Labarai

Gwamna Abba ya tallafa wa NNPP Kwankwasiyya/Abba Gida-Gida Media Forum da milyan 30

Gwamna Abba ya tallafa wa NNPP Kwankwasiyya/Abba Gida-Gida Media Forum da milyan 30

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bai wa ƙungiyar masu yaɗa manufar gwamnatin shi Kwankwasiyya/Abba Gida-Gida Media Forum tallafin naira miliyan 30. Gwamna wanda ya tabbatar da haka yayin da yake buɗe taron bada tallafin naira 200,000 da shugabanin wannan Ƙungiya suka bai wa ya'yan wannan Ƙungiya dan basu damar samo hanyar dogaro da kai gare su. Gwamna Abba Kabir yace wannan yunƙuri da Ƙungiyar ta yi yana ɗaya daga cikin abinda wannan gwamnati ta sanya a matakin farko baya ga Ilimi dan kawar ma natasa dukkan tunanin da zai sanya su barin…
Read More
Gwamnan Kano ya yi wasu naɗe-naɗe da sa ranar rantsar da sabbin kwamishinoni

Gwamnan Kano ya yi wasu naɗe-naɗe da sa ranar rantsar da sabbin kwamishinoni

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya amince da naɗe-naɗe muƙamai da dama da nufin ƙarfafa gwamnatinsa don gudanar da shugabanci nagari. Ta cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya aiko wa Blueprint Manhaja a yammacin ranar Lahadi, ya bayyana waɗanda aka naɗa kamar haka:Hon. Ahmad Muhammad Speaker a matsayin mai bada shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai; sai Injiniya Ahmad a matsayin mai bada shawara na musamman kan ayyuka; da kuma Malam Sani Abdullahi Tofa a muƙamin mai bai wa gwamna shawara na musamman kan ayyuka…
Read More
Gwamna Abba Kabir ya sake naɗa sabbin muƙamai

Gwamna Abba Kabir ya sake naɗa sabbin muƙamai

Daga RABI'U SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir na Jihar Kano ya sake wasu sababin naɗe-naɗen muƙamai masu muhimmanci don cigaba da kawo canji mafi kyau a tafiya gwamnatin shi. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Malam Sanusi Ahmad Bature ya fitar ga manema labarai. Sanusi Bature ya bada wannan sanarwar mai nuni da cewa waɗanda aka naɗa ɗin za su cigaba da aiki ba tare da ɓata lokaci ba, kama daga Hon Ahmad Muhammad Speaker a matsayin babban mai bai wa gwamna shawara a kan harkokin yaɗa Labarai. Sanarwar tace Ahmad ya…
Read More
‘Yan sanda sun ceto jaririn da aka jefar, sun kama mahaifiyarsa a Abuja

‘Yan sanda sun ceto jaririn da aka jefar, sun kama mahaifiyarsa a Abuja

Daga BELLO A. BABAJI Rundunar ƴan sanda a Abuja a ta yi nasarar ceto wani jariri ɗan kwana ɗaya da haihuwa a kusa da wani juji dake bayan wata kasuwa da aka jingine aikinta a yankin Mpape dake birnin. Kakakin rundunar, SP Josephine Adeh ta faɗi hakan a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta bayyana wa al'umma yadda aka ceto jaririn. Ta ce a safiyar ranar 3 ga watan Junairu ne jami'an rundunar na Mpape suka samu rahoto game da jaririn inda bayan sun garzaya ne sai suka same shi a ƙunshe cikin zani. SP Josephine…
Read More
Rikicin APC a Zamfara: Shinkafi ya rubuta wa Tinubu da Ganduje wasiƙa

Rikicin APC a Zamfara: Shinkafi ya rubuta wa Tinubu da Ganduje wasiƙa

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jigo a jam’iyyar All Progressive Congress (APC) a Jihar Zamfara Dr Sani Abdullahi Shinkafi ya rubutawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da shugaban jam’iyyar APC na Ƙasa Abdullahi Umar Ganduje wasiƙa kan halin rikicin dake neman kunno Kai a jam’iyyar ta APC na yunƙurin ɗora ‘yan takara a zaɓen 2027, inda ya bayyana cewar hakan ba zai ƙara yin aiki a jihar ba. Dakta Shinkafi wanda ya bayyana cewar ya tsallake rijiya da baya a wani yunƙurin hallaka shi a ranar Juma’ar da ta gabata da wasu da ake zargin ‘yan bangar siyasa ne suka…
Read More
Gwamnatin Katsina za ta ɗauki ma’aikata 70 da za su kula da dazuka

Gwamnatin Katsina za ta ɗauki ma’aikata 70 da za su kula da dazuka

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya bada umarnin ɗaukan ma'aikata guda saba'in da za su kula da dazukan da ke jihar. Wannan mataki da gwamnati ta ɗauka ya biyo bayan rahoton da ya samu na cin iyaka da saran itace ba bisa ƙa’ida ba a dazuka na gwamnati tun shekara 2017 zuwa yanzu. Gwamna Raɗɗa ya ce ayyukan ma'aikatan dajin shine kula da sa ido kan masu saran itace ba bisa ƙa'ida ba da musu cin iyaka a dazukan, sanarwar ta ce. Gwamna Dikko Raɗɗa ya amince wa ma'aikatar aikin gona ta kula da…
Read More
Yan Sanda a Katsina sun kuɓutar da mutane 18 daga hannun ‘yan bindiga

Yan Sanda a Katsina sun kuɓutar da mutane 18 daga hannun ‘yan bindiga

' Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan sanda a Katsina sun sami nasarar kuɓutar da mutane 18 da suka fito daga ƙaramar hukumar Batsari za su garin Yankara da ke ƙaramar hukumar Faskari. 'Yan bindigan sun tare motocin hayar guda huɗu ɗauke da waɗannan mutane a hanyar Funtua zuwa Gusau. Jami'in yaɗa labarai na rundunar 'yan sanda a Katsina ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya shaidawa manema labarai haka a Katsina. Ya faɗa cewa motocin haya ɗauke da waɗannan mutane akan hanyar su na zuwa Yankara su kai karo da 'yan bindiga a babban hanyar Funtua zuwa Gusau. Ko da samun…
Read More

Ba na goyan bayan yaɗa hotunan masu aikata laifuka a soshiyal mediya – Injiniya Aliyu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Injiniya Rabiu Aliyu, Shugaban kamfanin Syrol Technologies ya wallafa hakan a shafukansa na sada zumunta a ranar Juma'a inda ya ce, "Wace doka ce ta bai wa ƴan sanda damar yaɗa waɗanda ake zargi da laifi a social media? Mene ne yasa a Jihar Kano da wasu jihohin Arewa ne kaɗai ake daukar video/hoton waɗanda ake zargi da laifi ba tare da hukuncin kotu ba a yaɗa?" "EFCC suma sukan yaɗa hotunan masu laifi, saidai mafi yawanci bayan masu laifin suke ɗauka domin su ɓoye fuskokinsu da identity nasu. Haka zalika a shawran jihohin ƙasar.…
Read More

Gwamna Ƙaura ya ƙaddamar da Hukumar BAROTA a Bauchi

Daga BELLO A. BABAJI Gwamna Bala Abdulƙadir Mohammed na jihar Bauchi, ya yi alƙawarin cewa gwamnatinsa ba za ta tsoma baki cikin ayyukan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Bauchi (BAROTA) da aka kafa ba, yana mai jaddada buƙatar yin gaskiya da nuna sanin makamar aiki a hukumar. Da ya ke jawabi a bikin ƙaddamar da rukunin farko na kadet na jami'an BAROTA 500 da Marshal a filin wasa na Dakta Rilwanu Sulaiman Adamu da ke gidan gwamnatin Bauchi, gwamnan ya bayyana cewa an samar da BAROTA ne domin magance matsalolin da suka addabi sha'anin zirga-zirgar ababen hawa,…
Read More
Mataimakin shugaban majalisar wakilai ya karɓi ‘yan jam’iyyun adawa 3,000 da su ka koma APC 

Mataimakin shugaban majalisar wakilai ya karɓi ‘yan jam’iyyun adawa 3,000 da su ka koma APC 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mataimakin shugaban majalisar wakilai, Benjamin Okezie Kalu, ya karɓi sabbin mambobi sama da 3,000 daga jam’iyyun siyasa daban-daban zuwa jam’iyyar APC a jihar Abia a hukumance. Jaridar ɓanguard ta rawaito cewa an karɓi sabbin 'yan APC din ne a Akwete da ke Ndoki a ƙaramar hukumar Ukwa ta Gabas a yayin wani shirin bayar da tallafi da Hon. Chris Nkwonta, mamba mai wakiltar Ukwa ta Gabas da Ukwa ta Yamma a majalisar wakilai ya shirya. Da yake jawabi ga ɗimbin jama’a da ga Ukwa ta gabas da kuma Ukwa ta Yamma, Kalu ya yi…
Read More