Labarai

Gwamna Abba ya buɗe titin kilomita biyar a Dawakin Tofa

Gwamna Abba ya buɗe titin kilomita biyar a Dawakin Tofa

Daga RABI'U SANUSI a Kano Gwamnan Kano,Abba Kabir Yusuf ya ƙaddamar da titi mai tsawon kilomita biyar a ƙaramar hukumar Dawakin Tofa, wanda gwamnatin baya ta yi watsi da aikinsa. Da ya ke jawabi yayin bude titin, Gwamna Abba ya buƙaci al'ummar yankin da su yi amfani da titin wajen bunƙasa tattalin arziƙinsu. Ya ce aikin titin na ɗaya ne daga cikin titinan kilomita biyar-biyar da gwamnatin Santa Rabiu Musa Kwankwaso ta fara aiwatarwa a dukkan ƙananan hukumomi 44 na jiha tun a shekarar 2013, wanda ya yi alkawarin kammalawa tun a lokacin yaƙin neman zabensa. Ya ce titin zai…
Read More
Gwamnatin Jihar Katsina ta musanta labarin zaman sulhu da ‘yan bindinga

Gwamnatin Jihar Katsina ta musanta labarin zaman sulhu da ‘yan bindinga

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta musanta wasu rahotanni dake cewa ta yi zaman sulhu da 'yan bindinga a ƙaramar hukumar Batsari, ɗaya daga cikin ƙananan hukumonin da 'yan bindingar suka fi kai hare hare a jihar. Kwamishinan yaɗa labarai da al’adu na jihar, Dakta Bala Salisu ne ya bayyana hakan. Kwamishinan ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin Jihar Katsina na nan kan bakanta na ƙin sasantawa ko yin wani zama na sulhu tsakanin gwamnati da 'yan bindingar. Sai dai Dakta Salisu, ya nanata aniyar gwamnati na karɓar duk wani ɗan bindiga da ya nuna zai miƙa…
Read More
Shugabannin ‘yan bindiga 15 sun miƙa wuya a Katsina

Shugabannin ‘yan bindiga 15 sun miƙa wuya a Katsina

Shahararrun ‘yan bindiga, Abu Radde da Umar Black, sun miƙa wuya tare da miƙa makaman su a ƙaramar hukumar Batsari, Jihar Katsina. A yayin wannan lamarin, an ceto mutane 15 da aka yi garkuwa da su, ciki har da maza uku, mata takwas, da yara huɗu. Wannan lamari ya zo ne a matsayin wata babbar nasara a yaƙi da ‘yan bindiga a yankin. Taron miƙa wuyan ya gudana a ranar 19 ga Janairu, 2025, a cikin yanayi na gaskiya da tsaro. Manyan jami’an tsaro, ciki har da wakilan sojoji, sun halarci wannan bikin tarihi domin tabbatar da sahihancin miƙa makaman.…
Read More
Bayan rantsuwa, Trump ya ɗauki gagarumin mataki

Bayan rantsuwa, Trump ya ɗauki gagarumin mataki

Daga USMAN KAROFI A ranar farko da Donald Trump ya hau kan mulki a matsayin Shugaban Amurka, gwamnatinsa ta sanar da rufe manhajar CBP One, wacce gwamnatin Biden ta ƙirƙiro don bayar da damar neman mafaka cikin tsari ga 'yan gudun hijira da ke shirin shiga Amurka ta iyakar kudu. Manhajar CBP One ta taimaka wajen rage yawan shiga ba bisa ƙa’ida ba a iyakar kudu ƙarƙashin gwamnatin Biden, inda ta baiwa kusan mutane miliyan ɗaya damar shiga Amurka ta hanyar shige da fice na doka. Sai dai, a yanzu, hukumar U.S. Customs da Border Protection (CBP) ta bayyana cewa…
Read More
Taron NBA: Gwamnan Zamfara ya nemi lauyoyin jihar su tsare ayyukansu bisa adalci

Taron NBA: Gwamnan Zamfara ya nemi lauyoyin jihar su tsare ayyukansu bisa adalci

Daga BELLO A. BABAJI Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya nuna muhimmancin sanya ƙwarewa da ƙoƙarin kiyaye adalci a yayin aiwatar da hukuncin doka acikin lauyoyi. Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da ya halarci taron lauyoyi da Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), reshen jihar ta shirya a Gusau. A wata sanarwa da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ƙungiyar ta bai wa gwamnan kyautar lambar yabo ga ƙoƙarinsa na inganta rayukan al'umma a jihar. Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa taruka irin wanda NBA ta saba shiryawa dama ne na bai wa lauyoyi fagen…
Read More
Kwamishina Waiya ya buƙaci gidajen jaridu su cigaba da nuna ƙwarewa a ayyukansu

Kwamishina Waiya ya buƙaci gidajen jaridu su cigaba da nuna ƙwarewa a ayyukansu

Daga BELLO A. BABAJI Kwamishinan yaɗa Labarai da Harkokin Cikin gida na Jihar Kano, Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya, ya yi kira ga gidajen jaridu da su cigaba da kiyaye ƙwarewa a harkar jarida. Kwamishinan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya karɓi baƙoncin wata tawagar masu kishin al'umma a ofishinsa. Ya jaddada cewa, ma'aikatarsa ta na cigaba da ƙoƙarin haɗa hannu da Hukumar Watsa labarai ta Ƙasa, NBC, don wayar da kan gidajen jaridu wajen inganta abubuwan da suke yaɗawa. A wata sanarwa da Daraktan Ayyuka na Musamman na Ma'aikatar ya fitar a ranar Litinin, Waiya ya nuna buƙatar…
Read More
Sojojin sun kawar da ɗimbin ‘yan ta’adda ciki har da ɗan Bello Turji

Sojojin sun kawar da ɗimbin ‘yan ta’adda ciki har da ɗan Bello Turji

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Dakarun Operation Fansan Yamma da na sojojin sama sun gudanar da aikin kakkaɓe maɓoyar 'yan ta'adda a yankunanan Shinkafi, Kagara, Fakai, Moriki, Maiwa da Chindo a yankin Sokoto da Zamfara yayin da suka hallaka 'yan ta'adda da dama ciki har da ɗan Bello Turji. Daraktan yaɗa labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai a Gusau yau Litinin. Karfin wutar da sojojin suka yi ya haifar da asarar rayukan 'yan ta'adda da kuma lalata cibiyar haɗa kayan aikinsu. Sanarwar ta kuma ƙara da…
Read More
Shettima ya isa Davos domin taron tattalin arziki na duniya na 2025

Shettima ya isa Davos domin taron tattalin arziki na duniya na 2025

Daga USMAN KAROFI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima, ya isa Davos, Switzerland, domin wakiltar Nijeriya a taron shekara-shekara na 2025 na taron tattalin arziƙi na duniya (WEF). Taron na bana ya haɗa shugabanni daga sassa daban-daban na duniya, manyan ‘yan kasuwa, da abokan cigaba domin tattaunawa kan manyan ƙalubale da damammaki a fannin tattalin arziƙi. A cikin jadawalin ayyukan sa, mataimakin shugaban Ƙasa zai halarci tarurruka masu muhimmanci, ciki har da wani taro mai taken “Taswirar samar da damammakin zuba jari ga kasuwannin Afirka,” wanda bankin ci gaban Afirka (AfDB) ya shirya tare da haɗin gwiwar WEF. Wannan taron zai…
Read More
NCC ta amince da ƙarin kuɗin kiran waya

NCC ta amince da ƙarin kuɗin kiran waya

Hukumar sadarwa ta ƙasa (NCC) ta amince da buƙatar kamfanonin sadarwa na ƙara farashin sabis ɗin su wanda ya shafi kuɗin kira. Mai magana da yawun hukumar, Reuben Mouka, ya bayyana cewa an bayar da wannan amincewa ne bisa tanadin Sashe na 108 na dokar sadarwa ta Nijeriya, 2003 (NCA), wanda ya ba hukumar ikon tsara da amincewa da farashin sabis na kamfanonin sadarwa. Mouka ya ce kamfanonin sadarwa sun nemi ƙarin farashin ne saboda yanayin kasuwar da ake ciki. Hukumar ta amince da ƙara farashin da ba zai wuce kaso 50 cikin 100 ba na farashin da ake amfani…
Read More