CAF ta bayyana ranakun gasar AFCON na 2025

Hukumar Ƙwallon Ƙafar Afrika, CAF, ta ce za a fara gasar kofin nahiyar ta shekarar 2025, wadda za a yi a ƙasar Moroko daga ranar 21 ga watan Disamba zuwa 18 ga watan Janairu. 

Shugaban hukumar, Patrick Motsepe ne ya bayyana haka a makon da ya gabata, a yayin taron majalisar zartarwa hukumar, wanda aka yi ta kafar bidiyo, inda ya ce yana da ƙwarin gwiwar gasar za ta kasance mafi armashi.

Tun da farko an tsara za a yi wannan gasa daga watan Yuni zuwa Yulin shekarar 2025 ne, amma sai aka canja shawara don gudun kada ta ci karo da gasar kofin duniya ta ƙungiyoyi da za a ƙaddamar a Amurka daga ranar 15 ga watan Yuni zuwa 13 ga Yulin shekara mai zuwa.

Sai dai ƙungiyoyin gasar Firmiyar Ingila ba za su ji daɗin wannan al’amari ba, saboda yadda suke matukar bukatar lokacin hutun kiristimeti da sabuwar shekara don aiwatar da wasanni masu mahimmanci, inda ƙungiyoyi ke buga wasanni fiye.