayin da ake tunanin ci gaban duniya zai yi rauni sosai a shekarar 2023, a hannu guda kuma ana sa ran tattalin arzikin kasar Sin zai farfado da kuma inganta, har ma ya amfani duniya baki daya.

Idan ba a manta ba, a ranar Juma’ar da ta gabata ce aka kammala babban taron shekara-shekara kan aikin raya tattalin arzikin kasar Sin a birnin Beijing, inda aka tsara ka’idojin raya tattalin arzikin kasar na shekara mai zuwa, da tsara muhimman batutuwan da suka shafi harkokin tattalin arziki na shekara mai zuwa, gami da fadada bukatun cikin gida, da hanzarta gina tsarin masana’antu na zamani, da karfafa hukumomin jin dadin jama’a da kamfanoni masu zaman kansu, da jawo karin jarin waje, da kuma hana aukuwar manyan hadurra na tattalin arziki da kudi.

Bankuna da dama na duniya ma sun yi hasashen cewa, tattalin arzikin kasar Sin, zai samu kyakkyawan sakamako a shekarar 2023, inda Morgan Stanley da Societe Generale, manyan kamfanonin ayyukan hada-hadar kudi na kasa da kasa guda biyu, sun yi hasashen karuwar kashi biyar cikin dari a shekarar 2023. Wannan wani babban albishiri ga duniya baki daya. Kyakkyawar Jumma’a ake ce, tun daga Laraba ake gane ta.

Masana na cewa, za a iya danganta hasashen da ake na samun makoma mai haske a shekara mai zuwa ga managartan matakan yaki da annobar COVID-19 da kasar ta dauka, da ingantattun manufofin ci gaban tattalin arziki, da yanayin da ake ciki a wannan shekara. Fata na-gari aka ce lamari.

Kyawawan matakan yaki da COVID-19 da kasar ta kyautata, za su yi tasiri mai kyau ga tattalin arzikin kasar. Inda ake hasashen samun farfadowar tattalin arzikin kasar cikin sauri a watanni 6 na farkon shekarar 2023, musamman a rubu’i na biyu.

Baya ga sassauta matakan yaki da annobar COVID-19, tare da la’akari da tsayin daka da karfin tattalin arzikinta, manazarta sun yi imanin cewa, tattalin arzikin kasar Sin, zai farfado a shekarar 2023, kuma zai ci gaba da zama abin dogaro, kana muhimmin karfin tattalin arzikin duniya a shekarar 2023. Ai sai an zubar da ruwa a kasa kafin a taka damshi.

Mai fassara: Ibrahim Yahaya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *