28
Jan
Daga AMINU AMANAWA a Sakkwato Shugaban kasuwar kayan gwari ta ƙasa da ƙasa ta Mile 12 da ke Legas, Alh Shehu Usman Jibril, ya bayyana cewa matakan da gwamnati ke ɗauka na inganta lamurran tsaro a Nijeriya ya taimaka wa lamurran kasuwancin kayan gwari, musamman na iya safarar su daga jihohin Arewa dake fama da matsalar tasaro zuwa kasuwar kayan gwari ta Mile 12. Shugaban ya bayyana hakan ne a wajen taron shekara-shekara da jagororin kasuwar ke gudanarwa a duk shekara domin tattauna nasarori da irin ƙalubalen da masu noma da kasuwancin kayan gwarin ke fuskanta, taron da a wannan…
