Gwamnatin Jihar Oyo ta sanar a ranar Juma’a cewa Gwamna Seyi Makinde ya amince da naɗin Yarima Abimbola Akeem Owoade a matsayin sabon Alaafin na Oyo.
A cewar wata sanarwa da Kwamishinan bayanan gwamnati da wayar da Kan al’umma na Jihar Oyo, Prince Dotun Oyelade ya sanya wa hannu, gwamna Makinde ya amince da zaɓen Prince Owoade bayan shawarar da aka yanke daga Oyomesi.
Kwamishinan ya bayyana cewa Oyomesi, bayan tuntuɓa da amfani da dabaru na al’ada, sun bayar da shawararsu ga gwamnan Jihar Oyo wanda ya amince da naɗin Prince Owoade a matsayin sabon Sarkin Oyo.
Prince Oyelade ya ƙara jaddada cewa sanarwar naɗin ta fito ne daga bakin Kwamishinan harkokin Ƙananan hukumomi da masarautu, Hon. Ademola Ojo, wanda ya ce wannan sanarwa ta kawo ƙarshen duk wata gardama da ta biyo bayan rasuwar Marigayi Mai Martaba, Oba Lamidi Olayiwola Adeyemi III, a ranar 22 ga Afrilu, 2022.
Hon. Ojo ya yi kira ga dukkan al’ummar jihar da su taya gwamnati murnar wannan babban lokaci tare da bayar da goyon bayansu ga sabon Alaafin na Oyo.
Kwamishinan ya yi addu’ar cewa Allah ya sanya zamanin mulkinsa ya zama mai cike da zaman lafiya, ci gaba, da haɗin kai a masarautar tarihi ta Oyo.