12
Dec
Daga JAMIL GULMA a Kebbi Hukumar gidan gyaran hali reshen ƙaramar hukumar Argungu ƙarƙashin jagorancin babban Sufurtanda Lauwal Yeldu ta ziyarci fadar Mai Martaba Sarkin Kabin Argungu Alhaji Sama'ila Muhammad Mera. Da ya ke jawabi yayin ziyarar Yeldu ya bayyana irin nasarorin da gidan da ke reshen ƙaramar hukumar Argungu ya samu a ƙarƙashin jagorancinsa sun haɗa da kimanin mutane ashirin suka sauke Al’ƙur’ani Maigirma, aƙalla sama da mutane arba'in sun koyi sana'o'in hannu daban-daban tare da samun ƙwarewa a cikin sana'o'in da suka haɗa da ƙere-ƙere da saƙe-saƙe wanda yanzu haka wadansu daga cikin su sun cigaba da sana'o'in…
