07
Jan
Daga USMAN KAROFI Hukumar da ke yaƙi da cututtuka masu yaɗuwa NCDC ta fitar da wata sanarwa domin wayar da kan jama’a da ɗaukar matakan kariya kan barazanar cutar Human Metapneumovirus (HMPV). Wannan na zuwa ne sakamakon rahotanni daga ƙasashen Sin, Birtaniya, da wasu sassa na duniya da ke nuna ƙaruwar yawan masu kamuwa da cutar. HMPV wata cuta ce ta numfashi da ke haifar da alamun mura mai sauƙi har zuwa matsanancin ciwon numfashi, musamman ga ƙananan yara, tsofaffi, da masu ƙarancin garkuwar jiki. HMPV na yaduwa ta hanyar fitar iska daga hanci ko baki, cuɗanya da mai ɗauke…
