04
Dec
Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jam'iyyar APC ta Jihar Zamfara ya yi Allah wadai da sanarwar da Gwamna Dauda Lawal ya yi a kafafen yaɗa labarai kwanan nan da ake zargin ya bai wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu sharaɗin ya kori ƙaramin ministan tsaro, Hon. Bello Mohammed Matawalle kafin ya koma jam'iyyar ta APC. Sakataren yaɗa labarai na jam'iyyar Yusuf Idris ya yi wannan sanarwar a cikin wata sanarwa da ya fitar wa manema labarai a Gusau a yau Alhamis. Jam'iyyar ta yi Allah wadai da yadda Gwamna Dauda ya ya ɗauki Matawalle a matsayin babban abokin gabar sa da…
