Taron NBA: Gwamnan Zamfara ya nemi lauyoyin jihar su tsare ayyukansu bisa adalci

Daga BELLO A. BABAJI

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara ya nuna muhimmancin sanya ƙwarewa da ƙoƙarin kiyaye adalci a yayin aiwatar da hukuncin doka acikin lauyoyi.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a lokacin da ya halarci taron lauyoyi da Ƙungiyar Lauyoyi ta Ƙasa (NBA), reshen jihar ta shirya a Gusau.

A wata sanarwa da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ƙungiyar ta bai wa gwamnan kyautar lambar yabo ga ƙoƙarinsa na inganta rayukan al’umma a jihar.

Gwamna Dauda Lawal ya jaddada cewa taruka irin wanda NBA ta saba shiryawa dama ne na bai wa lauyoyi fagen tattauna batutuwan shari’a don ci-gaban adalci, demokraɗiyya da hukuncin doka.

Ya yi kira ga lauyoyin da su cigaba da nuna ƙwarewa a yayin gudanar da ayyukansu wajen tabbatar da adalci ga al’umma musamman a lokacin da suke neman adalci.

Ya kuma yaba wa ƙungiyar wajen nuna turjiya yayin tabbatar da adalci har a lokutan da ake fuskantar ƙalubale wanda hakan ɗaya ne daga cikin ginshiƙan kowacce al’umma.

Har’ilayau, gwamnan ya ƙudiri aniyar cigaba da ƙoƙarin dawo da zaman lafiya mai ɗorewa a jihar da ke fuskantar barazanar tsaro a ƴan shekarun nan.

Kazalika, ya yi godiya ga waɗanda suka shirya ba shi kyautar lambar yabon inda ya ce hakan ya samu ne sakamakon ƙoƙarinsa na yaƙar ta’addanci da samar da ababan more rayuwa a jihar