Yadda aka ƙarƙare gasar firimiyar Nijeriya na 2023/24

Spread the love

A ƙarshe dai ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Enugu Rangers ta ɗauki kofin babbar gasar firimiyar Nijeriya a karo na takwas bayan doke Gombe United har gida da ci 2-1.

Rangers ta samu jimillar maki 70 a gasar ta Nigeria Professional Footbal League (NPFL) kakar 2023-24, wanda hakan ke nufin ta samu tikitin zuwa gasar zakarun Afirka.

An gudanar da bikin ba ta kofin ne a filin wasa na Jos International Stadium – inda Gome United ke buga wasa – bayan wasan mako na 38.

Rangers ce ta fara cin ƙwallo minti uku da take wasa ta hannun Ogunleye, sannan Obaje ya ƙara minti huɗu bayan haka, kafin Hassan ya farke wa Gombe ƙwallo ɗaya a minti na 25.

Tun a ranar 16 ga watan Mayu Rangers ta haɗa maki 67 a saman teburi da ya ba ta zama gwarzuwar gasar bayan doke Bendel Insurance 2-0.

Kafin lashe gasar, Rangers ta ci wasa 21 cikin 38 da ta buga, ta yi canjaras bakwai sannan ta yi rashin nasara sau 10.

Remo Stars ce ta ƙare a mataki na biyu da maki 65, sai Enyimba a mataki na uku da maki 63, waɗanda suka samu gurbin shiga gasar zakarun Afirka ta baɗi.

Kamar yadda aka saba, ƙungiyoyi huɗu na ƙasan teburi ne ke sauka daga babba zuwa ƙaramar gasar ta firimiya wato Nigeria National League (NNL). 

Ƙungiyoyin su ne Sporting Lagos, Doma United, Heartland, Gombe United. 

A ranar Lahadi ne aka kammala gasar firimiyar Nijeriya (NPFL) ta 2023-24 bayan buga jimillar wasa 370, kuma ita ce karo na 52 a tarihi.

Yayin da Rangers International ta zama gwarzuwar gasar, ƙungiyoyin Sporting Lagos, da Doma United, da Heartland, da Gombe United ne suka ƙare a ƙasan teburin gasar kuma suka sauka zuwa ƙaramar gasar NNL.

Ƙungiyoyin Remo Stars, da Enyimba ne za su wakilci Nijeriya a gasannin zakarun Afirka na CAF Champions League da kuma CAF Confederations Cup.

Abubuwan da ya kamaya a sani a gasar;

Ɗan wasan Enyimba, Ɓictor Mbaoma, shi ne kan gaba wajen jefa ƙwallaye a raga bayan ya ci 16.

Ɗan wasan gaba na Kano Pillars, Yusuf Abdullahi, shi ne kaɗai ya ci ƙwallo sama da uku a wasa ɗaya, inda ya ci Gombe United ƙwallo biyar a wasan da suka yi nasara 5-2.

’Yan wasa shida ne suka ci ƙwallo uku rigis a wasa ɗaya a kakar bana. Su ne Robert Mizo (Bayelsa United), Yusuf Abdullahi (Kano Pillars), Albert Hillary (Plateau United), Nyima Nwagua (Riɓers United), Silas Nenrot (Plateau United), Ubong Friday (Akwa United), Godwin Obaje (Plateau United).

Remo Stars ce ta fi kowa karɓar jan kati a kakar bana, inda aka bai wa ‘yan wasanta jan katin har sau bakwai, Enyimba ce ke biye mata da shida.

Tun ana saura wasa ɗaya a gama gasar Rangers ta ɗauki kofin.

Tun ana saura wasa ɗaya a gama gasar Rangers ta ɗauki kofin.

Doma United da ta sauka daga gasar, ta fi kowa buga wasa mai yawa ba tare da an zira mata ƙwallo a raga ba, da guda uku kawai ta ɗara zakarun gasar Rangers.

Rangers sun fi kowa buga wasa mai yawa ba tare da rashin nasara ba, inda ta jera wasa 10 ba a doke ta ba, ta ɗara Doma United da wasa ɗaya.

Heartland, wadda ta sauka daga gasar – ita ce ta fi kowa yawan wasa a jere ba tare da nasara ba. Ta buga wasa 11 babu nasara, sai kuma Doma da Gombe da suka buga 10-10 a jere babu nasara.

Ɗan wasan Plateau United, Silas Nenrot, shi ne ya ci ƙwallo uku rigis a mafi ƙanƙantar lokaci a bana. Ɗan wasan gaban ya ci cikin minti 11 a wasan da suka doke Gombe United 4-0 a wasan mako 25. An ba da jan kati sau 49. An buga finareti 90, inda aka ci 70 kuma aka ɓarar da 20. An ci ƙwallaye 848. Sau 29 ƙungiyoyoyi suka yi nasara a wasannin da suka buga a waje. Gombe ce ta fi kowa ɗibar ƙwallaye, inda aka zira mata 76 jimilla.

An buga canjaras a wasa 86.

By ukarofi