Kwankwasiyya JAMB, NECO da WAEC Kyauta: Anya?!

Daga FATUHU MUSTAFA

Wato ina ga Kwankwaso yana abin nan ne da Bature ke cewa ‘Clever by half’. Ga wanda bai san me ake nufi da wannan azancin na Bature ba, sai ya nemi Magana Jari ta ɗaya ya karanta labarin ‘Mara gaskiya ko cikin ruwa ya yi Jiɓi (Gumi)’. Ya yi hakan ne ta hanyar gaya wa mutane abinda suke so su ji ko da kuwa ba zai yiwu ba. Musamman tunda ya lura mutane, son ransu ne a gabansu ba son gaskiya ba.

Amma in dai mutane gaskiya suke so, da sai su tambaye shi, mun ji za ka bayar da wadannan kyauta ga ‘ya’yan mu, amma ya kamata ka gaya mana ta yaya? Manufarsa dai ya janyo hankalin iyaye da matasa, wanɗanda su ne kashi 70 na masu zaɓe, tunda kowa son na bati yake. Amma bari mu ga, shin hakan abu ne mai yiwuwa?

Da farko dai ina ganin an ma jahilci ya tsarin tarayya na qasa yake aiki a Nijeriya. Domin tambayar farko shi ne, shugaban ƙasa na da wannan ƙarfi a tsarin mulkin Nijeriya? Shin zai yiwu a tsarin gwamnatin tarayya ka iya hana biyan waɗannan kuɗaɗe a duk faɗin ƙasar?

Ko shakka babu, shugaban ƙasa na iya cewa a daina biyan kuɗaɗen wadannan jarabawa, amma fa a matakin makarantun sikandire na gwamnatin tarayya wato ‘Federal Government Kwaleji’, wanda yawan ɗalibin bai haura kashi 10 na yawan ɗaliban sakandiren Nijeriya ba. Sauran kashi casa’in ɗin dukkansu malllakin jihohi ne.

A Kano akwai sakandire sama da 1000, amma ƙwaya huɗu ne na gwamnatin tarayya, ɗaya a Unguwa Uku, ɗaya a Minjibir, ɗaya a Karaye, sai Army day dake barikin Bukaɓu. Waɗannan kuwa yawan ɗalibansu bai kai kashi 2 na yawan ɗaliban Kano ba. To ina ga sauran kashi 98 na ɗaliban? Ya za a yi da su?

Na biyu, shin gwamnatin tarayya za ta hana hukumar shirya jarabawa da Afirka ta Yamma aiki a Nijeriya ne? Domin ita dai ba mallakin gwamnatin tarayya ba ce. Ko kuwa za ta ringa biya wa yara kuɗin yin jarabawar ne, da na jiha da na tarayya?

Kamar yadda na fada a sama, zai iya ringa ware kuɗi yana biya wa ɗaliban dake karatu a sakandire mallakar gwamnatin tarayya, amma ba ya da ikon biya wa na jiha. Dan haka, ina ganin wannan kawai wayon a ci ne?

Na faɗa a doka, shugaban ƙasa baya da ikon tsoma baki a harkar ilmin jiha, wannan ne ya sanya baya ga hukumar kula da ilmin firamare ta gwamnatin tarayya, akwai hukma kuma ta jiha da ake kira SUBEB, kuma gwamna shi ke da ikon ya yi yadda yake so da kuɗaɗen wannan hukuma. Dan haka, bai da ikon ya tursasa gwamnonin jihohi su biya wa yara kuɗin jarabawa kyauta.

Na san wani zai ce to ai NECO da JAMB mallakin gwamnatin tarayya ne, dan haka, zai iya ba su dokar su bayar da fom dinsu kyauta ga ɗaliban jihohi. To a nan abin da kamar wuya. Domin dai, sai an koma zauren majalisa an tafka mahawara a kan dokokin da suka kafa su, suka ba su damar su sayar da fom, wanda wannan abu ne da zai ɗau lokaci.

Saboda da ma tunda aka kafa hukumar JAMB, aka babl ta dama ta sayar da fom, duk wanda ya ɗana jarabawar ba wanda ya taɓa yin ta kyauta, shekara 30 da na zana saya na yi. Ban ki ya ce zai rage mata kuɗi ba. Ita kuwa NECO da WAEC da ma can gwamnatocin jiha ne suke biya, shi ya sa ba a ganewa. Kuma ko da ɗin, akan yi jarabawar ‘Mock’ in ka ci a biya maka, in ba ka ci ba, ka sake. Sai dai daga baya abubuwa suka lalace aka ce, in ba ka ci ba ka biya wa kanka.

Matsala ta biyu a dai kan maganar JAMB da sauransu ita ce, samar da kuɗaɗen da za a yi hakan. Domin a wannan lokaci da tattalin arziki ke cikin wani hali, zai yi wuya gwamantin tarayya ta iya kwasar kuɗinta ta kashewa jihohi. Haka kuma shi a matsayinsa na shugaban ƙasa, bai isa ya tursasa gwamnatocin jihohi su biya wa yara kuɗin jarabawa kyauta ba. Domin tsarin mulki bai ba shi wannan dama ba.

Hanya ɗaya da hakan za ta iya yiwuwa shi ne, ya nemi majalisar tarayya da ta jihohi su yi wa kundin tsarin mulkin ƙasar nan gyaran fuska, a ɗauke ilmi daga jerin dokokin haɗaka, wato ‘concurrent list’ ya koma na gwamnatin tarayya kaɗai wato exclusive list. Wanda haka kuma abu ne mai wuya.

Ni dai a gani na, wannan salo ne na begun kura da gwado. A fake da kaska don a harbi guzuma.

Fatuhu mustapha marubuci kuma ɗan jarida, mai sharhi a kan al’amuran siyasa. Ya rubuto daga Abuja.