Labarai

EFCC ta bankaɗo makarantar koyon yahoo a Edo

EFCC ta bankaɗo makarantar koyon yahoo a Edo

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin ƙasa Ta'annati (EFCC), ta ce ta kama mutane 25 waɗanda take zargin masu damfara ne ta yanar gizo a wani wuri da ake kyautata zaton na horar da damfara ne a Benin, babban birnin Jihar Edo. A cikin wani rubutu da ta ɗora a shafinta na X, hukumar ta ce ta yi nasarar yin hakan ne a ranar Alhamis ta hanyar amfani da jami'anta na Benin. Ta ce kamen ya biyo bayan samun wasu sahihan bayanan sirri ne da ke nuna cewa ana amfani da wani gini a matsayin wurin…
Read More
Marigayi Lawal Sa’idu Funtua shahararren marubuci ne, inji Dujiman Katsina

Marigayi Lawal Sa’idu Funtua shahararren marubuci ne, inji Dujiman Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban kwamitin harkokin cikin gida na Majalisar Wakilai kuma Dujiman Katsina, Hon. Abdullahi Aliyu Ahmed ya nuna alhininsa kan rasuwar ɗaya daga cikin sanannun ƴan jarida a Najeriya, Sa'idu Funtua. Marigayin ya rasu ne ranar Alhamis da ta gabata bayan ya ɗauki tsawon lokaci yana fama da rashin lafiya. A wata takarda da jami'in yaɗa labarai, Sardaunan Francis ya fitar, ɗan majalisar ya bayyana Lawal Sa'idu a matsayin ƙwararren dan jarida da al'umma ke alfahari da shi kan faɗin gaskiya komai ɗacinta . Ya ce rayuwarsa a aikin jarida yafi mayar da hankali wajan rubuce-rubuce…
Read More
Lambobin da suka koɗe: Kotu ta hana jami’an kiyaye haɗurra kama motoci da cin tarar direbobi

Lambobin da suka koɗe: Kotu ta hana jami’an kiyaye haɗurra kama motoci da cin tarar direbobi

Daga BELLO A. BABAJI Wata babbar kotun tarayya dake Legas, ta haramta wa Hukumar Kiyaye Haɗdura (FRSC) kama motoci masu koɗaɗɗun allunan lambobi. Mai Shari'a Akintayo Aluko ya bayyana hakan a ranar Juma'a inda ya kuma hana hukumar karɓar tara ko hukunta direbobin da ke ɗauke da motoci masu koɗaɗɗun lambobi. Kotun ta bada umarnin ne a lokacin da ta ke hukunci game da wata ƙara da wani lauya mai suna Chinwike Chamberlian Ezebube ya shigar akan FRSC. Ya shigar da ƙarar ne akan hukumar don kotun ta bayyana ko FRSC ta na da alhakin hukunta masu koɗaɗɗun allunan lambobi…
Read More
Abinda ya sa na umarci a cire tozuna a manyan titina – Ministan Ayyuka

Abinda ya sa na umarci a cire tozuna a manyan titina – Ministan Ayyuka

Daga BELLO A. BABAJI Ministan Ayyuka, David Umahi ya ce ya umarci a cire tozuna a manyan titinan Nijeriya ne don inganta zirga-zirgar ababen hawa da rage cinkoso a titinan. Ministan ya bayyana hakan ne a wani zama na kwana biyu da injiniyoyi da manyan ma'aikata a Abuja, ranar Juma'a. Zaman, wanda Ma'aikatar ta shirya, an yi masa take ne da; 'Ensuring Delivery Mr. President's Agenda on Road Infrastructural Development', wato tabbatar da isar da ayyukan Shugaban ƙasa game da bunƙasa ci-gaban titina. Ya ce yana da muhimmanci a cire tozunan sakamakon haifar da haɗurra da suke yi da tsawaita…
Read More
Mu na aiki tuƙuru wajen dawo da martabar tattalin arziƙin Nijeriya, inji Shettima

Mu na aiki tuƙuru wajen dawo da martabar tattalin arziƙin Nijeriya, inji Shettima

Daga BELLO A. BABAJI Mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima ya jadadda ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na haɓaka harkokin tattalin arziƙi da inganta kiwon lafiya a Nijeriya. Hakan na zuwa ne a lokacin da Gidauniyar Sir Emeka Offor (SEOF) ta sanar da bada gudunmawar Dala miliyan 5 ga Gidauniyar Rotary don magance matsalolin yawan mace-macen mata masu ciki a Nijeriya. A lokacin da ya ke magana a yayin ziyarar Shugaban Amintattu na Rotary Foundation na Ƙasa-da-ƙasa, Mark Daniel Maloney a Fadar Shugaban ƙasa, Shettima ya jinjina wa gagarumar gudummawar da gidauniyar da wasu masu-ruwa-da-tsaki suka bayar ga ci-gaban Nijeriya. Ya…
Read More
Tinubu ya yaba wa gwamnoni bisa goyon bayan ƙudirin kwaskwarimar haraji

Tinubu ya yaba wa gwamnoni bisa goyon bayan ƙudirin kwaskwarimar haraji

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana jin daɗinsa ga ƙungiyar gwamnonin Nijeriya bisa goyon bayan ƙudirin kwaskwarimar haraji guda huɗu da ya miƙa wa majalisa domin tantancewa. Ya kuma jinjina wa gwamnonin kan namijin ƙoƙarin da suke yi wajen jagorancin al'ummarsu da samar da haɗin kai tsakanin jagororin ƙasar ba tare da la'akari da yare, yanki ko kuma banbancin siyasa ba wanda hakan wani mataki ne da zai haɓaka ci-gaba a Nijeriya. A wata takarda da mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya fitar a ranar Alhamis, Tinubu ya yaba wa Shugaban ƙungiyar kuma…
Read More
An ɗauke wuta a Fadar Shugaban Ƙasa da wasu sassan Abuja bayan sace wayoyin layukan lantarki

An ɗauke wuta a Fadar Shugaban Ƙasa da wasu sassan Abuja bayan sace wayoyin layukan lantarki

Daga BELLO A. BABAJI Fadar shugaban ƙasa dake Abuja da ake kira da Aso Rock ta shiga halin ɗaukewar wuta bayan da wasu ɓata-gari suka sace wayoyin layukan lantarkin da ke kai wa fadar da wasu sassan birnin wuta. Babban jami'in yaɗa labaran Kamfanin Raba Wutar lantarki ta Ƙasa (TCN), Ndidi Mbah ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a inda ya ce lamarin ya auku ne a yankin wajen shaƙatawa na 'Millennium Park'. Jami'in ya kuma ce ɓarayin sun kuma ɗauke waya mai tsawon mita 40 wanda hakan ya shafi ɓangarori takwas na yankin Central…
Read More
Wata biyu kan karaga: Al’ummar Keffi na ci gaba da yaba wa Dokta Idris Damagani

Wata biyu kan karaga: Al’ummar Keffi na ci gaba da yaba wa Dokta Idris Damagani

Daga JOHN D. WADA a Lafiya A yanzu haka al’ummar ƙaramar Hukumar Keffi a jihar Nasarawa suna cigaba da yaba wa sabon shugabansu wanda aka zaɓa aka kuma rantsar kimanin watanni 2 kacal da suka gabata a inuwar jami’iyyar APC mai mulki a jihar wato Dokta Idris Ahmad Damagani dangane da tsalon shugabancin sa wadda acewar su ke cigaba da canja fatsalin karamar hukumar ta Keffi da kewayen ta baki daya kawo yanzu bayan watannin 2 kacal. Waɗannan al’umma ainihin ‘yan karamar hukumar ta Keffi da wakilin mu ya zanta dasu game da ayyuka da salon shugabancin sabon shugaban nasu…
Read More
Mun fara gudanar da harkokin karatu gadan-gadan a zango na 2025 a NSUK – Kwamared Jafar Abubakar

Mun fara gudanar da harkokin karatu gadan-gadan a zango na 2025 a NSUK – Kwamared Jafar Abubakar

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Sabon mai magana da yawun babbar jami’ar jihar Nasarawa dake Keffi (NSUK), Kwamared Jafar Abubakar ya ce tuni jami’ar ta fara aiwatar da harkokin karatu na zangon karatun sabuwar shekarar 2025 da ake ciki. Kwamared Jafar Abubakar ya bayyana haka ne a lokacin da yake tattaunawa da wakilinmu a ofishinsa dake jami’ar ranar Litinin na mako da ake ciki. Ya buƙaci ɗaliban babbar jami’ar mallakar gwamnatin jihar ta Nasarawa musamman wadanda basu dawo daga hutun karshen shekara da aka tafi kwanakin baya ba su hanzarta yin haka don a yanzu harkokin taratun yama yi…
Read More
Yadda Jimmy Carter ya ziyarci Abacha don neman ya sake ni – Obasanjo

Yadda Jimmy Carter ya ziyarci Abacha don neman ya sake ni – Obasanjo

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Tsohon Shugaban ƙasa, Olusegun Obasanjo, ya bayyana yadda tsohon Shugaban Amurka, Jimmy Carter, ya taka muhimmiyar rawa wajen ceto rayuwarsa. Obasanjo ya yi wannan bayani ne a taron tunawa da Carter, wanda gudanar a ɗakin karatu na Olusegun Obasanjo da ke Abeokuta, a Jihar Ogun, don karrama Carter. Tsohon shugaban na Amurka ya rasu ranar 29 ga watan Disamban 2024, yana da shekaru 100. Obasanjo, ya bayyana cewa Carter ya kai wa marigayi Janar Sani Abacha ziyara da kansa domin roƙon a sako shi daga kurkuku. “Shugaba Carter yana cikin abokaina na waje da suka jajirce…
Read More