Darajar kuɗin Nijeriya daga 2004 Zuwa 2022

Daga AMINU ƊAN ALMAJIRI

Wanda duk ya kalli irin tuƙin da ake yi wa Nijeriya a yau, ya san ana yi mata tuƙin da zai kai ta ga halaka.

Da yawa mutane ban sani ba, son zuciya ne ya sa idan Khalifa Muhammad sanusi II ya yi magana a kan shaanyin tattalin arziki da sha’anin mulkin ƙasar nan suke masa ca! Ko kuwa rashin sani? idan rashin sani ne, sai na ce dama masu hikima sun ce, ‘Ɗan Adam maqiyin abinda ya jahilita ne’.

idan kuwa son zuciya ne, ya kamata kam yanzu su fito su faɗa wa jama’a cewa, a irin duk abinda Khalifa yake magana a kai, wanda suke cewa yana da yawan magana, wanne ne bai faru ba ko yake shirin faruwa?

Mu kalli matsayin Dala daga 2004 zuwa 2022

Soludo a zamaninsa ana canjar duk Dala 1 akan kuɗin Nijeriya 139.6. Duk da ƙara daraja da Dalar ta yi a zamaninsa, canjinta bai wuce duk Dala ɗaya a kuɗin Nijeriya 180.6 ba daga 29 ga Mayun 2004 zuwa 29 ga Mayun 2009.

Khalifa Muhammad Sanusi (II) Bayan kammala wa’adin Soludo shi ne ya zo bayansa, shi a nasa zamanin ma saboda tausayin halin da talakawa ke ciki, wanda buhun shinkafa a wannan lokacin ba ta wuce dubu bakwai ba, amma maimakon Dalar ta ƙara matsawa gaba, sai ta dawo daga canjarta da ake yi a kuɗin Nijeriya duk guda 1 daga 180.6 zuwa 166.1.

Hakan ya faru ne bisa gogewa da sanin makamar aiki da Khalifa yake da ita, wanda tun daga 3 Yuni, 2009 zuwa 2 ga Yuni 2014, talakawan Nijeriya ana rayuwa ne cikin aminci daga kuncin yunwa da talauci, duk da a wannan lokacin rayuwar ana ganin ta yi zafi.

Ƙarshe-ƙarshen wa’adin khalifa Muhammad Sunnusi (ii) a CBN Dalar ta ɗan ƙara daraja kaɗan, shi ma kuma ba komai ya jawo hakan ba sai bashi da aka ciyo, amma duk da haka, a kan yadda ake canzar Dala a zamanin Khalifa, duka naira 1 ce ta ƙaru. Allah ya saka wa Khalifa da alkhairi.

Emefiele, tun daga 3 ga watan Yuni na 2014 zuwa yau da yake a kai, maimakon kuɗin Nijeriya su cigaba da zama a cikin darajarsu, sai da ta kai a yanzu duk Dala 1 ana canzarta a kan kuɗi Naira 800 a yanzu, bayan an bar masa Dalar ana canzar ta duk guda 1 a kuɗin Nijeriya a kan kuɗi Naira 167.

Talakawa a yanzu ba sa buƙatar sharhi a wannan gaɓar, domin kowa yana ji a jikinsa, kowa ya san me ake nufi da darajar Naira da rashin darajarta a yanzu, kowa ya gane abinda tun farko khalifa yake ta magana a kai a kan irin yanayin da ƙasar za ta faɗa bisa irin tuƙin da ake mata, lissafi da hukunci kam ya rage wa al’umma wajen zaɓe.

Amma jamaa mu sani, ko an samu canjin gwamnati, gyara ƙasar nan ba zai zama abu mai sauqi ba, mu faɗa wa kanmu gaskiya, sai dai muna fatan Allah ya gyara mana ƙasarmu Nijeryia, ya ba mu adalan shugabanni.

Aminu Ɗan Amajiri ɗan ƙasa ne mai bayyana ra’ayi. Ya rubuto daga Kano.