Yaqi da taaddanci na buƙatar haɗin gwiwar dukkanin sassa

Daga CMG HAUSA

Ta’addanci da dukkanin nau’o’insa na cikin manyan ƙalubalolin da ƙasashen duniya da dama ke fuskanta, tun daga sassan Turai zuwa Asiya da gabas ta tsakiya da nahiyar Afirka, kusan ba inda wannan matsala ba ta shafa ba.

Masharhanta na ta bayyana hanyoyi, da dabarun da suke ganin wajibi a bi su, idan har ana fatan shawo kan wannan ƙalubale da ya zamewa duniya ƙadangaren bakin tulo.

Yayin ziyarar babban magatakardar MDD Antonio Guterres, a ƙasashen Senegal da jamhuriyar Nijar da Najeriya, babban jami’in ya yi tsokaci game da muhimmancin haɗa ƙarfi da ƙarfi tsakanin dukkanin ƙasashen duniya, domin ba da gudummawar kakkaɓe wannan matsala, musamman a yankunan da ta fi kamari.

Mr. Guterres ya jaddada buƙatar ƙasashen duniya, su kara baiwa ƙasashen yankin Sahel na Afirka taimakon jin kai, ta yadda za su iya farfadowa, da sake gina wuraren da hare-haren taaddanci suka lalata.

Ƙarƙashin irin wannan manufa, akwai buƙatar samar da kuɗaɗen gudanarwa, da sake tsugunar da wadanda suka rasa matsugunnansu, da ’yan gudun hijirar da tashe-tashen hankula suka kora. Baya ga bukatar sauya tunanin mayakan da suka taba shiga ƙungiyoyin ’yan ta’adda, amma daga bisani suka mika wuya ga mahukunta.

Daga kalaman babban jami’in MDDr, da ma na sauran masana, muna iya fahimtar cewa, yaƙi da ta’addanci ba aiki ne na ƙasashen da abun ya fi shafa kaɗai ba, maimakon haka, aiki da ya dace dukkanin ƙasashen duniya su baiwa muhummanci, su hada gwiwa wajen musayar dabaru, da samar da horo da ƙwarewar makamar aiki, ta yadda za a gudu tare a tsira tare.

Fassarawa: Saminu Hassan