Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ƙungiyar Ƙwadago ta Nijeriya, NLC, ta yi kakkausar suka ga kiran da wasu ‘yan siyasa ke yi na a sassauta tattaunawar mafi ƙarancin albashi.
Adebayo Aribatise, sakataren aungiyar ƙwadago ta NLC a Jihar Oyo, ya bayyana damuwar sa yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Lahadi a Ibadan.
Aribatise ya bayar da hujjar cewa rashin tattaunawa kan mafi ƙarancin albashi zai yi illa ga ma’aikata a jihohi da dama, domin ba dukkan gwamnatocin jihohi ba ne za su bi ƙa’idojin albashin ma’aikata.
Wannan matsaya ta zo ne a matsayin martani ga shawarwarin baya-bayan nan daga ’yan siyasa masu fafutukar ganin an kawo ƙarshen tattauna batun biyan albashi a matakin jiha.
Dokta Kayode Fayemi, wani fitaccen mai fafutukar ganin an sasanta batun albashin ma’aikata, kuma tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, ya bayyana buƙatar da ke akwai na jihohi su gudanar da tattaunawar albashi daban-daban da ƙungiyoyin ƙwadagon su, ba tare da gwamnatin tarayya ba.
Fayemi, wanda ya taɓa shugabantar ƙungiyar gwamnonin Nijeriya, ya jaddada cewa rarrabuwar kawuna na tattalin arziki a tsakanin jihohi na buƙatar irin wannan tsari na raba gari, wanda ya shahara da cewa, “Dukka yatsu ba su zama ɗaya.”
Fayemi ya ƙara da cewa tattaunawar mafi ƙarancin albashin ma’aikata tana amfana da ƙaramin ɓangare na al’ummar da ke cikin waɗannan tattaunawa. Duk da haka, Aribatise ya ci gaba da jajirce kan adawar da ya ke yi na raba ragamar mulki.
Aribatise ya yi nuni da cewa har yanzu jihohi da dama ba su cika aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000 da ake da su ba, duk da kokarin da NLC ke yi a matakin kasa da jihohi.
Ya bayyana damuwarsa cewa baiwa jihohi ikon tattaunawa akan albashi ba tare da wata matsala ba zai iya haifar da ci gaba da cin zarafin ma’aikata.
“Doka ta umarci jihohi su bi tsarin mafi ƙarancin albashi na ƙasa,” inji Aribatise.
“Ya zama wajibi gwamnatin tarayya ta cigaba da bin wannan tsari. Idan ba tare da wannan ba, wasu gwamnoni za su iya amfani da lamarin, suna biyan ma’aikata ɗan ƙanƙanin kuɗi.”
Aribatise ya yi gargaɗin cewa karkasa tattaunawar albashi zai iya sa wasu gwamnoni su yi amfani da ƙarfinsu wajen aiwatara da tsarin, lamarin da zai kai ga kulla yarjejeniyoyin da za su kawo cikas ga jin daɗin ƙananan ma’aikata, waɗanda za su iya samun ƙarancin albashi.
Tsayuwar ƙungiyar ta NLC ya nuna muhimmancin kiyaye tsarin haɗin kan ƙasa na tattaunawa kan batun albashi don tabbatar da cewa dukkan ma’aikata sun samu adalci ta gaskiya ba tare da la’akari da yanayin aikinsu ba.
