Labarai

Ba za mu lamunci shashanci a gwamnatinmu ba – Gwamna Abba ga sabbin kwamishinoni

Ba za mu lamunci shashanci a gwamnatinmu ba – Gwamna Abba ga sabbin kwamishinoni

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya bayyana ƙudurin shi na ɗaukar matakin daya kamata ga dukkan kwamishinan daya kawo masu wasa a gwamnatin su. Alhaji Abba Kabir ya bayyana haka ne a yayin zaman majalisar zartarwa karo na 23 da ake gudanarwa a duk lokacin da ya kamata dan bayyana ma al'ummar Jihar Kano dukkan abinda yakamata su samu da kuma sani game da gwamnatin da suka zaɓa. ''Yanzu, kuma a wannan lokaci da muke ciki ba zamu lamunci dukkan wani shashanci ba, dan haka dukkan kwamishinan da ya kawo mana wargi ko…
Read More
Mai ba gwamnan Kano shawara ya rasu kwana ɗaya da rantsar da shi

Mai ba gwamnan Kano shawara ya rasu kwana ɗaya da rantsar da shi

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Sabon mai bai wa gwamnan Kano shawara kan ayyuka, Injiniya Ahmad Ishaq Bunkure ya rasu, kwana ɗaya da gwamna Abba Kabir Yusuf ya rantsar da shi a gidan gwamnati. A wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya rabawa manema labarai, marigayin ya rasu a yau Laraba a ƙasar Masar. Ya ce Gwamna Yusuf, wanda ya nuna kaɗuwa ga rasuwar Bunkure, ya bayyana mutuwar ta sa a matsayin babban rashi ga iyalinsa da ma Kano baki ɗaya. “Wannan wani yanayi ne na kaɗuwa da alhini saboda Injiniya Bunkure mutum ne…
Read More
Sojoji shida da ƴan ta’adda 34 sun mutu a harin sansanin sojoji a Borno – Hedikwatar Tsaro

Sojoji shida da ƴan ta’adda 34 sun mutu a harin sansanin sojoji a Borno – Hedikwatar Tsaro

Daga BELLO A. BABAJI Hedikwatar Tsaro (DHQ) ta tabbatar da mutuwar ƴan ta'adda 34 da sojoji 6 sakamakon wani hari a sansanin sojoji dake Sabon Gari a ƙaramar hukumar Damboa a Jihar Borno. Daraktan yaɗa Labarai, Manjo-Janar Edward Buba ya bayyana hakan a wata sanarwa, inda ya ce kawo yanzu ba a bayyana sojojin da suka rasa rayukan nasu ga iyalansu ba wanda za a yi hakan a hukumance nan ba da jimawa ba. Edward Buba ya ce ƴan ta'addar sun kai harin ne a wani yunƙuri na ramuwa sakamakon kashe wani kwamandansu da sojoji suka yi. A lokacin da…
Read More
An sako mutumin Kano, Mubarak Bala da aka tsare a kurkuku bisa ɓatanci ga addini

An sako mutumin Kano, Mubarak Bala da aka tsare a kurkuku bisa ɓatanci ga addini

Daga BELLO A. BABAJI Wani mazaunin Kano mai suna Mubarak Bala ya samu ƴanci daga gidan yari bayan shekaru huɗu da aka tsare shi bisa laifin ɓatanci. Mubarak Bala mai shekaru 40 an maka shi a kotu ne sakamakon samun sa da laifuka 18 na wasu abubuwa da ya wallafa a shafin Facebook a shekarar 2020. A lokacin da BBC take hira da shi, Mubarak ya ce an yi ta nuna damuwa kan halin da yake ciki daga masoya da makusanta. Nijeriya dai ƙasa ce da ta bada muhimmanci matuƙa game da lamuran da suka shafi addini, don haka ne…
Read More
Abinda ya kamata mu sani akan cutar HMPV

Abinda ya kamata mu sani akan cutar HMPV

Daga USMAN KAROFI A cikin 'yan kwanakin nan, cutar da ake kira Human Metapneumovirus (HMPV) ta yi tsanani a yankunan Arewa maso gabashin ƙasar Sin, inda ta fi addabar yara. Wannan annoba ta haifar da cunkoson marasa lafiya a asibitoci, abin da ya tuna wa mutane da farkon bayyanar cutar Covid-19. Hukumar kula da cututtuka ta ƙasar ta bayyana cewa adadin masu kamuwa da cutar ya ƙaru sosai a wannan lokaci fiye da na bara. HMPV tana haifar da alamomi makamantan mura, kamar tari, rashin lafiya, zazzabi, da kumburin hanci. Duk da haka, tana iya haifar da matsaloli masu tsanani…
Read More
Tinubu ya dawo Abuja daga Ghana

Tinubu ya dawo Abuja daga Ghana

Daga USMAN KAROFI Shugaba Bola Tinubu ya dawo Abuja bayan kusan makonni uku baya Abuja.Jirgin Airbus A330 da ya ɗauko Shugaban ƙasar da muƙarrabansa ya sauka a filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe, Abuja, da misalin ƙarfe 10:30 na dare. Tinubu ya samu tarba daga shugaban ma’aikatansa, Femi Gbajabiamila, mai ba da shawara kan tsaron ƙasa, Nuhu Ribadu, da sauran manyan jami’an tsaro. Tinubun ya dawo ne daga Accra, Ghana, inda ya halarci rantsar da Shugaba John Mahama a ranar Talata. A yayin tafiyarsa daga Abuja, shugaban ƙasar ya kuma ziyarci Jihar Enugu. A ranar 18 ga Disamba, 2024, shugaba Tinubu…
Read More
NFF ta naɗa kocin Super Eagles na dindindin

NFF ta naɗa kocin Super Eagles na dindindin

Daga USMAN KAROFI Hukumar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya (NFF) ta amince da naɗin Éric Sékou Chelle a matsayin sabon kocin tawagar ƙwallon ƙafa ta Nijeriya, Super Eagles. Wannan naɗin ya biyo bayan shawarar kwamitin da ke da alhakin zaɓen kocin ya bayar, wanda ya gabatar da sunan Chelle a taron da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis, 2 ga Janairu, 2025. Chelle, wanda ya taɓa horar da tawagar ƙwallon ƙafa ta Mali tun daga 2022, ya taka rawar gani a gasar cin kofin Afrika na 2023 da aka gudanar a Cote d’Ivoire, inda tawagarsa ta kusa kai wa matakin kusa…
Read More
ICPC ta maka tsohon hadimin El-Rufa’i kotu bisa zargin almundahana

ICPC ta maka tsohon hadimin El-Rufa’i kotu bisa zargin almundahana

Daga USMAN KAROFI Hukumar ICPC ta gurfanar da tsohon shugaban ma’aikatan tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, Alhaji Muhammad Bashir Saidu, a gaban babbar kotun tarayya da ke Kaduna. Haka kuma an gurfanar da wani jami’i a ma’aikatar kuɗi, Ibrahim Muktar, bisa tuhumar da suka shafi zargin almundahana da karkatar da kuɗaɗe. Bisa ga tuhumar da ake yi ƙarƙashin lamba FHC/KD/IC/2025, ana zargin Bashir Saidu, wanda ya taɓa zama Kwamishinan Kudi na Kaduna, da karɓar kuɗaɗe da suka haura Naira miliyan 155 a watan Maris na shekarar 2022, ta hannun wani hadiminsa mai suna Muazu Abdu. Hukumar ICPC ta bayyana…
Read More
Nijeriya za ta taimaka wa Ghana – Tinubu ga sabon shugaban ƙasar

Nijeriya za ta taimaka wa Ghana – Tinubu ga sabon shugaban ƙasar

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya taya Shugaba John Mahama na Ghana bisa rantsar da shi da aka yi, ya na mai cewa Nijeriya za ta taimaka wa ƙasar ta hanyoyin da suka dace. A ranar Talata ne aka rantsar da Mahama a matsayin shugaban ƙasar bayan shekaru da dama da ya jagoranci ƙasar a baya. Shugaba Tinubu yana ɗaya daga cikin shugabannin da suka halarci taron rantsarwar, ya na mai jaddada ƙarfin abota da alaƙar dake tsakaninsa da Mahama da kuma ƙasarsa ta Ghana. A shekarun 2012 zuwa 2017 ne Mahama ya shugabanci Ghana bayan nasara…
Read More
Nijeriya ta yi nasarar haƙo gangar mai Milyan 1.5 a karon farko cikin shekaru huɗu

Nijeriya ta yi nasarar haƙo gangar mai Milyan 1.5 a karon farko cikin shekaru huɗu

Nijeriya ta yi nasarar cimma burinta na cike giɓin da take samu wajen haƙo mai wanda ƙungiyar ƙasashe masu albarkatun mai OPEC ta kayyade mata na haƙo ganga miliyan 1.5 a kowace rana. Wannan shinekaron farko cikin shekaru huɗu da Nijeriya ta sami irin wannan gagarumar nasara tun bayan dawowar matsalar masu fasa bututun mai da gwamtocin baya suka fuskanta. Wasu alƙaluman binciken Bloomberg sun nuna cewa yawan man da Nijeriya ke haƙowa ya ƙaru da ganga 40,000 zuwa miliyan 1.51 a watan Disambar bara. A baya dai ƙungiyar OPEC ta ware wa Nijeriya damar haƙo ganga Milyan 1.8 a…
Read More