05
Jan
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wani jigo a jam’iyyar PDP kuma tsohon mamba a kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Atiku Abubakar a zaɓen 2023, Dr Adetokunbo Pearse, ya buƙaci jam’iyyar da ta tabbatar da ta fidda ɗan takara daga yankin Kudu a zaɓen shugaban ƙasa na 2027. Pearse, shi ne shugaba kuma daraktan tattara bayanai da ba da rahoto na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na Atiku Abubakar a jihar Legas wanda ya ba da shawarar a yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai ta ƙasa (NAN) a ranar Lahadi a jihar Legas. Ya ce fidda…
