Saƙon sallah: Mu na ƙoƙarin rage ƙarin farashin aikin Hajjin bana – NAHCON

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaban Hukumar Hajji ta Ƙasa, NAHCON, Barista Zikrullah Kunle Hassan, ya bayyana cewa hukumar na nan na iya bakin ƙoƙarinta na ganin cewa an rage farashin aikin Hajji na bana, duk da cewa ba makawa sai an ƙara farashin.

Kunle ya bayyana haka ne a saƙon sallah da ya fitar, wanda ya sanya hannu da kansa ranar Litinin.

A cewarsa, NAHCON na bin hanyoyin da su ka dace don ganin cewa an an bi hanyoyin da su ka dace domin ganin cewa ƙarin farashin aikin Hajjin bai yi yawan da har za a koka ba.

Sai dai kuma ya yi kira ga maniyyata da su ma su hanzarta su cika kuɗaɗen su kafin NAHCON ta sanar da farashin aikin Hajji da ta ƙayyade.

Ya ce biyan kuɗin a kan lokaci zai bai wa hukumar damar sanin adadin alhazan Nijeriya, sai ta yi amfani da hakan wajen yin shirye-shiryen aikin Hajjin.

Hassan ya kuma bayyana sabbin tsare-tsare da aka ɓullo da su a aikin Hajjin na bana, inda ya ƙara da cewa tuni NAHCON ta yi nisa wajen shirye-shirye na aikin Hajjin bana.