Labarai

Majalisar Dokokin Legas ta tsige kakakin majalisa mafi daɗewa

Majalisar Dokokin Legas ta tsige kakakin majalisa mafi daɗewa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD ’Yan majalisar dokokin jihar Legas sun tsige kakakin majalisar, Mudashiru Obasa, sakamakon zarge-zargen da ake yi masa da suka jiɓanci batun saɓa dokokin majalisa da kuma almundahana. Tuni majalisar ta maye gurbinsa da mataimakiyarsa Misis Mojisola Meranda.  Misis Meranda, wadda ke wakiltar mazaɓar Apapa 1, ta kasance tsohuwar mai tsawatarwar majalisar. Yayin da Mojeed Fatai ya kasance sabon mataimakin kakakin majalisar dokokin ta jihar Legas. Korar Obasa na zuwa ne wata guda bayan da ake zarge shi da kashe Naira biliyan 17 wajen gyara kofar da ke kai wa majalisar. An ga ma’aikatan majalisar jihar cikin…
Read More
Rufe iyakokin Nijeriya bai amfani ba a yaƙi da matsalar tsaro – Majalisa

Rufe iyakokin Nijeriya bai amfani ba a yaƙi da matsalar tsaro – Majalisa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Majalisar Dokokin Nijeriya ta bakin kwamitinta na haɗin gwiwa kan Masana’antu, Ciniki, da Zuba Jari, ta soki manufofin rufe iyakokin Nijeriya, tare da bayyana rashin tasirinsa wajen daƙile aikata laifukan da suka shafi kan iyaka kamar su ‘yan bindiga da fasa ƙwauri. A yayin zaman tsaron kasafin kuɗin shekarar 2025 da ma'aikatar masana'antu, kasuwanci da zuba jari, 'yan majalisar sun nuna rashin jin daɗinsu kan yadda ake ci gaba da fuskantar ƙalubalen tsaro da tattalin arziki da ke da nasaba da yadda aka rufe iyakokin ƙasar da Nijar da Chadi, domin a cewarta Nijeriya na yaudarar…
Read More
Majalisa ta tuhumi JAMB kan kashe biliyan N2 kan abinci da maganin ƙwari

Majalisa ta tuhumi JAMB kan kashe biliyan N2 kan abinci da maganin ƙwari

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kwamitin Kuɗi na Majalisar Dokokin Tarayyyar Nijeriya sun tuhumi Hukumar Shirya Jarrabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) kan kashe kuɗin da suka wuce ƙa'ida kan abinci da lemu da ruwa da maganin sauro da sauransu a 2024. Kwamitin ya yi barazanar cire hukumar daga jerin ma'aikatun da za su shiga cikin kasafin kuɗin gwamnatin tarayya na 2025. Hakan na zuwa ne bayan da shugaban hukumar, Farfesa Ishaƙ Olayede ya gabatar da kasafin kuɗin hukumar na 2025 a gaban kwamitin na haɗin guiwa tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai. Olayede ya ce, JAMB ta samar da kuɗin shiga…
Read More
Gwamna Bago ya haramta karɓar kuɗin PTA a makarantun gwamnatin Neja

Gwamna Bago ya haramta karɓar kuɗin PTA a makarantun gwamnatin Neja

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya haramta karɓan kuɗaɗen ƙungiyar malamai ta iyaye ga ɗaliban da ke makarantun firamare da sakandare na gwamnati a faɗin jihar. Bago ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis a wata ziyarar aiki da ya kai wa Sarkin Pawa a ƙaramar hukumar Munya a wani ɓangare na duba ayyukan da ake yi a yankin. Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗauki nauyin biyan duk yaran da ke makarantun gwamnati kuɗaɗen PTA. “Wannan gwamnati ta ɗauki nauyin biyan kuɗin PTA na duk yaran da ke makarantun gwamnati a faɗin…
Read More
Falana ga Sanusi: Zauna daram, ba za a yi sarakuna biyu a Kano ba

Falana ga Sanusi: Zauna daram, ba za a yi sarakuna biyu a Kano ba

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Lauyan kare haƙƙin bil’adama, Femi Falana (SAN) ya ce, dole ne Masarautar Kano ta samu sarki ɗaya kacal, kamar yadda Kotun ɗaukaka ƙara ta amince da shi kuma Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, shi ɗin ne dai duk da tsananin adawa. Mista Falana ya bayyana haka ne a wajen taron tunawa da Cif Gani Fawehimi karo na 21 a Legas. Ya ce, “Amma mu a matsayinmu na lauyoyi, idan aka taru a wurin, dole ne mu gaya wa kanmu gaskiya. Ranka ya daɗe muna son taya ka murnar nasarar da ka samu…
Read More
Muna da kyakkyawar jituwa tsakaninmu da Yarabawan Legas – Sarkin Hausawan Festac

Muna da kyakkyawar jituwa tsakaninmu da Yarabawan Legas – Sarkin Hausawan Festac

Daga DAUDA USMAN a Legas Sarkin Hausawan Festac, Alhaji Mustapha Musa Katsina ya bayyana cewa, al'ummar Hausawa mazauna Jihar Legas suna ƙara samun jituwa da zaman lafiya tare da fahimtar juna a tsakaninsu da sauran ƙabilu mazauna jihar bakiɗaya. Sarkin Hausawan wanda kuma shi ne jagaban al'ummar Hausawan Festac ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan da Mai Martaba Sarkin Yarabawan ƙaramar Hukumar Amuwo Odofin ya kammala naɗa masa rawani tare da jaddada masa sarautarsa ta sarkin Hausawan Festac da kewayenta bakiɗaya. Taron jaddada naɗin sarautar ya samu halartar waɗansu daga cikin sarakunan Yarabawan ƙaramar hukumar Amuwo Odofin da sauran…
Read More
Gwamna Abba Kabir ya samu kyakkyawar tarbiyya tun daga gidansu – Muhammad Hussain

Gwamna Abba Kabir ya samu kyakkyawar tarbiyya tun daga gidansu – Muhammad Hussain

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana cikar shekaru 62 a Gwamna Abba kabir Yusuf  a rayuwa da cewa masu albarka ne da ba a taba samun Gwamna da ya yi abubuwa na alhairi da yawa cikin dan lokaci da hawansa mulki ba kamarsa. Alhaji Muhammad Hussain Mashkur daya daga cikin hadiman Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan da yake zantawa da yan jarida a taron da akayi na zuriyar Malam Ibrahim Dabo da akayi a gidan Gwamnati a ranar Asabar. Ya ce abinda ya jawowa Gwamna ɗabi'antuwa da kyawawan hali saboda irin managarcin tarbiyya ne  daya samu…
Read More
 Za mu riƙe amanar da Gwamna Abba ya ba mu don bunƙasa cigaban matasa a Kano – Mustapha Kwankwaso

 Za mu riƙe amanar da Gwamna Abba ya ba mu don bunƙasa cigaban matasa a Kano – Mustapha Kwankwaso

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana Gwamnatin Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa mai son ci gaban matasa ce duba da irin kulawa da yake bai wa cigaban su a fannoni daban-daban. Kwamishinan matasa da wasanni na jihar Kano, Hon Mustapha Rabiu Musa Kwankwaso ne ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida. Ya bayyana cikar Gwaman Abba Kabir Yusuf shekaru 62 abin farin ciki ne ga matasa da duk al'ummar jihar Kano suna taya shi murna akan wanan ci gaba, da ya shigo da abubuwa na alkhairai a cikin wannan sabuwar shekara. Ya ce idan aka duba…
Read More
Yadda saurayi ya ‘fille kan budurwarsa’ a Nasarawa

Yadda saurayi ya ‘fille kan budurwarsa’ a Nasarawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Ana ci gaba da alhinin wata budurwa mai suna Salome Adaidu, wadda ake zargin saurayinta da fille mata kai a jihar Nasarawa da ke arewacin Nijeriya. Jami'an tsaro ne suka damƙe saurayin mai suna Timileyin, wanda mawaƙin yabo na addinin Kirista ne, ɗauke da kan Adaidu, a ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu, kusa da wani coci. Lokacin da take bayani kan lamarin, Anibe Treasure, wadda ƙawa ce ga marigayiyar ta ce ta ga labarin cewa wani ya fille kan budurwarsa a shafukan sada zumunta amma ba ta san cewa ƙawarta ba ce har…
Read More
Nahiyar Afirka na da abin da za ta dogara da kanta — Tinubu

Nahiyar Afirka na da abin da za ta dogara da kanta — Tinubu

Daga  SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa Nahiyar Afirka na da dukkanin abubuwan da ake buƙata domin ta iya dogara da kanta. Ya ce Afirka na da arzikin ƙasa, mutane masu hazaƙa, da dukiyar da za ta iya amfani da su domin ciyar da nahiyar gaba. Tinubu ya yi wannan bayani ne a Abu Dhabi, Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa, a ranar Litinin lokacin da ya gana da Shugaban ƙasar Rwanda, Paul Kagame. A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na ɗ, Tinubu ya ce: “A yammacin yau, na yi ganawar faɗaɗa fahimta tare…
Read More