Harin jirgin qasa: Muna aiki domin ceto mutanen da aka sace – Buhari

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya tabbatar wa iyalai da ‘yan uwan mutanen da aka sace daga jirgin qasan Abuja zuwa Kaduna cewa za a dawo da ‘yan uwansu gida ba tare da matsala ba.

Ya bayyana haka ne a yayin da wasu al’ummar Abuja suka kai masa gaisuwar Sallah ranar Litinin a fadarsa ta Aso Villa.

Wata sanarwa da Femi Adesina, mai magana da yawun Shugaba Buhari ya fitar ta ambato shugaban ƙasar yana cewa ‘yan bindigar suna amfani da mutanen da suka kama ne a matsayin wata garkuwa.

“A yayin da muke murnar wannan lokaci na farin ciki a tsakanin abokai da iyalai, muna sane cewa iyalai da dama a ƙasarmu suna cikin yanayi na tsoro da zaman ɗar-ɗar sakamakon sace ‘yan uwansu da ‘yan ta’adda suka yi, cikinsu har waɗanda aka sace bayan an sanya bam a jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna.

“Na bai wa jami’an tsaro umarni su yi gaggawar kuvutar da su daga hannun masu satar mutane cikin ƙoshin lafiya,” in ji Buhari.

Fiye da kimanin wata guda kenan ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane suka tare jirgin ƙasan Abuja zuwa Kaduna, inda suka jefa masa bam sannan suka buɗe masa wuta, har suka yi sanadin rasa rayukan wasu, da yin garkuwa da wasu da dama, wanda har zuwa yanzu ba su shaqi iskar ‘yanci ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *