“A wannan zamani kusan dole ne neman na kai ga ’ya mace”
Daga AISHA ASAS
Kalmar neman na kai ga ‘ya mace na da ma’anoni da dama a tsakanin al’umma, musamman a ƙasar Hausa. Yayin da ka ce, ku ƙyale ‘ya’ya mata su nemi na kansu, wasu kan fassara hakan da ku bar mata su lalace, ko su ba wa mata dama su zama kamar maza, ko kuma su bar mata su yi yadda suke so. Wasu kuma sai suke ganin kamar hanya ce ta yaɗa manufofin Yahudu.
Wannan na ɗaya daga cikin dalilan da suke sa wasu mazan tirjiya ga matansu kan ba su damar neman abin rufa wa kai asiri. Wanda wani lokacin ma akan samu mazan da ke kallon hakan a matsayin haramun.
A wasu wuraren sana’a ko aiki ga mace yakan iya zama haramun ba shakka, duk da cewa, lokuta da yawa ba sana’ar ce haramun ba, yadda matan ke yin ta ne ya haramta ta gare su.
Bari mu ɗauki sana’a a kafafen sadarwa da ta zama wata sauƙaƙiyyar hanyar kasuwanci ga mata, wanda da yawa a malamai sun tabbatar da babu illa ga irin wannan kasuwanci ga mata. Saidai ko kun san cewa akwai ta yadda za ta iya zama haramun gare ki mace. Ta yaya?
Wasu mata sukan yi amfani da fuskarsu wurin janyo hankalin maza kansu har su yi masu ciniki, ta hanyar ɗora hotunansu har waɗanda bai dace ma a ɗauke su ba bare har a kai ga yaɗawa. Da ire-iren su mata kan janyo ra’ayin maza sheɗanu su dinga ribibin kayansu koda ba sa buƙata. Ta kai wasu matan sukan iya ɓoye kasancewar su matan aure don kawai a masu ciniki. Yayin da wasu ma idan sun riƙa har waya za su iya yi da mazan da ba na su ba, ana kashe murya wai duk dan neman kasuwa.
Wani lokacin za ka ga mace, walau budurwa, bazawara ko matar aure, sun ci ado, ana ɗaukar ƙamshi, idan ka nemi sanin inda za su, wata ma’aikata ko wani wuri za su kai wa kwastomominsu kaya su siya ko waɗanda suka siya. A zauna ana fira da dariya, wai ke nan kin iya kasuwanci.
To, wannan yanayi ko littafan addini ki ke saidawa kin yi haramun, kuma ba wanda zai iya halasta miki abinda ki ke yi. Kuma duk wani miji mai kishin iyalansa ba zai iya lamuntar hakan ba. Kai koda ba matar aure ba ce wannan ɗabi’a ba ta kamace ta ba.
A wani ɓangare kuwa akwai sana’o’i da za su iya sa mace yin mu’amala da maza sosai, kamar kama shago cikin kasuwa, yin sana’o’in da maza ne suka fi yin su, wanda duk wanda za ki yi mu’amala da shi to zai kasance namiji. A irin wannan abin yana da fuska biyu.
Wasu mata na mu’amala da maza bisa mutuntawa, a cikin komai suna tunatar da kansu su mata ne, akwai ababen da ba za su yi ba don kawai suna mata. Wanda alaƙar da suke yi da su za ta kasance cikin mutuntawa.
Akwai kuma wani lokacin da matan za su mayar da kansu mazan, ala dole su wayewa, har ya kasance ba su da sauran mutunci a idon jama’a.
A irin wannan, miji ko iyaye na da damar hana irin wannan sana’ar, tare da samar da madadinta gare su.
Zancen neman na kai ga ‘ya mace ba ya cikin ababen da addini ya wajabtawa miji ya bar matarsa ta yi, don haka hana ta bai zama kaucewa ba. Saidai shi addini maslaha ne, zamani kuma kan canza, yanayin rayuwa na iya matsantawa da za a iya neman sauƙi, kuma idan an kiyaye dokokin Allah, sai a samu yadda ake so.
Saidai ya kai maigida, kafin ka hana matarka neman na kai, ka fara da tambayar kanka, ko akwai wani alfanun da ke cikin barin mace ta yi sana’a?
Shafin Gimbiya na jaridar Blueprint Manhaja, ya gayyato ɗaya daga cikin matan da suka san daɗin neman na kai, domin kasancewar ta ma’aikaciya, kuma ‘yar kasuwa, ba don komai ba sai don ta amsa mana wannan tambayar.
MANHAJA: Menene alfanun da ke cikin barin mace ta nemi na kanta?
JIDDAH NGURU: Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu. A cikin barin mace ta yi sana’a ko aiki akwai alfanu masu tarukan yawa. Wanda sai dai a faɗi iya waɗanda suka samu kawai.
Kaɗan daga cikinsu akwai;
Kiyaye darajarta tun tana matashiya budurwa. Idan mace budurwa tana aiki ko sana’a kafin ta yi aure, tana samu wata hanya ko lasisi na kiyaye mutunci da darajarta kanta. Rayuwar ƴa mace cike take da bukatu da wahalhalu, wanda idan ba ubangiji ne ya taimaka ya rufa asiri iyayenta masu wadata ba ne da ƙoƙari sai ki ga an samu matsala. Bayan ci da sha mace tana son ƙyalƙyali da gayu. Su kuma waɗannan abubuwan da kuɗi ake samun su. To a ina za ta samu kuɗin idan iyayenta ba su da hali? Ta hanyar sana’a ko aiki. To idan ba ta yin su fa? Kin ga ƙarshe saurayi ne dai zai ba ta. Idan kuma ba a yi dace ba, saurayin ya zamo ba mutumin kirki ba, to shikenan an samu matsala.
Amma da zarar Allah ya taimaka wannan yarinyar tana aikinta ko tana sana’a kuma ta kama aikin ko sana’ar da gaske, za ki ga ba kanta ba ma, hatta iyayenta da ƴan uwanta ta rufa musu asiri. Za ta taimaki kanta, za ta iya taimakon babanta ko Mlmamanta da wasu daga cikin buƙatun gida, za ta koyawa ƙannenta sana’ar da ta ke yi, ko kuma ta sama musu aiki.
Uwa-uba kuwa idan aka koma kan matar aure da ke gidan miji da yara. Anan ne za ka ga amfanin sana’a ko aikin mace. Musamman an samu mace mai hankali da sanin ya kamata, ta kuma haɗu da namiji mara mugunta da ƙyashi. Anan ne za ka ga rayuwar gidan mace mai aiki da sana’a da wacce ta ke zama haka kawai akwai gagarumin bambamcin da tazara mai yawa. Kama daga ta zaman lafiya da haɗin kai da miji, rufin asiri da uwa-uba soyayya da shakuwa.
A wannan yanayi da zamanin da muke ciki, maza masu dogon tunani da hankali su kan yi iya ƙoƙarinsu gurin sanin ya matarsu ta ke, kuma wanne irin neman kuɗi ne ya dace da ita , da kansa zai nemo ya kuma tallafa mata ya ƙarfafeta. Sabida a ƙarshe yasan kusan dukkan moriyar wannan sana’ar ko aikin akansa za ta kare.
Haka duniyar ta tashi tun tale-tale. Yawanci mazaje kan riga matayensu mutuwa. To a zamanin da muka riski kanmu, matuƙar namiji ya rasu ya bar iyalansa babu aikin yi ko sana’a, to tabbas sai waɗanda ubangiji ya kuɓutar daga shan wahala da ƙangin rayuwa. Hatta taimakon da ake yiwa iyalan mamaci daga ƴan uwa da abokan arziki waɗanda suka riƙe amana da zumunci ma sai ki ga baya shekara. Daga wannan lokacin kowa ya kama gabansa, an bar matarsa da dawainiyar yara da ta gida. Ga misalai nan kullum muna ta gani, yanda ake ta nuna matan da mazajensu suka rasu suka bar su da yara, kullum a waya ana buƙatar taimako da tallafi a gurin al’umma ta yanda za a agaji rayuwarsu. Ko yarinya kika gani an kama ta na yawo ko yaro an kama shi yayi sata ko shaye-shaye sai ki ji maraya ne da aka mutu aka bar mahaifiyarsu da dawainiyarsu kuma ba ta da kwakkwarar sana’a ko aikin yi.
Gidajen yari ya cika da mata bila’adadin sabida matsalar bashi. Wasu ma mazajen nasu na raye a duniyar. Amma wahala da dawainiyar gida ta sa sun ciyo sun kasa biya.
Idan muka koma kan bazawara ma haka lamarin ya ke. Wata an sake ta da yara, wata kuma mijin rasuwa ya yi. Ta ɗauko yara ta dawo gidansu da zama. Watakila iyayenta su ma ta kansu suke, ko wani ɗan uwanta ke ɗaukar nauyinsu, shi ma ga nasa iyalin, dole rayuwa za ta yi wahala. Idan ba ta da aikin yi ko sana’a shi ne za ki ga zawarawa a gida sun koma tamkar mata masu zaman kansu, yau ba ita anan gobe tana can tare da wane. Duk a ƙoƙarin ta na yanda za ta ciyar da kanta da yaranta. Ta addabi iyayenta ta addabi unguwa tana ɓatawa yaranta suna. Amma idan akwai abin yi, shiru za ku ji ta har lokacin da Ubangiji zai yanke mata wahala.
Malamai suna ta wa’azi sosai Allah ya saka musu da alkhairi. Suna ƙara wayar da kan mazaje kan amfanin barin matansu su yi sana’a ko aiki tunda ba haramun ba ne a addinan ce. Kuma kowanne namiji idan zai yi tsakani da Allah ya san wacce ce matarsa ya san kuma irin aiki ko sana’ar da ya dace da ita.
Dan haka amfanin aiki ko sana’a a gurin mace walau budurwa, matar aure ko bazawara a wannan zamanin namu zan iya cewa kusan dole ne, ba ra’ayi ba ne.
MANHAJA: A na ki gani, waɗanne irin dalillai ne ke sa maza hana matansu nema?
Dalilan suna da yawa. Amma kaɗan daga ciki akwai, Zuga. Wasu mazan suna bari zuga ko magana tana tasiri a cikin rayuwar gidajensu. Wasu walau ƴan uwa ko abokanai suna daga gefe wai sune za su tsara maka yanda za ka tafiyar da gidan ka. Shawara ba abu ne mara kyau ba. Amma tabbas kafin mace ko namiji yayi shawara da wani daga waje akan matsalar gidansa ya tabbatar da wanene wannan ɗin da ya ke ba shi shawarar. Shin abinda ya ke faɗa masa gaskiya ne tsakani da Allah ko akwai son rai. Shin da gaske shi wanda ya ke ba shi wannan shawarar masoyinsa ne na hakika kuma shi ma a gidansa a irin wannan shawarar ya ke amfani da ita, kuma ta yi masa amfani. Don mutane da yawa kan fada maka wani abin ne dan kawai su tarwatsa maka rayuwar gidanka su koma gefe suna maka dariya.
Wani ba shi da hanyar ko damar da zai ba matarsa jari ta yi sana’a. To dan haka yana jin haushin ya ga wani ya yi zai hana ka. Wani kuma wannan zaman lafiya da fahimtar juna da ku ke da shi da iyalanka shi baya samu, to duk hanyar da zai samu ya hana ku zai iya. Sai ki ga da mace ta samu aiki ko sana’ar yi wani daga waje kama daga aboki ko ɗan uwa yana cewa, kar ka yarda , ai da mace ta fara samun kuɗi za ta gagare ka, ko za ta lalace da sauransu. Wanda kuma yawanci ba haka ba ne. Kowanne namiji yasan matar da ya aura ya kuma san abinda za ta iya da wanda ba za ta iya ba. Shi da kansa sai ya zauna ya tantance.
Na gaba akwai girman kai. Akwai wasu daga cikin maza masu girman kai, da suke ganin kashi ne a gurinsu ace matarsu tana aiki ko sana’a, ai an raina su ma. Wanda watakila iya buƙatunta ma bai iya kammalawa ba, balle na ƴaƴanta da iyayenta da ƴan uwanta. Kuma sukan manta rayuwa ta kan iya sauyawa. Samun da ya ke yi yau, ba lallai gobe a same shi ba . Amma shi a ganinsa kaskanci ne kamar sa a ce matarsa tana neman kuɗi. Wannan dalilin ma kan hana wasu mazan barin matansu aiki ko sana’a.
Rashin kamun kai. Wasu mazan kan hana matansu aiki ko sana’a sabida rashin kamun kan ita macen. Mace ta zama mai surutu , shiga cikin maza , kule-kule da duk wasu dabi’u na rashin kamun kai kan sa ya hana ta yi. Sabida yasan zai siyowa kansa matsala ne zuwa gidansa.
Hassada, da gaske ana samun maza masu yiwa matansu hassada sosai. Zai ga ya za a ce matarsa tana samun kuɗi kamar yanda ya ke samu, ko kuma ma ace matarsa ta fi sa samun kuɗi. To wannan hassdarar na taka gagarumar rawa gurin hana ta neman kuɗi dan baya son ta taro shi ko ta fi shi.
Wannan sune kaɗan daga cikin dalilan da kansa wasu mazan hana matansu yin sana’a ko aiki.