Labarai

Sufeton ƴan sanda ya umarci a ɗauki mataki akan waɗanda suka kai hari ofishin rundunar a Borno

Sufeton ƴan sanda ya umarci a ɗauki mataki akan waɗanda suka kai hari ofishin rundunar a Borno

Daga BELLO A. BABAJI A ranar Juma'a ne Sufeton ƴan sanda, Kayode Egbetokun ya umarci a ɗauki mataki akan waɗanda suka kai hair a ofishin rundunar dake Nganzai a Jihar Borno. A ranar Alhamis ne harin mayaƙan Boko Haram ya yi sanadiyyar mutuwar ƴan sanda biyu a yayin wani ba-takashi tsakanin ɓangarorin biyu inda aka samu ɗauki daga jami'an haɗaka na CJTF. A lokacin da ya ke tsokaci game da lamarin, Sufeton ƴan sandan ta ofishin jami'in yaɗa labaran rundunar, Muyiwa Adejobi ya bayyana sunayen jami'an da suka rasa rayukan nasu a matsayin Sufeto Bartholomew Kalawa da kuma Koforal Mustapha…
Read More
Shirin daƙile ta’addanci don samar da tsaro a makarantu

Shirin daƙile ta’addanci don samar da tsaro a makarantu

A kwanakin baya ne dai rahotanni suka ce gwamnatocin jihohi da hukumomin tsaro da ma’aikatu sun yanke shawarar haɗa ƙarfi da ƙarfe domin magance ta’addanci da nufin samar da ingantaccen tsaro a makarantu. Manufar ita ce a motsa masu ruwa da tsaki don ba da gudummawa ga shirin, don samar da kuɗaɗe da samar da ingantaccen ilimi a Nijeriya. Baya ga samar da tsaro a makarantu ga yara, haka kuma don a rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Nijeriya. An fara ƙaddamar da shirin ne mai suna ‘Safe school initiatiɓe’ a ranar 7 ga Mayun 2014, don…
Read More
Yadda saƙon da gwamnan Bauchi ya bai wa Sheikh Jingir zuwa Tinubu ya ɗauki hankali

Yadda saƙon da gwamnan Bauchi ya bai wa Sheikh Jingir zuwa Tinubu ya ɗauki hankali

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kalaman da gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammad, ya yi wa fitaccen malamin addini Sheikh Yahaya Jingir game da mawuyacin halin da ake ciki a Nijeriya na ci gaba da jan hankalin jama'a musamman a shafukan sada zumunci. Cikin wani bidiyon da ya karaɗe shafukan sada zumunta, an ga Gwamnan Bala Mohammed, na jawabi ga Sheikh Jingir a fadar gwamnatin Bauchi lokacin da shehin malamin ya kai masa ziyarar ta'aziyar rashin matar mahaifinsa. An jiyo gwamnan na shaida wa Sheikh Jingir cewa ya kamata ya faɗa wa Shugaban ƙasa Bola Tinubu halin da ƙasar…
Read More
Nijeriya ta bukaci MDD ta binciki yadda Boko Haram ke samun kuɗaɗe da horo

Nijeriya ta bukaci MDD ta binciki yadda Boko Haram ke samun kuɗaɗe da horo

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Najeriya ta yi kira ga Majalisar ɗinkin Duniya da ta gudanar da bincike kan yadda ake samar da  kudade da horar da ‘yan ta’addan Boko Haram. Blueprint ta rawaito cewa Babban Hafsan Tsaro na ƙasar, Janar Christopher Musa, ne ya yi wannan kiran a wata hira da ya yi da Al-Jazeera kwanan nan. Musa ya bayyana cewa akwai wata hanyar samun kudade ta duniya ga ‘yan ta’addan, inda ya jaddada bukatar Majalisar dinkin duniya ta shiga don gano asalin kudaden. Janar din ya tambayi yadda 'yan ta’addan su ka samu damar tsayawa tsawon shekaru…
Read More
Abin da na tattauna da El-Rufa’i da wasu – Shugaban SDP

Abin da na tattauna da El-Rufa’i da wasu – Shugaban SDP

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban jam'iyyar SDP na ƙasa, Shehu Gabam ya fitar da jawabin da suka tattauna da jigo a jam'iyya mai mulki ta APC, Malam Nasiru El-Rufa'i. Gabam ya gabatar da hakan ne a yayin hira da gidan talabijin na 'channels' a ranar Alhamis inda ya ce babu laifi acikin tattaunawa da jami'yyarsa ta yi da tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufa'i. Ya ce, "Mai ya sa ake damuwa game da tattaunawa da tsohon gwamnan da Segun Sowunmi" da aka ce ba su da muhimmanci, inda ya ƙalubalanci rashin ba su muƙaman da suka nema na inganta harkokin gwamnati. Jagoran…
Read More
Gwamnan Dauda ya gana da ministan kiwo, ya ce Zamfara ta shirya wa kiwon zamani

Gwamnan Dauda ya gana da ministan kiwo, ya ce Zamfara ta shirya wa kiwon zamani

Daga BELLO A. BABAJI Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar wa sabuwar Ma'aikatar Ci-gaban Kiwo da aka samar a Nijeriya cewa jiharsa ta na da wadataccen filaye na gudanar da harkokin kiwo. Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyara ga Ministan Ma'aikatar, Alhaji Idi Maiha a Hedikwatarta dake Abuja. Wata sanarwa da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris ya fitar, ta ce gwamnan ya jaddada cewa Zamfara jiha ce mai arziƙin harkar noma da kiwo, saboda haka za ta taimaka matuƙa wajen ayyukan ma'aikatar. Gwamna Dauda ya bayyana muradin Gwamantinsa tana bada haɗin kai ga samun nasarori a…
Read More
China ta ware Dala miliyan 255 domin kammala aikin jirgin ƙasan Kano-Kaduna

China ta ware Dala miliyan 255 domin kammala aikin jirgin ƙasan Kano-Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Bankin ƙasar China ya amince da bayar da Dala miliyan 254.76 domin kammala aikin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna. Bankin ya amince ya ba da rancen ne gabanin ziyarar da Ministan Harkokin Wajen China, Mista Wang Yi, zai kawo Nijeriya a wannan makon, inda ya gana da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba. Aikin titin jirgin ƙasa daga Kano zuwa Kaduna mai nisan kilomita 203 zai ci kuɗi Dala miliyan 973, kuma zai sada su da Abuja. Aikin ya samu tsaiko amma Bankin na a China ya ba da tabbacin samar da…
Read More
Mista Abraham Ekpo ƙwararren sakatare ne, cewar Shugaban ƙaramar Hukumar Karu

Mista Abraham Ekpo ƙwararren sakatare ne, cewar Shugaban ƙaramar Hukumar Karu

Daga JOHN D. WADA a Lafiya Sabon Shugaban ƙaramar Hukumar Karu a jihar Nasarawa, Honorabul Barista Abubakar Aliyu Madaki ya yaba wa sabon babban sakatarensa na ƙaramar hukumar Mista Abraham Ekpo dangane da aiki tuƙuru da kuma ƙwarewarsa a aikin na sakatare. Shugaban ƙaramar hukumar Honorabul Barista Abubakar Aliyu Madaki ya bayyana haka ne a zantawarsa da wakilinmu a sakatariyar ƙaramar hukumar dake Karu ranar Laraba na mako da ake ciki. Ya ce tabbas da shi da sauran shugabannin ƙaramar hukumar ba su yi zaɓin duhun dare ba na zaƙulo Mista Abraham Ekpo tare da na da shi babban muƙamin…
Read More
’Yan bindiga sun sace mutane 46 a Zamfara 

’Yan bindiga sun sace mutane 46 a Zamfara 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 'Yan bindiga a jihar Zamfara sun yi garkuwa da aƙalla mutane 46 yayin wani hari da su ka kai kan al'ummar garin Gana da ke jihar. Rfi ta rawaito cewa masu tayar da hankali na zuwa a dai dai lokacin da wasu majiyoyi ke cewa ɗan bindigar daji Dogo Giɗe ya sanyawa wasu garuruwa 23 a ƙaramar hukumar Tsafe duk cikin jihar ta Zamfara harajin naira miliyan 100 bisa sharaɗin kai musu hari matuƙar suka gaza haɗa adadin kuɗin da ya nema. Sai dai kuma a zantawar da sashen Hausa na RFI ya yi…
Read More
Manyan muƙarraban Tinubu sun fi na Buhari haɗari – Solomon Dalung 

Manyan muƙarraban Tinubu sun fi na Buhari haɗari – Solomon Dalung 

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Solomon Dalung, tsohon ministan matasa da wasanni, ya ce muƙarraban da ke kewaye da Shugaba Bola Tinubu sun  fi na tsohon Shugaba Muhammadu Buhari haɗari, wayewa, da burin cimma manufofi. Blueprint ta rawaito cewa a yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels a ranar Talata, Dalung, wanda a baya ya bayyana cewa akwai wasu mutane da ke tafiyar da gwamnatin Buhari a ɓoye, ya ce waɗanda ke kusa da Tinubu sun fi haɗari. Ya ƙara da cewa muƙarraban dake kewaye da Buhari ba su da ilimi sosai…
Read More