02
Jan
Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamna Dikko Raɗɗa na Jihar Katsina ya sha alwashin kawo ƙarshen matsalar rashin tsaro da ya addabi wasu sassan jihar a wannan shekarar da aka shiga. A saƙon shi na murnar shiga sabuwar shekara Malam Dikko Raɗɗa ya ce duk da matsalar tsaro ta zama ƙalubale a ƙasar baki ɗaya,a nan Jihar Katsina gwamnati ta ɗauki matakai da dama na kawo ƙarshen matsalar a jihar. Kan haka ne gwamnan ya ce gwamnatin sa a karo na biyu ta ɗauki jami'an tsaro na al'umma (CWC) tare da samar masu da abun hawa da sauran kayan aiki.…
