Labarai

Zargin badaƙala: El-Rufa’i ya ziyarci tsohon shugaban ma’aikatan gidan gwamnatinsa a kurkuku

Daga BELLO A. BABAJI Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufa'i ya ziyarci Kurkukun Kaduna don ganin tsohon shugaban ma'aikatan gidan gwamnatinsa, Bashir Sa'idu da aka tsare. A ranar Litinin ne aka kama shi tare da kai shi wata kotun shari'a dake Rigassa wadda ta umarci a tsare shi a gidan yarin bisa zargin sa da hannu a badaƙalar wasu kuɗaɗe da ma wasu tuhume-tuhume. Rahotanni sun ce El-Rufa'i ya je gidan yarin ne tare da wasu tsofaffin kwamishinoninsa da suka haɗa da; Kwamishinan Ilimi, Jafaru Sani; Kwamishinar Ci-gaban Al'umma, Hafsat Baba; da kuma Ibrahim Hussaini wanda shi ne tsohon…
Read More

‘Yan sanda sun gano makamai masu linzami uku, sun hana fashewar bom a Borno

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an ƴan sanda a Borno sun gano wasu makamai masu linzami guda uku da kuma dakatar da fashewar bom a jihar. Kakakin ƴan sandan, Nahum Daso ya ce an gano makaman ne a yankin Dala Kafanti na Maiduguri, babban birnin jihar a ranar 2 ga watan Janairu, 2025. A ranar Alhamis ne wata mai suna Asabe James ta ruwaito wa hukumar ƴan sanda cewa ta ga wani buhu dake ɗauke da wasu ababen zargi a bayan gidanta inda rundunar ta aika da jami'an kula da ababan fashewa (EOD) zuwa yankin. Daga nan ne jami'an suka garzaya…
Read More

Kamfanonin waya sun nemi Gwamnatin Tarayya ta amince da ƙarin kaso 100 na farashi

Daga BELLO A. BABAJI Kamfanonin waya na Telecoms sun miƙa takardar buƙatar ƙara farashi ga Gwamnatin Tarayya da kaso 100. An miƙa kundin ne ga Hukumar Sadarwa ta NCC don warware matsalolin tashin farashin gudanarwa da hauhawar farashi da ƙarin adadin kashe-kashe. Shugaban Kamfanin MTN a Nijeriya, Karl Toriola ya faɗi hakan a wata hira da gidan talabijin na Arise a ranar Alhamis, inda ya ce babu tabbas kan cewa ko NCC za ta amince da buƙatar. Ya ce yana da muhimmanci su ƙara farashin kasancewar kamfanonin suna fuskantar matsalolin hauhawar farashin gudanarwa yayin ayyukansu. Ya kuma ce duk da…
Read More

‘Yan Sanda a Katsina sun kuɓutar da mutane 361 daga komar ƴan ta’adda

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina 'Yan sanda a Jihar Katsina sun yi nasarar kuɓutar da mutum 361 daga hannun yan ta'adda a shekarar 2024. Kakakin rundunar, ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya sanar da hakan a lokacin da ya ke wa manema labarai bayanin nasarorin da rundunar ta samu acikin shekarar. Ya ce mutanen tuni aka miƙa su ga iyalan su yayin da suka kashe ƴan bindiga 40 a wurare daban-daban a faɗin jihar. "Mun kuma samu nasarar kama ɓarayin shanu guda 81 da gano shanu da suka sata guda 2081." Har'ilayau, jami'an ƴan sandan sun kama yan fashi da makami…
Read More
Kasafin 2025: Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira biliyan 60 wajen ciyar da ɗalibai

Kasafin 2025: Gwamnatin Tarayya za ta kashe Naira biliyan 60 wajen ciyar da ɗalibai

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta ce ta ware Naira biliyan 60 a kasafin kuɗin 2025 don shirin ciyar da ɗalibai na makarantun firamare, wanda zai kasance ɗaya daga cikin sabbin ayyukan da za a aiwatar ƙarƙashin shirin Farfaɗo da Tattalin Arziki na Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya (ERGP). Tsohon ministan ilimi ya bayyana cewa shirin ciyar da ɗalibai zai koma ƙarƙashin kulawar ma’aikatar, inda aka fara shi tun farko kafin a mayar da shi ƙarƙashin Ofishin Shugaban ƙasa. An ware wa Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya fiye da Naira biliyan 348 daga jimillar fiye da Naira tiriliyan 2.517…
Read More
Saƙon Tinubu na sabuwar shekara soki-burutsu ne – PDP

Saƙon Tinubu na sabuwar shekara soki-burutsu ne – PDP

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar jam'iyyar hamayya a Nijeriya, PDP ta ce jawabin da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi wa al'ummar ƙasar na sabuwar shekara, kalaman baka ne kawai. A jawabin da Tinubun ya yi ranar Laraba 1 ga watan Janairun, 2025, ya bayyana tsare-tsaren da ya ce gwamnatinsa za ta ɓullo da su domin rage tsadar farashin abinci da samar da tsaro da kuma wasu nasarori da ya ce gwamnatinsa ta samu. A dangane da kalaman shugaban ne jam'iyyar PDP ta bakin tsohon sakatarenta na ƙasa Sanata Umaru Tsauri, ta mayar da martani da cewa kalaman…
Read More
Rashin adalci ne babban ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta, inji Akpabio

Rashin adalci ne babban ƙalubalen da Nijeriya ke fuskanta, inji Akpabio

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja  Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana rashin adalci a matsayin babban ƙalubalen da Nijeriya ke fama da ita. Akpabio ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi a Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom a yayin addu’ar nuna farin cikin na ɗaga darajar mai shari’a Festus Ntong, zuwa kotun ɗaukaka ƙara bayan bayan shafe tsawon shekaru yana hidimta wa jihar ta Akwa-Ibom. A cewar sanarwar da mai taimaka wa sanatan na musamman kan yaɗa labarai, Akpabio ya ɗora alhakin matsalar tsaron da Nijeriya ke fama da shi ne kan rashin adalci inda ya ce…
Read More
Da kafafen sada zumunta ana iya gina ƙasa a kuma bunƙasa arziki – Yusha’u Shuaibu

Da kafafen sada zumunta ana iya gina ƙasa a kuma bunƙasa arziki – Yusha’u Shuaibu

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano  Gidauniyar Adnan Mukhtar and Associates ta shirya taron lakca don taya murnar ranar haihuwa ga Shugaban rukunin makarantu MAAUN Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo, da ya cika shekara 47 a duniya a gidan Mumbayya Gwammja, Kano ranar Litinin. A  jawabinsa, ƙwararen masani akan kafofin yaɗa labarai kuma masani akan kafafen sadarwa na zamani, kuma shugaban Kamfanin PRNigeria Alhaji Yusha'u Shuaibu ya bayyana cewa muhimmancin soshiyar midiya wajen gidlna ƙasa, inda ya ce "Mutane da yawa suna soshiyal midiya amma sun fi amfani da ita ne ta hanyar raha wato entertainment abinda muke cewa shi ne za…
Read More
Yadda ‘yan bindiga suka sace fasinjoji, suka ƙone mota a Zamfara

Yadda ‘yan bindiga suka sace fasinjoji, suka ƙone mota a Zamfara

Daga SANI HAMAD GIWA a Abuja ’Yan bindiga sun kai wa wata mota ɗauke da fasinjoji hari a ƙaramar Hukumar Shinkafi da ke Jihar Zamfara, inda suka sace dukkanin fasinjojin motar sannan suka ƙone motar. Lamarin ya faru a garin Kwanar Jalab da ke gundumar Zungeru a safiyar ranar Talata. Wani mazaunin yankin, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya ce, “’Yan bindigar sun tare motar, suka sace fasinjoji goma, sannan suka ƙone motar. “Wannan shi ne karo na farko da suka ƙone mota bayan sun yi garkuwa da mutane. Lamarin ya tayar da hankali sosai.” Wannan hari ya haifar…
Read More
Kamfanin mu sashi ne don tallafawa Jami’ar Isyaka Rabiu da kuɗin shiga – Dakta Naja’atu Bala

Kamfanin mu sashi ne don tallafawa Jami’ar Isyaka Rabiu da kuɗin shiga – Dakta Naja’atu Bala

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano Manajan daraktan tuntuɓa ta Jami'ar Khalifa Isyaka Rabiu dake Kano, wato Khairun Consultancy Limited, Dokta Naja'atu Bala Rabiu ta ce an buɗe kamfanin ne domin saye da sayarwa da ƙirƙirar abinda babu, ko saye da sayarwar kaya ga jami'ar kamar yadda suke a halin yanzu, amma nan gaba za su iya faɗaɗa shi zuwa wajenta a matsayin kamfani. Ta bayyana haka ne da take ƙarin haske ga 'yan jarida, ta ce sannan kuma suna yin ƙananan kwasa-kwasai da bita da bayar da horo ga 'yan kasuwa da ɗalibai da ƙungiyoyin masu sana'o'i da sauran mutane…
Read More