Labarai

Gwamnatin Kano ta yi watsi da dokokin haraji

Gwamnatin Kano ta yi watsi da dokokin haraji

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Jihar Kano, ta bayyana matsayarta kan sabbin dokokin haraji da ake tattaunawa a Majalisar Dokokin Nijeriya. Mataimakin Gwamnan jihar, Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf, ya bayyana wannan matsayi a lokacin bikin sabuwar shekara ta 2025 da aka gudanar a Filin Mahaha da ke ƙofar Naisa. Wannan bayani ya fito ne ta hannun kakakin yaɗa Labaran Gwamnan, Ibrahim Garba Shu’aibu. Gwarzo, ya ce: “Waɗannan dokokin haraji ba su ne mafita ga matsalolin tattalin arziƙinmu ba. “Jihar Kano ba ta yarda da kowace doka da za ta cutar da walwalar…
Read More
Shell: NNPC ya gayyaci Obasanjo a matsayin martani ga kalamansa

Shell: NNPC ya gayyaci Obasanjo a matsayin martani ga kalamansa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Kamfanin man fetur na Nijeriya (NNPC) ya miƙa goron gayyata ga tsohon Shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo, domin zuwa matatar mai ta Fatakwal, saboda tabbatar da matsayinta na gudanar da aiki. Wannan ya biyo bayan hirar da Obasanjo ya yi da gidan talabijin na Channels ne kwanakin baya, inda ya bayar da misali da shawarar kamfanin Shell Petroleum Deɓelopment Company (SPDC) da ke nuna matatar ba za ta yi aiki yadda ya kamata ba. A cewar tsohon shugaban, Shell da aka tuntuɓa, don samun daidaito a matatar, ya bayyana damuwarsa game da cin hanci da…
Read More
Fasto ya bindige matashi bayan buga ‘knockout’ na sabuwar shekara a coci

Fasto ya bindige matashi bayan buga ‘knockout’ na sabuwar shekara a coci

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Wani babban limamin cocin Katolika ya harbe wani matashi har lahira bayan da ya tayar banga ta ‘knockout’ a cocin. Lamarin ya faru ne a yayin taron sabuwar shekara da aka gudanar a ranar 1 ga Janairu, 2025, a Amaimo da ke yankin ƙaramar Hukumar Ikeduru ta Jihar Imo. Shaidu sun yi iƙirarin cewa, matashin yana bikin sabuwar shekara da wasan banga a wajen harabar cocin lokacin da limamin cocin ya tunkare shi. Rikicin ya yi ƙamari, wanda ya kai ga harbe-harbe. A wani saƙon da aka wallafa a shafin Facebook, ‘For The Loɓe Of Anambra,’…
Read More
Babu ƙullin karɓe ƙananan hukumomi daga hannunku – Tinubu ga gwamnoni

Babu ƙullin karɓe ƙananan hukumomi daga hannunku – Tinubu ga gwamnoni

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ɗora wa gwamnonin jihohin ƙasar nan 36 alhakin gudanar da ayyukan raya ƙasa a matakin ƙasa, inda ya ce cin gashin kan harkokin kuɗi da aka bai wa ƙananan hukumomi ba wani yunƙuri ne na kwace mulkin ɓangaren daga hannun gwamnoninnba. Shugaban ya ce, shugabancin gwamnoni a matakin ƙasa shi ne jigon samar da wadataccen abinci, wadatar tattalin arziki da ci gaban ƙasa cikin sauri. Tinubu ya bayyana haka ne a ranar Laraba a lokacin da mambobin ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya (NGF) ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak suka kai masa…
Read More
Duk da takun-saƙa, sojojin Nijeriya da Nijar sun ci gaba da yaƙar Lakurawa

Duk da takun-saƙa, sojojin Nijeriya da Nijar sun ci gaba da yaƙar Lakurawa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hedikwatar Tsaro ta Nijeriya ta jaddada ƙudirinta na gudanar da ayyukan haɗin gwiwa da sintiri tare da sojojin Nijar duk da ƙazafin da shugaban sojojin Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ya yi wa Nijeriya. Wannan dai na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin tarayya na kawo ƙarshen ayyukan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda kamar Lakurawa a yankin Arewa maso Yamma da sauran ’yan ta'adda a sassan jihohin da ke kan iyaka tsakanin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar. A baya-bayan nan Tchiani ya zargi Nijeriya da kyale Faransa ta yi amfani da yankinta a matsayin matattarar hargitsa ƙasarsa. Ya kuma yi zargin cewa…
Read More
’Yan sandan Kano sun cafke Shamsiyya bisa zargin shahara a satar waya

’Yan sandan Kano sun cafke Shamsiyya bisa zargin shahara a satar waya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Mai magana da yawun Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano, SP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya bayyana kama wata matashiya mai suna Shamsiyya. ’yar shekara 19, wacce ake zargin ta ƙware wajen damfarar mutane da sace wayoyi da kuma kuɗaɗe, bayan shafe shekara ɗaya ana neman ta ruwa a jallo. Tun bayan bayyana kamen nata a ranar Laraba, mutane da dama suke ta tururuwar zuwa babban ofishin 'yan sanda na Jihar Kano, domin ganin an ƙwato masu haƙƙoƙinsu, wanda a halin yanzu an bayyana kimanin wayoyi sama 20 da ta damfari mutane ta hanyoyi daban-daban. Haka…
Read More
Mun kashe Naira biliyan 2.4 don ɗaukar nauyin ɗalibai 41 a ƙasar Masar – Gwamnatin Katsina

Mun kashe Naira biliyan 2.4 don ɗaukar nauyin ɗalibai 41 a ƙasar Masar – Gwamnatin Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Gwamnatin Jihar Katsina ta bayyana cewa ta kashe naira biliyan 2 da miliyan ɗari 200 domin ɗaukar nauyin ɗalibai 41 da ke karatun aikin likita a ƙasar Masar. Shirin yunƙuri ne da gwamnatin jihar ta yi don magance matsalar ƙarancin likitoci a jihar. Mataimakin gwamnan jihar Farouk Lawal Joɓe, ne ya bayyana haka lokacin da ya ke zantawa da manema labarai, inda ya ce kuɗaɗen sun haɗa da kuɗaɗen karatu, wurin kwana, sufuri, da sauran kuɗaɗen da ɗaliban za su kashe a yayin gudanar da karatun na su. Joɓe, ya bayyana irin ƙalubalen da jihar…
Read More
Gwamna Abba ya buƙaci Shugaban Ƙasa ya ƙara samar wa Kano ayyukan cigaba

Gwamna Abba ya buƙaci Shugaban Ƙasa ya ƙara samar wa Kano ayyukan cigaba

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya buƙaci Shugaban ƙasa Ahmad Bola Tinubu da ya ƙara taimaka ma Jihar Kano da hanyoyi da za su kawo ma jihar cigaba. Gwamnan ya bayyana hakane yayin da ya bi ayarin sauran wasu gwamnonin ƙasar nan taya shugaban ƙasar murnar shigowa sabuwar shekarar nan ta 2025 a Jihar Legas. Wannan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da babban daraktan yaɗa labaran shi Sanusi Ahmad Bature ya fitar ga manema labarai. Haka kuma Gwamna Abba kabir yace kawo ayyukan cigaban da gwamnatin tarayya za tayi zai taimaka…
Read More
Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zurmi ya rasu a haɗarin mota

Mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zurmi ya rasu a haɗarin mota

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Allah ya yiwa mataimakin shugaban ƙaramar hukumar Zurmi, Hon. Bala Arzika Kanwa rasuwa, ya rasa ranshi a sakamakon hatsarin mota da ya rutsa da shi yau da safe a kan hanyar Ƙaura Namoda zuwa Zurmi. Haɗarin ya faru ne a sakamakon taho mu gama da wata motar ɗaukar kaya wanda nan take Allah ya karɓi rayuwar Marigayi Hon. Bala Arzika Kanwa. Da yake nuna alhinsa, gwamna Dauda Lawal a shafin sa na sada zumunta (Facebook) ya fara da cewar, Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un, Na samu labari mara daɗi na rasuwar Mataimakin Ƙaramar gukumar…
Read More
Kotu ta tasa ƙeyar Mahdi Shehu zuwa gidan kaso

Kotu ta tasa ƙeyar Mahdi Shehu zuwa gidan kaso

Daga USMAN KAROFI An tsare fitaccen mai sharhi daga Kaduna, Mahadi Shehu, a gidan gyaran hali na Kaduna bayan gurfanar da shi a gaban kotun Majistare (CMC 1) da ke kan titin Ibrahim Taiwo, Kaduna, ranar Talata. Ana tuhumar sa da laifuka guda biyu wanda suka haɗa da, haɗin baki, taimakawa da goyon bayan ayyukan ta’addanci, wanda ya ci karo da sashe na 26 (2)(3) na Dokar Hana Ta’addanci ta 2022, da kuma tada hankalin jama’a, wanda ya saɓa da sashe na 78 na Dokar Penal Code ta jihar Kaduna ta 2017. Alƙalin kotun, Abubakar Lamiɗo, ya bayar da umarnin…
Read More