10
Jan
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta tabbatar cewa za a ƙara kuɗin kiran waya da data, amma ba da kashi 100 kamar yadda kamfanonin sadarwa suka nema ba. Ministan Sadarwa da Tattalin Arziƙi, Dokta Bosun Tijani ne, ya bayyana hakan bayan wata tattaunawa da kamfanonin sadarwa a Abuja. Ya ce ana ci gaba da tattaunawa, kuma Hukumar Sadarwa ta Nijeriya (NCC) za ta sanar da sabon tsarin kuɗin nan ba da jimawa ba. “Mun fahimci buƙatar ƙarin kuɗin, amma ba za a ƙara zuwa kashi 100 ba. “Burinmu shi ne kare masu amfani da sadarwa tare da…
