10
Jan
Daga BELLO A. BABAJI Jami'an ƴan sanda biyu ne suka rasa rayukansu sakamakon wani harin boma-bomai da wasu mayaƙan Boko Haram suka kai a ofishin rundunar da ke garin Gajiram na ƙaramar hukumar Nganzai a Jihar Borno. Haka ma wani jami'in ƴan sandan ya samu mummunan rauni a yayin da aka yi ba-takashi tsakanin ɓangarorin biyu inda a lokacin ne jami'an haɗaka na CJTF da ke kusa da ofishin suka kawo ɗauki tare da fatattakar ƴan ta'addar. Wata majiya daga jami'an tsaro ta ce mayaƙan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 11 na dare a ranar Laraba. Ta ce…
