Buhari ya bayyana wanda zai miƙa wa ragamar mulki a 2023

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa, wanda zai miƙa wa mulki a 2023, mutum ne wanda ‘yan Nijeriya suka zaɓa.

Shugaba Buhari ya faɗi haka ne da yake zantawa da manema labarai a Aso Rock bayan an sauka sallar Idi.

Ɗan jarida ya tambayi Shugaba Buhari cewa ”’yan takarar Shugaban Ƙasa na ta zuwa wurinka neman yarda, kuma wasu sun ce ka ce muce su je su fito takara, wa za ka miƙa wa mulki a 2023?

Sai Buhari ya ce, ”duk wanda ‘yan Nijeriya suka zaɓa shi ne zan miƙa wa mulki.

Bayan haka kuma Shugaba Buhari ya ƙara da yin tsokaci akan matakan da jami’an tsaron ƙasar nan suke ɗauka domin kawo ƙarshen matsalar tsaro a Nijeriya.

”Duk manyan hafsoshin tsaron ƙasar nan da Sufeto Janar ɗin ‘yan sanda na aiki tuƙuru domin ganin an kawo ƙarshen matsalar ‘yan ta’adda a ƙasar nan.

”Yanzu abinda muka saka a gaba shine mu ga yadda za a kawo wa manoma tsaro domin damina ta tunkaro, a samu a koma gona.

A wannan shekara Shugaba Buhari ya garzaya tsohuwar filin Parade na Abuja domin yin sallar Idi.

Rabon da a yi sallah a wannan masallaci ya kai shekara uku tun ɓarkewar annobar Korona .

Bayan haka ‘yan uwa da abokan arziki sun riƙa tururuwa zuwa Fadar Shugaban Ƙasa domin gaisuwar sallah ga Shugaba Buhari.