Kowa ya kama gabansa idan Nijeriya ba ta zaunuwa – Igboho

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Mai fafutukar kafa ƙasar Yarabawa, Sunday Adeyemo, wanda aka fi sani da Sunday Igboho, ya nemi ƙabilun Nijeriya su kama gabansu matuƙar Nijeriya ba ta tsaya da ƙafarta ba, yana mai cewa, da yawa daga cikin ‘yan ƙasar ba su alfahari da bayyana kansu a matsayin ‘yan ƙasar da ke yammacin Afrika.

A wani faifan bidiyo da aka gani ta yanar gizo a ranar Alhamis, Igboho, wanda aka gani a filin jirgin sama a ƙasar Birtaniya, ya ce, cin hanci da rashawa, rashin tsaro da kuma taɓarɓarewar tattalin arziki ne ke janyo rashin kishin ƙasar.

Ya yi tsokaci na musamman kan rashin tsaro a filayen jiragen saman Nijeriya, inda ya ce, galibi ana sace kayan matafiya.

A cewar Igboho, matasan Yarabawa da suka samu ilimi da gogewa ta hanyar tafiye-tafiye a faɗin duniya, suna da sha’awar samun ƙasar Yarabawa, wacce za ta samu sauyi.

Ya ce, da gwanintarsu za a iya gina ƙasar Yarabawa, ta kuma rikiɗe ta zama al’umma ta zamani mai wadata, kwatankwacin yadda ake yi a nahiyar Turai.

Ya ce: “Ko a cikin filin jirgin, babu tsaro. Za su iya sace kayanka a cikin jakarka (a filayen jirgin saman Nijeriya). Duk waɗannan abubuwa ne ke hana mutane yin alfahari da ƙasar Nijeriya.

“Abubuwa irin wannan suna sa mu baƙin ciki da bayyana kanmu a matsayin ’yan Nijeriya. Wannan shine dalilin da ya sa muke ba da shawarar rabuwa. Idan Nijeriya ba ta aiki a matsayin ƙasa, yana da kyau mu bi hanyoyinmu daban-daban.

“Matasan mu (Yarabawa) za su canza al’ummar Yarabawa. Yawancinsu sun zagaya ko’ina cikin duniya kuma sun koyi abubuwa da yawa. Idan suka dawo ƙasar Yarabawa, ilimin zai taimaka musu wajen gina ta da kuma kawo sauyi ga al’umma kamar na Turai.”

Ku tuna cewa a watan Fabrairun 2024, mai tayar da kayar baya na Yarabawa ya koma shekaru uku bayan ya gudu zuwa Jamhuriyar Benin.

A watan Yulin 2021, an kama Igboho tare da matarsa, Ropo, a Cotonou, Jamhuriyar Benin, kuma an tsare su bisa buƙatar gwamnatin Nijeriya.

Igboho ya tsere daga Nijeriya ne bayan da jami’an tsaro na farin kaya (DSS) suka kai samame gidansa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo, a ranar 1 ga Yuli, 2021.

Samamen ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu yayin da aka kama wasu mataimakansa 12.

Hukumar DSS dai ta yi zargin cewa Igboho na tara makamai, inda daga bisani ta bayyana cewa ana neman sa.

Yunƙurin da gwamnatin Nijeriya ta yi na mayar da shi Nijeriya bayan kama shi ya ci tura.