Labarai

Ruwa ya fi man fetur amfani wajen bunƙasa noma – Auwalu Ya’u

Ruwa ya fi man fetur amfani wajen bunƙasa noma – Auwalu Ya’u

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Daya daga cikin matasa, manoma kuma ɗan kasuwa mai kamfanin sayar da injinan noma da ke Kano, Alhaji Auwalu Yau Kura, ya bayyana cewa idan aka yi amfani da dama-damai da madatsun ruwan da mu ke da su a Nijeriya wajen bunƙasa noman rani da na damina, to babu shakka za mu gane cewa arziƙi da za a samu a dalilin ruwa ya fi na man fetur amfani, musamman ma a  Kano da su ke da dama-damai, da aka samar da su sama da shekara 50 da tsohon Gwamnan Kano Alhaji Audu Bako ya samar…
Read More
Gwamnan Jihar Ribas ya gabatar da kasafin kuɗin 2025 ga ‘yan majalisa biyar

Gwamnan Jihar Ribas ya gabatar da kasafin kuɗin 2025 ga ‘yan majalisa biyar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Ribas Siminalayi Fubara ya gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2025 na naira triliyan ɗaya da biliyan ɗari takwas a gaban 'yan majalisu guda biyar domin dubawa da kuma amincewa. Fubara ya ce za a aiwatar da kasafin kudin shekara mai zuwa domin tabbatar da samun cigaba a tattalin arziki mai ɗorewa, da kawo cigaba ga jihar, a lokaci guda kuma zai inganta rayuwar 'yan jihar. Gwamnan ya ce an ware sama da biliyan 30 a fannin noma, yayin da ya ce an ware naira biliyan 63 a fannin samar da ilimi, sai…
Read More
Da gudunmawar Muhammad Garba na zama Shugaban NUJ na ƙasa – Kwamared Alhassan Yahaya

Da gudunmawar Muhammad Garba na zama Shugaban NUJ na ƙasa – Kwamared Alhassan Yahaya

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Shugaban ƙungiyar 'Yan Jaridu na ƙasa, Kwamared Alhassan Yahaya, ya bayyana cewa da gudunmawar Malam Muhammad Garba, tsohon Kwamishinan Yaɗa Labarai na Jihar Kano kuma tsohon Shugaban ƙungiyar 'Yan Jaridu na ƙasa, NUJ kuma tsohon shugaban ƙungiyar 'yan jaridu na Afrika WAJA yanzu kuma shugaban ma'aikata na shugaban jam'iyyar APC na ƙasa Malam Muhammad Garba da gudummawarsa ne, da kuma goyan bayansa, da shawarwarin ne ta sa ya zama shugaban wannan ƙungiya na farko wanda ya fito daga Arewa maso Gabas, kuma ɗan Arewa wanda ya samu wannan muƙami bayan shekaru tara da saukar ɗan…
Read More
Nan ba da jimawa ba za mu tuntuɓi Kwankwaso – PDP

Nan ba da jimawa ba za mu tuntuɓi Kwankwaso – PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar jam'iyyar hamayya a Nijeriya, PDP ta ce nan ba da jimawa ba za su tuntuɓi tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa kwankwaso, domin ya sake komawa jam'iyyar a yi tafiya tare domin ganin bayan jam'iyyar APC mai mulki a ƙasar. Muƙaddashin shugaban jam'iyyar, Ambasada Umar Iliya Damagun ne ya bayyana haka a hirarsa da BBC, yayin da yake mayar da martani kan kalaman da Kwankwason ya yi na cewa jam'iyyar, PDP ta mutu, kuma ba za ta iya wata nasara ba a nan gaba. Ya jaddada cewa a yanzu haka a shirye…
Read More
Muna da masaniya kan jajircewar Hon. Doguwa wajen aiki – Injiniya Abdulrazak

Muna da masaniya kan jajircewar Hon. Doguwa wajen aiki – Injiniya Abdulrazak

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Babban sakataren ma'aikatar albarkatun ruwa ta Jihar Kano, Injiniya Abdulrazak Haruna, ya bayyana cewa suna da cikakkiyar masaniya da labarin cewa sabon kwamishinan albarkatun ruwa na Jihar Kano Hon. Haruna Umar Doguwa, jajirtacce ne wajen aiki da bauta wa al'umma, da kuma biyayya da dokokin aiki na gwamnatin Kano ƙarƙashin shugabancin Alhaji Kabir Yusuf. Ya ce wannan dalili ya sa suke farin ciki da zuwan shi wannan ma'aikata, kuma ɗaukacin ma'aikatan wannan ma'aikata za su bashi goyan baya ɗari bisa ɗari, domin ciyar da ma'aikatar da Kano baki ɗaya, kamar dai yadda babban Sakataran Injiniya…
Read More
Fadar Shugaban ƙasa ta buƙaci Bala ya janye barazanar da ya yi wa Tinubu

Fadar Shugaban ƙasa ta buƙaci Bala ya janye barazanar da ya yi wa Tinubu

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Fadar Shugaban ƙasa ta buƙaci gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya janye barazanar da ya yi wa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan batun sake fasalin haraji. Wata sanarwa a ranar Litinin mai taken; martani a kan 'Za mu nuna wa Tinubu Launinmu na Gaskiya' da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da sadarwar jama'a, Sunday Dare ya raba a kan hannun ɗ, ya bayyana barazanar Mohammed a matsayin "mai tayar da hankali.” Hakan ya biyo bayan sanarwar da gwamnan ya fitar ya ce shugaba Tinubu yana kira ne da a kawo rashin…
Read More
Dalilan da suka sa mu ka shirya tsarin ajiye aiki da wuri – Cardoso

Dalilan da suka sa mu ka shirya tsarin ajiye aiki da wuri – Cardoso

Babban bankin Nijeriya (CBN) ya sake bayyana cewa ma’aikata 1,000 da suka bar aiki a watan Disamba na shekarar 2024 ba a tilasta musu ba, sai dai sun fita ne ta hanyar wani shirin ajiye aiki ba tilas (Early Exit Programme).Gwamnan babban bankin, Olayemi Cardoso, ya bayyana hakan a ranar Juma’a a Abuja yayin zaman jin ba’asi da kwamitin musamman na Majalisar Wakilai yake yi kan batun. Wakilin Gwamnan, Bala Bello, wanda shi ne darakta mai kula da sashen ayyuka na bankin, ya ce shirin ajiye aiki ba tilas da gyara tsarin aiki da sake fasalin bankin suna da nufin…
Read More
Rashin wuta zai sami wasu yankunan Abuja tsawon sati biyu

Rashin wuta zai sami wasu yankunan Abuja tsawon sati biyu

Wasu mazauna birnin tarayya (FCT) za su fuskanci dogon lokacin katsewar wutar lantarki daga ranar Litinin, 6 ga Janairu, 2025. Wannan na zuwa ne bayan sanarwar da Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) ya fitar, inda ya bayyana cewa za a sami katsewar wuta a sassa daban-daban na babban birnin saboda aikin gyara da sauya layukan wutar lantarki. Kamfanin ya bayyana cewa katsewar wutar ta taso ne sakamakon sauya wuraren 33KV DC Airport Feeder da 132KV Kukwaba-Apo Transmission Line Towers da ke Southern Expressway. A cikin sanarwar da kamfanin ya wallafa a shafinsa na X ranar Juma’a, ya ce…
Read More
Amarya ta sanya guba a abincin ango wajen bikinsu, mutum ɗaya ya mutu, an kai ango asibiti

Amarya ta sanya guba a abincin ango wajen bikinsu, mutum ɗaya ya mutu, an kai ango asibiti

Daga USMAN KAROFI Wani bikin aure a Jihar Jigawa ya rikiɗe zuwa tashin hankali bayan da ake zargin amarya ta sanya guba a cikin abincin da aka bayar a wajen liyafar bikin. Wannan lamari ya jawo mutuwar ɗaya daga cikin baƙin da suka halarci bikin, yayin da angon ya shiga mawuyacin hali a asibiti. Lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Jahun ta jihar. Ganau sun bayyana cewa abin da amaryar ta aikata na iya zama sakamakon wata bita-da-ƙulli da ke tsakaninta da wani. Da yake magana da 'yan jarida a ranar Jumma’a, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan…
Read More
Fintiri ya naɗa sabbin sarakuna guda bakwai a Adamawa

Fintiri ya naɗa sabbin sarakuna guda bakwai a Adamawa

Daga USMAN KAROFI Gwamnan Jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, ya amince da naɗin sabbin Sarakuna guda bakwai ga sabbin masarautu da aka ƙirƙirar a jihar. Sanarwar ta fara aiki nan take kamar yadda gwamnan ya bayyana. Sunayen sabbin Sarakunan gargajiya da wuraren da suke mulka sun fito ne ta wata sanarwa da Kakakin yaɗa labarai na gwamnan, Humwashi Wonisikou, ya fitar, ya kuma miƙawa 'yan jarida a ranar Jumma’a. Gwamna Fintiri, wanda ya taya sabbin sarakunan murna, ya bayyana cewa naɗinsu ya dogara ne akan cancanta da karɓuwarsu a wajen jama’arsu. Ya kuma yi kira gare su da su zama…
Read More