20
Jan
Tsohon shugaban ƙasa na Amurka, Donald Trump, ya sake ɗarewa kan kujerar shugabancin ƙasar a matsayin shugaban ƙasa karo na biyu, a wani abin tarihi da ya faru ranar Litinin. Trump, wanda ya rantsar da kansa a gaban Majalisar Dokoki ta Amurka, ya sha alwashin ɗaukar matakai masu tsauri kan batutuwan shige da fice da kuma al'adun ƙasar, yana mai cewa zai fara gaggawar soke dokokin tsohon shugaban ƙasa Joe Biden. Taron rantsarwar, wanda aka gudanar a cikin ɗaki saboda tsananin sanyi, ya samu halartar manyan mutane da suka haɗa da shugabannin kamfanoni kamar Elon Musk, Mark Zuckerberg, Jeff Bezos,…
