Buhari ya jajenta rasuwar sojojin saman Nijeriya a hatsarin Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jajen mutuwar sojojin Nijeriya biyu waɗanda suka yi hatsarin jirgin saman soji a Kaduna.

A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar, Mallam Garba Shehu, ya fitar ya ambato Shugaba Buhari yana bayyana “damuwarsa” bisa mutuwar Flight Laftanar Abubakar Alkali da Flight Laftanar Elijah Haruna Karatu.

“Na yi matuƙar kaɗuwar da ba zan iya cewa komai ba bisa rasuwar waɗannan matasa biyu waɗanda suka sadaukar da rayuwar wajen bauta wa ƙasa,” in ji Buhari.

Ranar Talata ne jirgin rundunar sojin sama ta Nijeriya ya yi hatsari inda duka jami’an biyu da ke cikinsa suka mutu.

A cikin shekara guda da ta gabata dai, jiragen sojin saman Nijeriya na yawan faɗuwa, lamarin da ke sanadiyyar mutuwar jami’an sojin daban-daban.