Labarai

Babban jami’in rediyon Freedom da Dala FM, Shehu Ɗalhatu ya rasu

Inna Lillahi Wa'inna Ilaihi Raji'un! Cikin alhini mu ke sanar da rasuwar ɗaya daga cikin daraktocin Hukumar Gudanarwar Rukunin Tashoshin Freedom Rediyo da Dala FM, Alhaji Shehu Ɗalhatu. Marigayin ya rasu ne a yammacin Jumu'ar nan a birnin Madina na ƙasar Saudiyya, inda aka bada umarnin yin jana'izarsa. Ana karɓar gaisuwa a gidan Wazirin Dutse, Alhaji Bashir Dalhatu da ke Hotoro Kwanar Maggi, a Kano. Mu na addu'ar Allah ya gafarta masa ya kuma ba mu haƙurin jure wannan rashi. Sanarwa daga Hukumar Gudanarwa ta Freedom Rediyo.
Read More

Gwamnatin Tarayya ta ceto matar da aka yi safarar ta daga Iraƙi

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a, 3 ga watan Junairu, 2025 ne wata ƴar Nijeriya mai suna, Eniola Isaac za ta dawo ƙasar bayan wakilan Nijeriya a Jordan sun shiga tsakani da ƙasar Iraƙi. Hakan na zuwa ne bayan wani rahoto da ke zargin cewa an yaudari matar ne mai shekaru 28 da cewa za a kai ta Iraƙi don samun rayuwa mai daɗi. Bayan ta sha duka da wasu nau'ukan wulaƙanci, sai Eniola ta koka ga hukumomin Nijeriya don su dawo da ita ƙasarta. Cikin wani rahoto da NiDCOM ya fitar a ranar Alhamis ta kafar X, ya…
Read More

Gwamna Ƙaura ya shiga tsaka mai wuya bayan kasafin biliyan N3.4 ga fetur da tafiye-tafiye

Daga BELLO A. BABAJI Jami'iyyar PRP reshen Bauchi ta yi tir da shirin Gwamnatin jihar da Majalisar Dokoki na kashe sama da Naira biliyan 3.4 ga sanya fetur a ababen hawa, janaretoci da tafiye-tafiye a shekarar 2025 a matsayin abin kunya da rashin iya sarrafa dukiyar al'umma. A cikin wata takarda da ke ɗauke da sanya hannun Sakatarenta, Hon. Wada Abdullahi, jami'yyar ta ce lokaci ya yi da za a riƙa bibiyar masu riƙe da muƙaman gwamnati don tabbatar da cewa sun yi adalci a kowane mataki musamman ganin yadda al'umma suke fuskantar matsin tattali a jihar. Ta ce yayin…
Read More

Gwamnan Nasarawa ya sallami sakataren gwamnati da kwamishinoninsa

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya rushe Majalisar Zartarwar Gwamnatinsa inda ya tsige sakataren gwamnati da ilahirin tawagar kwamishinoninsa. A ranar Juma'a, 3 ga watan Junairu ne gwamnan ya gabatar da hukuncin a yayin zaman Majalisar Zartarwa inda ya yi godiya gare su bisa ayyukan da suka yi wa gwamnati da mutanen jihar tare da musu fatan alheri. An umarci tsigaggun kwamishinonin da su miƙa harkokin ma'aikatun da suka yi wa aiki da kayan gwamnati ga manyan sakatarorin ma'aikatun. Haka nan shi ma sakataren gwamnati mai barin gado, ya miƙa ragamar aiki ga babban sakataren gudanar…
Read More
Majalisar Dokoki za ta amince da kasafin kuɗin tiriliyan N49.7 na 2025 a Fabrairu

Majalisar Dokoki za ta amince da kasafin kuɗin tiriliyan N49.7 na 2025 a Fabrairu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD An samu bayani game da yadda Majalisar Dokokin ƙasar ke shirin zartar da ƙudurin kasafin kuɗin shekarar 2025 na Naira Tiriliyan 49.7. A bisa tsarin lokacin majalisar, kwamitin haɗin gwiwa na majalisar wakilai kan kasafin kuɗi zai gabatar da rahotonsa kan kasafin kuɗin a ranar Juma’a 31 ga watan Janairun 2025, inda za a kafa tsarin da ake sa ran za a amince da shi a farkon watan Fabrairu. Jadawalin Majalisar ya nuna cewa ana sa ran ma’aikatu da hukumomi za su kare kason su a gaban kwamitocin da abin ya shafa daga ranar Litinin, 7…
Read More
NAFDAC ta sha alwashin saka ƙafar wando ɗaya da dillalan magungunan jabu a 2025

NAFDAC ta sha alwashin saka ƙafar wando ɗaya da dillalan magungunan jabu a 2025

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta ƙasa (NAFDAC) a ranar Lahadi ta yi barazanar saka ƙafar wando ɗaya da waɗanda ta bayyana a matsayin 'dillalan kisa' masu samar da abinci da magungunan jabu a shekarar 2025. Hukumar ta kuma yi alƙƙwarin ƙara zage damtse wajen yaƙi da magunguna marasa inganci da gurɓatattun magunguna da kayayyakin abinci marasa inganci a shekarar 2025. Darakta Janar na NFDAC Farfesa Mojisola Adeyeye ta bayyana hakan a cikin saƙonta na sabuwar shekara, wanda mashawarcin hukumar, Sayo Akintola ya miƙa. Ta kuma tabbatar wa da jama’a cewa ana aiwatar da…
Read More
Kasafin 2025: An shawarci gwamnati ta yi amfani da biliyan N113 a raya ƙasa maimakon sayen motoci

Kasafin 2025: An shawarci gwamnati ta yi amfani da biliyan N113 a raya ƙasa maimakon sayen motoci

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani masani kan harkokin kuɗi, Farfesa Uche Uwaleke, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya da ta karkatar da Naira Biliyan 113 da aka tanadar a cikin ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2025 na sayen motoci zuwa ayyukan samar da ababen more rayuwa a ƙasar. Uwaleke, farfesa ne a fannin kasuwar jari, kuma shi ne Daraktan Cibiyar Nazarin Kasuwar Hannu a Jami’ar Jihar Nasarawa Keffi. Ya bayar da shawarar ne a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ranar Juma’a a Abuja. Ya ce, ya tattara jerin sunayen hukumomin gwamnati 288 da suke jerar sayen motoci a cikin kasafin…
Read More
An shiga fargaba kan ƙaratowar wa’adin Mele Kyari a matsayin shugaban NNPC

An shiga fargaba kan ƙaratowar wa’adin Mele Kyari a matsayin shugaban NNPC

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ana ƙara nuna damuwa dangane da ƙarewar wa’adin Babban Jami’in Kamfanin Man Fetur ta Nijeriya, Mele Kyari, da kuma yiwuwar naɗa sabon shugaban da zai jagoranci harkokin katafaren ɓangaren man. Wasu masu sa ido a masana'antar na ganin cewa shugaban na NNPC, wanda zai cika shekaru 60 a ranar 8 ga Janairu, 2025, na iya ficewa daga kamfanin mai na ƙasa, abin da ke ƙara nuna damuwa game da makomar shugabancin kamfanin nan gaba. Wannan ya zo ne a yayin da wasu mutane suka bayyana cewa, ana sa ran wa’adin Kyari zai ƙare a shekarar 2027,…
Read More
 ‘Yan Nijeriya za su ga bunƙasar arziki da saukar farashin kayayyaki a 2025 – Bagudu

 ‘Yan Nijeriya za su ga bunƙasar arziki da saukar farashin kayayyaki a 2025 – Bagudu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Ministan Kasafin Kuɗi da Tsare-Tsaren, Sanata Abubakar Bagudu, ya tabbatar wa 'yan Nijeriya cewa tattalin arzikin ƙasar zai inganta a shekara mai zuwa duk da cewa gwamnati tana hasashen raguwar hauhawar farashi. Bagudu ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai na Fadar Shugaban ƙasa tare da wasu ministoci bayan taro da Shugaba Bola Tinubu a Legas a ranar Lahadi. Da yake magana kan sabbin manufofin gwamnati, Bagudu ya ce gwamnatin Tinubu ta ɗauki matakai masu wuya, kuma ƙasar ta sha gwagwarmaya mafi muni da za a iya tsammani. "Don haka,…
Read More
Yanzu ake buƙatar haɗin kan al’umma da gwamnati domin farfaɗo da harkar ilimi – Hamisu Rabiu

Yanzu ake buƙatar haɗin kan al’umma da gwamnati domin farfaɗo da harkar ilimi – Hamisu Rabiu

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An bayyana cewa taron tsofaffin ɗalibai da ake wani dandali ne na sada zumunci taron da 'yan makarantar ɗandago suka yi mai albarka ne da tarihi da ba a taɓa irin sa saboda sun ga kakanni da iyaye da yayye da ƙanne, an zo an ga fuskokin juna ko haka kaɗai aka yi aka tashi an yi zumunci. ɗaya daga cikin tsofaffin ɗaliban makarantar 'yan aji na 87 kuma fitaccen ɗan kasuwa shugaban Hamir Global ɓenture Alhaji Hamisu Rabiu ne ya bayyana hakan a yayin taron cikar makarantar firamare na ɗandago shekaru 90 da kafuwa…
Read More