Labarai

Gwamnatin Katsina ta tallafa wa iyalan waɗanda ‘yan bindiga suka kashe da miliyan N16

Gwamnatin Katsina ta tallafa wa iyalan waɗanda ‘yan bindiga suka kashe da miliyan N16

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina  Gwamnatin jihar Katsina ta tallafa wa iyalan waɗanda yan bindiga suka kashi a wasu ƙauyuka da ke ƙaramar hukumar Charanchi.  Kauyukan sun haɗa da Kartaka, Farfaru da Dangaladima da suke gundumar Raɗɗa. Da yake jawabi bayan ya kammala raba kuɗin mataimaki na musamman kan yaƙi da ta'adanci da kuma kula da yan gudun hijira Alhaji Sa'idu Ibrahim ɗanja Kogunan Jibiya ya jajenta wa iyalan da suka rasa nasu. Ya ce wannan tallafi ba wai diyya ce ga waɗanda suka rasa rayukansu ba, "Gwamna Raɗɗa ya fito da wannan tsari na tallafawa iyalan waɗanda suka rasa…
Read More
An ƙaddamar da makaranta da masallaci na waƙafi na Marigayi Aminu Maifamfo

An ƙaddamar da makaranta da masallaci na waƙafi na Marigayi Aminu Maifamfo

Daga IBRAHIM MUHAMAD a Kano Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo ya jagoranci ƙaddamar da buɗe makaranta da masallaci ta gidauniyar waƙafi ta da khumusi ta Marigayi Aminu Umar Mai famfo da ɗan sa mataimakin manajan daraktan Hukumar KASCO, Hon. Aminu Aminu ya gyara aka ƙaddamar a Unguwar Kawaji. Mataimakin Gwamnan Kwamred Aminu Gwarzo ya yaba wa iyalan Marigayin bisa cika wannan buri na mahaifinsu na samar da makarantar da masallaci ya bayyana Marigayi Aminu Umar Maifamfo da dattijon arziƙi da ya bada gudunmuwa a rayuwarsa wajen tallafawa al'umma kuma Allah ya albarkaci bayansa cikin zuri'arsa aka samu…
Read More
Kasafin 2025: INEC ta nemi a ba ta biliyan N126 madadin N40bn da aka ware ma ta

Kasafin 2025: INEC ta nemi a ba ta biliyan N126 madadin N40bn da aka ware ma ta

Daga BELLO A. BABAJI Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC, ta ƙi amincewa da Naira biliyan 40 da Gwamnatin Tarayya ta ware mata daga Kasafin shekarar 2025 inda ta nemi majalisa da ta amince a ba ta biliyan N126 ta hannun kwamitin INEC da harkokin zaɓe. A ranar Juma'a ne Shugaban hukumar, Farfesa Mahmud Yakubu ya gabatar da buƙatar hakan ga kwamitin a lokacin da ya ke kare kasafin. Farfesan ya bayyana cewa harkokin zaɓe yanzu a Nijeriya sun ƙara nauyi wajen gudanar da su, ya na mai cewa a saboda haka ne suke buƙatar isassun kuɗaɗe. Ya ce aƙalla su…
Read More
An kama ɗan sanda bisa laifin wulaƙanta Naira

An kama ɗan sanda bisa laifin wulaƙanta Naira

Daga BELLO A. BABAJI Bayan karaɗe kafafen sadarwa da wani bidiyo da ke nuna yadda wani jami'in ƴan sanda yake wulaƙanta takardun Naira, rundunar hukumar ta sanar da kama shi. Faifan bidiyon ya nuna yadda jami'in, wanda mataimaki ne na wani ɗan kasuwa mai suna Cif Okoya ya ci mutuncin Naira wanda hakan ya haifar cecekuce acikin al'umma. A wani rubutu da hukumomin ƴan sanda suka wallafa ta kafar Facebook, sun ce an gano jami'in da ya aikata laifin a lokacin da ƴaƴan ɗan kasuwar suka yaɗa bidiyon da ke nuna yadda lamarin ya faru inda a yanzu haka ya…
Read More
Rikicin Masarautar Kano: Ba a yi wa Bayero adalci ba, cewar Kotun Ɗaukaka Ƙara

Rikicin Masarautar Kano: Ba a yi wa Bayero adalci ba, cewar Kotun Ɗaukaka Ƙara

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI a Abuja Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke zamanta a Abuja ta yanke hukuncin cewa, Babbar Kotun Jihar Kano ba ta yi wa Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, adalci ba a shari’ar da ya ke gudanarwa tsakaninsa da Gwamnatin Jihar Kano kan tuɓe shi da gwamnatin ta yi ba. A yayin da ya ke yanke hukuncin ranar Alhamis, Alƙali Mohammed Mustapha, wanda ya jagoranci sauran alƙalan kotun uku, ya bai wa Alƙalin Alƙalan Jihar Kano umarnin ya naɗa sabon alƙali, don sake gudanar da shari’ar, wacce tun farko ta wakana a ƙarƙashin Alƙali Amina…
Read More
Rikicin Masarautar Kano: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bai wa Sanusi nasara kan Bayero

Rikicin Masarautar Kano: Kotun Ɗaukaka Ƙara ta bai wa Sanusi nasara kan Bayero

Daga USMAN KAROFI A ranar Juma’a, Kotun ɗaukaka Ƙara dake Abuja ta yi watsi da hukuncin babbar Kotun tarayya reshen Kano da ya shafi naɗin sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II. A cikin ƙarar da gwamnatin jihar Kano ta ɗaukaka kan batun sarauta, Kotun ɗaukaka Ƙara ta soke hukuncin kotun ƙasa wanda ya tambayi sahihancin naɗin Sanusi. Shugaban kwamitin alƙalai uku, mai Shari’a Mohammed Mustapha, ya bayyana cewa babbar Kotun tarayya ta yi kuskuren shiga hurumin da ba nata ba wajen yanke hukuncin kan batun da ya shafi sarauta. Tun farko, mai shari’a Abdullahi Liman na babbar kotun tarayya…
Read More
Azuta Mbata ya zama shugaban ƙungiyar ƴan ƙabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo

Azuta Mbata ya zama shugaban ƙungiyar ƴan ƙabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo

Daga BELLO A. BABAJI An zaɓi Sanata John Azuta-Mbata a matsayin shugaban ƴan ƙabilar Igbo na Duniya baki ɗaya. Azuta-Mbata shi ne tsohon Sanatan Ribas ta Gabas a Majalisar Tarayya, wanda aka zaɓe shi a tsohon masaukin gwamnatin jihar Enugu dake Enugu, babban birnin jihar bayan ganawa da masu-ruwa-da-tsaki. Taron ya samu halarcin wakilai daga Kudu maso Gabas inda aka samu kimanin wakilan ƙungiyoyi 200. Mbata zai gaji Ozichukwu Chukwu a muƙamin wanda ɗan jihar Imo ne. An haifi Mbata ne a Junairun shekarar 1960 inda ya yi karatun digirinsa na biyu a Jami'ar Ibadan. Ya kuma taɓa zama Sanata…
Read More
Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da wani masallaci a Katsina

Gwamna Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da wani masallaci a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na Jihar Katsina ya buƙaci masu hannu da shuni da su gina masallatai da makarantun Islamiyya waɗanda za su taimaka wajen tarbiyyartar da al’umma. Ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake ƙaddamar da wani sabon masallacin Juma’a a ƙaramar hukumar Sandamu, wanda wani jami'in "yan sanda, AIG Mustafa Bala Sandamu, ya gina. Gwamna Raɗɗa ya ce gina masallatai da makarantun islamiyya zai taimaka matuƙa wajen koyar da ilimi da kyawawan halaye wanda zai sa al'umma ta inganta. Ya umurci kwamitin masallacin da al’ummar garin Sandamu da su riƙa ba…
Read More
Shettima ya maƙala wa ƴan sandan tawagarsa lambobin ƙarin girma

Shettima ya maƙala wa ƴan sandan tawagarsa lambobin ƙarin girma

Daga USMAN KAROFI Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, a ranar Juma’a ya yi bikin ɗora sabbin muƙaman da aka ba wasu jami’an ‘yan sanda biyar daga tawagarsa ta tsaro, bayan samun ƙarin girma daga hukumar kula da aikin ‘yan sanda (PSC). Waɗanda aka ƙarawa girman sun haɗa da Idowu Olatunji, wanda aka daga zuwa Chief Superintendent of Police (CSP), Adamu Barma zuwa Superintendent of Police (SP), da kuma Rufai Mohammed Bello, Usman Abubakar, da Yanas Zidon, da aka ɗaga su zuwa Deputy Superintendent of Police (DSP). A yayin taron bikin ɗaurin muƙamin da aka gudanar a fadar shugaban ƙasa, mataimakin…
Read More
‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaron CWC da ƴan sa kai 21 a Katsina

‘Yan bindiga sun kashe jami’an tsaron CWC da ƴan sa kai 21 a Katsina

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Jami'in yaɗa labarai na rundunar ƴan sanda a Katsina DSP Abubakar Sadiq Aliyu ya tabbatar da afkuwar lamarin. Ya bayyana cewa su waɗannan jami'an tsaro sun rasa rayukansu a ƙauyen Ɓaure da ke ƙaramar hukumar Batsari bayan sun je ta'aziyar mutuwar wasu mutane. Da dama sun sami raunuka daga hare haren ƴan bindiga a ƙauyen da harin ya faru. DSP Abubakar Sadiq ya ce yanzu haka jami'an 'yan sanda sun shiga ƙauyen Bature da sauran ƙauyukan domin zaƙulo ƴan ta'addan da suka aikata wannan ɓarna Babu dai wani ƙarin bayani dangane da halin da ake…
Read More