Labarai

An kashe ‘yan sanda biyu da kora shanu sama da 500 a Kebbi

An kashe ‘yan sanda biyu da kora shanu sama da 500 a Kebbi

Daga JAMEEL GULMA a Kebbi Rahotanni daga ƙaramar hukumar Argungu da ke Jihar Kebbi sun nuna cewa waɗansu mutane da a ke sa ran Lakurawa ne masu da'awar musulunci da ke ƙwace dabbobin mutane musamman shanu da sunan suna karɓar zakka sun kai farmaki a wani ƙauyen Natsini mai tazarar kilomita bakwai tsakanin shi da garin Argungu, inda suka kashe 'yan sanda biyu da ke aiki a kan babbar hanyar da ta haɗa ƙananan hukumomin Argungu da Augie da kuma Jamhuriyar Nijar sannan kuma suka farwa wani gidan gona mallakar Alhaji Lauwali Abdullahi (Lauwali Black) suka yi awon gaba da…
Read More
Matatar mai: Yar’Adua bai amince da Dala miliyan 750 da Ɗangote ya ba NNPC ba – Obasanjo

Matatar mai: Yar’Adua bai amince da Dala miliyan 750 da Ɗangote ya ba NNPC ba – Obasanjo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon shugaban ƙasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana wasu sababbin bayanai da suka shafi ƙalubalen da matatun man Nijeriya ke fuskanta, ciki har da yunƙurin mayar da matatun zuwa wani kamfani da bai yi nasara ba da kuma asarar kuɗaɗe da aka yi a ƙarƙashin gwamnati. A wata tattaunawa ta musamman da ya yi da gidan talabijin na Channels Tɓ, wanda Wakilinmu ya sa ido a ranar Alhamis, Obasanjo ya tattauna batun matatun mai na Fatakwal, Warri da Kaduna, inda ya jaddada ƙoƙarinsa na neman taimako daga waje domin gyara su da kuma kula…
Read More
Zargin ta’addanci: Jamhuriyar Benin ta nuna ɓacinta ga iƙirarin Janar Tchiani

Zargin ta’addanci: Jamhuriyar Benin ta nuna ɓacinta ga iƙirarin Janar Tchiani

Daga SANI HAMAD GIWA a Abuja A ranar Talatar da ta gabata ne Jamhuriyar Benin ta gayyaci jami’in diflomasiyyar Jamhuriyar Nijar bayan zargin da shugaban mulkin sojan Jamhuriyar Nijar, Birgediya Janar Abdourahamane Tchiani, ya yi na cewa, ƙasashe masu makwabta da Nijar suna goyon bayan ‘yan ta’adda a yammacin Afirka. Benin dai na neman ƙarin haske daga jami'in diflomasiyyar ne bayan da Tchiani ya zargi ƙasar da zama magoya baya ga 'yan ta'adda da kuma son tada zaune tsaye a Nijar. Ministan harkokin wajen ƙasar Benin Olushegun Bakari ya aike da wasiƙar zanga-zangar a hukumance ga jami'in diflomasiyyar. "Saboda zarge-zargen…
Read More
Yadda na rasa mahaifiyata da ɗana bayan auren ɗiyata – Gwamna Namadi

Yadda na rasa mahaifiyata da ɗana bayan auren ɗiyata – Gwamna Namadi

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, a ranar Lahadin da ta gabata, ya bayyana cewa ɗansa, Abdulwahab, da mahaifiyarsa, Hajiya Maryam, sun rasu kimanin mako guda da auren ɗiyarsa, Fatiha. Idan za a iya tunawa, ɗan gwamnan ya rasu a makon da ya gabata a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi sa’o’i 24 kacal bayan mahaifiyarsa ta rasu sakamakon rashin lafiya. A ranar Lahadin da ta gabata ne Gwamnan Jihar Gombe kuma Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa, Muhammadu Yahaya, ya jagoranci tawagar da suka kai ziyarar jaje a garin Kafin Hausa da ke Jihar…
Read More
Yadda muka shawo kan Tinubu ya ƙi karɓar tayin minista a gwamnatin Yar’Adua – Ojudu

Yadda muka shawo kan Tinubu ya ƙi karɓar tayin minista a gwamnatin Yar’Adua – Ojudu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babafemi Ojudu, tsohon mashawarcin tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari na musamman kan harkokin siyasa, ya bayyana yadda shi da sauran muƙarrabansa suka shawo kan Shugaba Bola Tinubu kan ya ƙi amincewa da tayin zama ministan kuɗi a ƙarƙashin Marigayi Shugaba Umaru Yar’adua. Ojudu ya bayyana hakan ne a yayin da yake bayyanawa kan harkokin jiha, wani faifan bidiyo wanda Edmund Obilo ya shirya, ranar Litinin. Ya yi nuni da cewa karɓar wannan aiki zai haifar da babbar barazana ta siyasa ga Tinubu, wanda a lokacin shi ne jagoran jam’iyyar Action Congress. "Wata rana Tinubu…
Read More
Tinubu zai halarci taron rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ghana, Mahama

Tinubu zai halarci taron rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban Ghana, Mahama

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Litinin, 6 ga watan Junairu, 2025 ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja zuwa Accra, Babban Birnin ƙasar Ghana domin halartar taron rantsar da zaɓaɓɓen Shugaban ƙasar, John Dramani Mahama wanda za a yi a ranar 7 ga wata. Mahama shi ne ya zama Shugaban ƙasar na 12 a lokacin da aka zaɓe shi a shekarar 2011 zuwa 2017 wanda daga bisani a watan Disambar 2024 aka sake zaɓan sa inda zai gaji Nana Akuffo-Addo wanda ya jagoranci ƙasar daga 2017 zuwa 2025. Shugaba Tinubu zai halarci taron ne bayan gayyata ta musamman…
Read More
Hukumar lafiya ta duniya ta  bayyana ɓarkewar annobar  Korona

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana ɓarkewar annobar Korona

Hukumar lafiya ta duniya (WHO) ta ayyana ɓarkewar annobar Korona a ƙasar Sin a matsayin lamari mai buƙatar gaggawa. Babban daraktan WHO, Tedros Ghebreyesus, ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai da aka gudanar a birnin Geneva. Kwamitin WHO kan wannan annoba ya gudanar da taro a ranar Alhamis da ta gabata, inda suka bada shawarar ayyana wannan ɓarkewar a matsayin babbar matsalar lafiya da ke buƙatar gaggawa (PHEIC). Shugaban kwamitin, Didier Houssin, ya bayyana cewa shawarar da aka yanke kusan duka membobi ne suka amince da ita a taron. A cewar Tedros, “Babban dalilin wannan ayyanawa,…
Read More
‘Yan bindinga sun kashe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na Katsina

‘Yan bindinga sun kashe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah na Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Wasu mutane da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne sun kashe shugaban ƙungiyar Miyetti Allah reshen jihar Katsina, Alhaji Amadu Surajo a ƙauyen Mai Rana da ke ƙaramar hukumar Kusada ta Jihar Katsina. Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq, ya tabbatar da faruwar lamarin da yammacin ranar Lahadi, cikin wata tattaunawa da ya yi da manema labarai a birnin Katsina. "DPO ya sanar da ni cewa lamarin ya faru ne a daren jiya," in ji kakakin rundunar. Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Katsina, Dakta Nasir Mu'azu ya bayyana…
Read More
Gwamna Abba ya amince da buƙatar ajiye aikin Diggol

Gwamna Abba ya amince da buƙatar ajiye aikin Diggol

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya amince da buƙatar ajiye aikin Kwamishinan bibiyar ayyuka Hon Engr Muhammad Diggol ba tare da ɓata lokaci ba. Wannan na ɗauke ne a wata sanarwa da Kakakin gwamnan Sanusi Bature ya fitar ga manema labarai a daren jiya. Diggol wanda akayi ma naɗin matsayin kwamishinan ma'aikatar Sufuri ta jihar Kano bayan samun nasarar gwamna Abba Kabir Yusuf a zaɓen da ya gabata na 2023, daga bisani gwamnan ya canza mashi ma'aikata ta bibiyar ayyukan gwamnati da tabbatarwa. Gwamna wanda ya miƙa saƙon godiyar shi ga tsohon Kwamishinan…
Read More
Shugaban asibitin ƙwararru na Best Choice ya taya Gwamnan Kano murnar cika shekaru 62

Shugaban asibitin ƙwararru na Best Choice ya taya Gwamnan Kano murnar cika shekaru 62

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban Asibitin Best Choice dake jihar Kano, Alhaji Auwal Lawal Muhammad ya taya Gwamna Abba Kabir Yusuf murnar cika shekaru 62 da haihuwa inda ya bayyana shi a matsayin shugaba mai hangen nesa da himma wajen yi wa al’umma hidima. Cikin wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannunsa, Shugaban asibitin yaba da nasarorin da gwamnan ya samu a fannin Ilimi, Kiwon lafiya, da samar da ababen more rayuwa, yana mai cewa hakan na nuni da irin kishi da jajircewarsa wajen cigaban jihar. Ya kuma yaba wa ƙoƙarin da gwamnan ya yi cikin ƙanƙanin lokaci inda…
Read More