Labarai

Muna da burin shirya musabaƙar Alƙur’ani na bebaye, kurame da makafi a Jami’ar Khairun – Farfesa Garba 

Muna da burin shirya musabaƙar Alƙur’ani na bebaye, kurame da makafi a Jami’ar Khairun – Farfesa Garba 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Jami'ar Khalifa Isyaka Rabiu an samar da ita ne bisa tunanin Khalifan Tijjaniyya marigayi Sheik  Isyaka Rabiu ne,wanda shine ya ƙirƙiro ta ta  zama kuma cikamakin ayyukan alkhairi da yake yi  kamar yanda aka san shi a yaɗa karatun ƙur'ani da haddar sa da gina masallatai da masallatan ta kyautatawa limamai da sauran abubuwa,haka ma ya yiwa karatun zamani hidima ta kafa makarantar furamare,da ƙaramar sakandire da babba  sai kuma ya ƙirƙiri wannan  jami'a. Mataimakin shugaban Jami'ar Khairun, Farfesa Abdulrashid Garba ne ya bayyana hakan da yake zantawa da 'yan jarida ya ce Allah cikin…
Read More
Gwamnatin Borno ta horar da mata 162 sana’o’in dogaro da kai

Gwamnatin Borno ta horar da mata 162 sana’o’in dogaro da kai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja A wani mataki na ƙarfafa wa mata da ‘yan mata da dogaro da kai, uwargidan Gwamnan Jihar Borno, Dakta Falmata Zulum, ta jagoranci bikin yaye mata 162 da suka kammala horo a makarantar koyon sana’o’i da ke Bolori II, a Maiduguri. An shirya wannan horo ne don tallafa wa mata musamman waɗanda suka yi hijira ko kuma ba su samu damar yin karatun boko ba, tare da nufin bunƙasa tattalin arziƙin jihar. Kwamishinan Ilimi, Kimiyya da Fasaha na Jihar, Injiniya Lawan Abba Wakilbe, ya ce shirin ya dace da manufar Gwamna Babagana Zulum, na…
Read More
Tinubu na cikin mutanen da suka fi tsara manyan laifukan rashawa a 2024 – OCCRP

Tinubu na cikin mutanen da suka fi tsara manyan laifukan rashawa a 2024 – OCCRP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Shugaban Nijeriya Bola Tinubu na cikin na gaba-gaba a jerinn mutanen da suka fi tsara manyan laifuka da kuma aikata cin hanci da rashawa, a cewar rahoton cibiyar kula da aikata manyan laifuka da rashawa ta duniya. Cibiyar Organized Crime and Corruption Reporting Project (OCCRP) kan nemi 'yan jarida da ƙwararru da ɗaiɗaikun mutane su kaɗa ƙuri'a wajen zaɓen mutanen da suka fi aikata tsararrun laifkuka a ɓangaren cin hanci da rashawa duk shekara. Tinubu ne ya zo na uku a jerin, yayin da tsohon Shugaban Syria Bashar al-Assad ya zo na ɗaya "saboda…
Read More
Hisbah ta fara kwashe yaran da ke gararamba kan titunan Kano

Hisbah ta fara kwashe yaran da ke gararamba kan titunan Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Kano ta fara kwashe 'dubban' yara da ke rayuwa a kasuwanni da ƙasan gadoji a Kano, babban birnin jihar. Gwamnatin ta fara ɗaukar matakin ne a ranar Litinin, inda ta samar da wani sansanin ajiyewa da kuma tantance yaran. Shugaban hukumar Hisbah a jihar, Sheikh Aminu Daurawa ya ce "mun samu rahoton akwai ɗaruruwa ko kuma dubban ƙananan yara da ba su haura shekara 15 ba waɗanda suke kwana a ƙarƙashin gadoji da cikin tashoshi da kuma kasuwanni." "Ci gaba da rayuwarsa a waɗannan wurare zai iya haifar da matsala ta tsaro da…
Read More
Yadda aka kashe abokin ango a taron ɗaurin aure

Yadda aka kashe abokin ango a taron ɗaurin aure

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan daba sun kashe wani ɗan shekara 25 a wurin taron ɗaurin auren babban abokinsa a Jihar Neja. Matashin, mai suna Murtala Hassan, wanda shi ne babban abokin ango ya gamu da ajalinsa ne a yayin da yake rabon faɗa a wurin bikin auren a unguwar Barkin-Sale da ke garin Minna. Shaidu sun ce matashin wanda ke sana’ar ɗinki ya rasu ne bayan an soka masa wuƙa a rikicin ƙungiyoyin ’yan daba masu gaba da juna ranar Lahadi da misalin ƙarfe 10 na dare. Wani mazaunin unguwar Barikin-Sale ya ce, rikicin kungiyoyin an daɗe…
Read More
Faretin ban girma da aka yi wa Seyi Tinubu bai kamata ba, inji Atiku

Faretin ban girma da aka yi wa Seyi Tinubu bai kamata ba, inji Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, ya yi Alla-wadai da faretin ban girma da ka yi wa ɗan gidan shugaban ƙasa, Seyi Tinubu, yana mai bayyana hakan a matsayin saɓa wa al’ada rundunar sojin Nijeriya tare da nuna buƙatar a gudanar da bincike kan al’amarin. A cikin wata sanarwa da ofishin mai magana da yawun Atiku ya sanya wa hannu, Paul Ibe, Atiku ya nuna rashin jin daɗinsa game da yadda aka saɓa wa dokar rundunar sojin Nijeriya na haɗa faretin girmamawa ga shugabannin. Atiku ya ƙalubalanci sahihancin sashen rundunar sojin da ake kira…
Read More
Ya kamata masu sayar da man girki a unguwanni su riƙa rangwame – Mustapha Shu’aibu 

Ya kamata masu sayar da man girki a unguwanni su riƙa rangwame – Mustapha Shu’aibu 

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Shugaban kasuwar Galadima, Alhaji Mustapha Shu'aibu Sulaiman ya bayyana damuwarsa akan  yadda masu sayar da man girki a tsakanin al'umma musamman a unguwanni ba sa rage farashin man, alhali kuwa an ɗan samu sauƙi akan ta'azzarar tsada da ya yi a kwanakin baya. Da yake zantawa da manema labarai ya ce kowa ya sani a watannin baya da suka gabata an samu hauhawar tsadar man girki, amma cikin ikon Allah yanzu Allah ya juya lamarin ana samun  sauƙi da ya fi a ce ƙaruwa yake a  harkar mai an samu ragi. Ya ce amma yana…
Read More
Bafarawa ya buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki a kan Turji

Bafarawa ya buƙaci gwamnati ta ɗauki mataki a kan Turji

Daga SANI HAMAD GIWA a Abuja Tsohon Gwamnan Jihar Sakkwato, Attahiru Bafarawa, ya yi kira ga gwamnati ta ɗauki matakin gaggawa a kan Turji. “Gwamnati ta ɗauki barazanar Turji da muhimmanci kuma ta kare al’umma,” inji Bafarawa. “Muna buƙatar zaman lafiya don magance matsalolin yunwa da rashin aikin yi, amma dole ne a haɗa hannu don tallafa wa jami’an tsaro.” A halin yanzu, sojoji sun bayyana Bello Turji a matsayin “wanda ya kusa zuwa hannu” tare da alƙawarin kawar da shi. A cewar Manjo Janar Buba, “Sojoji suna ƙara matsa lamba a kan ‘yan ta’adda. “Turji zai gamu da irin…
Read More
Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 20, sun ƙwato litar mai 90,000

Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 20, sun ƙwato litar mai 90,000

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Rundunar Sojin Nijeriya, da ke Fatakwal ta lalata haramtattun matatun 20 tare da ƙwato litar man fetur sama da 90,000 da aka sace a yankin Neja Delta. Daga ranar 23 zuwa 29 ga watan Disamba, 2024 sojoji sun kuma lalata kwale-kwale guda 21 da ake amfani da su wajen satar mai, tare da kama mutum takwas da ake zargi. A yayin samamen, an gano manyan tankunan ajiyar mai ɗauke da man da aka sato, da kuma haramtattun kayan aikin tace mai a Jihohin Ribas, Bayelsa, Akwa Ibom, da Delta. A ƙaramar Hukumar Asari-Toru, sojoji…
Read More
Gwamnatin Kano za ta shigar da fursunoni cikin shirin inshorar lafiya

Gwamnatin Kano za ta shigar da fursunoni cikin shirin inshorar lafiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano ta ce ta shigar da fursunoni cikin tsarin inshorar lafiyarta a jihar domin samar musu da ingantaccen kula da lafiya kyauta yayin da su ke a tsare. Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami'in hulɗa da jama’a na Hukumar Kula da Gyaran Hali ta Nijeriya reshen Jihar Kano, CSC Musbahu Kofar-Nasarawa, ya sanya wa hannu a ranar Litinin a Kano. ƙofar-Nasarawa ya rawaito shugabar Hukumar taimakekeniyar lafiya ta Jihar Kano (KACHMA), Dr. Rahila Aliyu Mukhtar, tana fadin haka yayin ziyarar ta ga Shugaban Hukumar kula da gidajen gyaran hali…
Read More