An ƙaddamar da shugabannin jam’iyyar ’yan citta na Arewa maso Yamma

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

Gwamnatin Jihar Kano tana gudanar da ayyuka a fannoni daban-daban don sauƙaƙa wa da bunƙasa harkar kasuwanci a jihar. 

Kwamishinan ma’aikatar kasuwanci na jihar Barista Ibrahim Muktar ya bayyana hakan a waje taron ƙaddamar da shugabannin ƙungiyar masu citta na ƙasa  na shiyyar jihohin Arewa maso Yamma.

Ya ce jihar Kano cibiya ce ta kasuwanci mai daɗaɗɗen tarihi da kuma take cigaba da jan ragamar kasuwanci duk da halin tattalin arziƙi da ake ciki.

Gwamnatin Jihar Kano na gudanar da muhimman ayyuka da suka haɗa da hanyoyi da kuma gina tasha ta tsandauri a garin Zawaciki don sauƙaƙa wa ‘yan kasuwa musamman irin waɗannan ƙungiyoyi na masu harkar citta bunƙasa kasuwanci.

A jawabinsa na maraba, shugaban ƙungiyar na ƙasa Mika Adamu Suleiman ya yi kira ga ‘yan ƙungiyar su haɗa kai don cigaban ƙungiyar da bunƙasarta yadda za a riƙa  samar da ingantacciyar citta da ake amfani da ita a ƙasa da  sarrafawa a fitar ƙasashen waje.

Shi ma Sarkin kasuwar Dawanau, Alhaji Hamisu Uba ya ce samar da ƙungiyar wani abu ne na alkhairi, ya kamata a tashi a yi hoɓɓasa  a jajirce a tabbatar da ana samar da ingantacciyar citta.

Sabon Shugaban ƙungiyar masu harkar citta na jihar Kano Alhaji Abubakar Mansur Abdullahi ya gode wa ‘yan ƙungiyar bisa haɗin kai da suka ba su na kaiwa wannan matsayi tare da kira gare su su ba shi cikakken haɗin kai don ciyar da ƙungiyar gaba.

Ya kuma gode wa gwamnatin jihar Kano kan gudummuwa da suke badawa kodayaushe.

Alhaji Abubakar Mansur ya yi kira ga Gwamnatin Kano akan ta cigaba da basu goyon baya domin  ciyar da jihar Kano gaba a ɓangaren citta daga kan nomanta har zuwa kasuwancinta.

Cikin waɗanda aka rantsar a ƙunshin ƙungiyar reshen jihar Kano sun haɗa da Alhaji Abubakar Mansur Abdullahi a matsayin shugaba; Hamza Abdullahi mataimakin shugaba; Alhaji Mahadi Abdullahi ma’ajin ƙungiya; Bazai Shawai jami’in hulɗa da jama’a da sauransu.

Shi ma da yake tattaunawa da ‘yan jarida ma’ajin ƙungiyar na Jihar Kano Alhaji Mahadi Abdullahi wanda ɗaya daga ‘yan kasuwa ne a kasuwar kayan amfanin gona ta duniya ya ce za su yi aiki tuƙuru don tabbatarbda cigaban ƙungiyar wajen yin duk abin da ya kamata  don ganin jihar Kano ta yi fice wajen harkar  hada-hadar cittan a duniya.

A yayin taron an rantsar da shugabannin ƙungiyar ‘yan citta na jihohin Kano, Katsina, Kebbi, Zamfara, Jigawa, Sakkwato da Kaduna.