Labarai

Gwamnatin Katsina ta ɗauki ma’aikatan kula da lafiya 254

Gwamnatin Katsina ta ɗauki ma’aikatan kula da lafiya 254

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina A ƙoƙarin da ta ke na bunƙasa sha'anin kiwon lafiya a jihar, gwamnatin Katsina ta ɗauki ƙarin sabbin ma'aikatan kula da lafiya 254. Mataimakin gwamnan jihar Farouk Lawal Joɓe ya faɗi haka a hira da manema labarai da ya yi a Katsina. Ya bayyana cewa tuni ma aka tura su aiki a manyan asibitoci da ke faɗin jihar domin kula da ɓangaren. A cewar mataimakin gwamnan, ma'aikatan sun haɗa da likitoci, ma'aikatan jinya,anguwan zoma da na fanin gwaje gwaje da masana haɗe haɗen magunguna . Alhaji Farouk Joɓe ya ce nan bada jimawa ba gwamnati…
Read More
Kwananka ya kusa ƙarewa – Hedikwatar Tsaro ga Bello Turji

Kwananka ya kusa ƙarewa – Hedikwatar Tsaro ga Bello Turji

Rundunar sojin Nijeriya ta bayyana cewa shugaban ‘yan ta’adda mai suna Bello Turji, wanda kwanan nan ya yi barazanar kai hari a wasu ƙauyukan jihohin Zamfara da Sakkwato idan aka ƙi sakin ɗan uwansa da wasu da sojoji suka kama a matsayin wanda kwanan shi suka kusa ƙarewa. Wannan furuci ya zo ne yayin da rundunar ta caccaki masu ƙalubalantar luguden bama-baman da aka kai a sansanin ‘yan ta’adda na Lakurawa a ranar Kirsimeti. Babban Janar Edward Buba, daraktan ayyukan hulɗa da jama’a na tsaron Ƙasa, ya ce, “Tun daga watan Janairu zuwa yau, 31 ga Disamba 2024, an kashe…
Read More

Gwamnan Kano ya rattaɓa hannu a kasafin kuɗin 2025

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya rattaɓa hannu kan Kasafin kudinshekarar 2025 dan inganta rayukan Al'ummar Jihar Kano. Gwamna Abba Kabir ya ce wannan kasafin kuɗi zai taimaka matuka wajen cimma Muradun da za su kawo ma jihar Kano cigaba matuka dan samun saukin rayuwa ga musamman Al'umma matasa masu tasowa. Haka kuma Gwamnan yana fatan wannan kasafin kuɗi zai ƙara bunƙasa hanyoyin samun damar bijiro da ayyuka kamar a bunƙasa harkokin Ilimi da Noma. ''Haka kuma muna fatan wannan Kasafin kudi zai taimaka wajen samar da Ayukan yi ga jama'ar Jihar Kano…
Read More
Gwamnatin Australia ta gargaɗi ‘yan ƙasarta kan shigo wa Nijeriya

Gwamnatin Australia ta gargaɗi ‘yan ƙasarta kan shigo wa Nijeriya

Daga USMAN KAROFI Gwamnatin Australia ta fitar da wata sanarwa mai tsauri, tana gargaɗin ‘yan ƙasar su sake tunanin buƙatar yin tafiya zuwa Nijeriya. Ma’aikatar harkokin waje da ciniki ta Australia (DFAT) ce ta bayar da wannan gargaɗin ranar Talata, inda ta bayyana matsalar tsaro mai tayar da hankali da ta haɗa da ta’addanci, garkuwa da mutane, da kuma yiwuwar rikicin farar hula a matsayin dalilan wannan shawara. A cikin sanarwar, gwamnati ta ce: “Ku sake tunanin buƙatar tafiya zuwa Nijeriya gaba ɗaya saboda yanayin tsaro mara tabbas da barazanar ta’addanci, garkuwa da mutane, laifuka masu tsanani, da kuma yiwuwar…
Read More

Zubairu Balannaji ya lashe gasar gajerun labarai ta Gwamnatin Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta Jihar Kano ta ayyana Zubairu Musa Balannaji a matsayin wanda yazo na farko a gasar gajerun labarai ta shekarar 2024 Da ya ke bayyana sakamakon gasar a ɗakin taro na Malam Aminu Kano da ke Mumbayya a Birnin Kano, shugaban kwamitin alƙalan gasar, Malam Ado Ahmad Gidan Dabino, ya bayyana labarin 'Bahaushiyar Al'ada', wanda Marubuci Zubairu Musa Balannaji ya rubuta a matsayin wanda ya yi nasara kuma ya zama na farko cikin labarai 50 da suka fafata a cikin gasar. Kazalika, ya bayyana labarin 'Gadon gida saida Horo' wanda…
Read More
Zubairu Balannaji ya lashe gasar gajerun labarai ta Gwamnatin Jihar Kano

Zubairu Balannaji ya lashe gasar gajerun labarai ta Gwamnatin Jihar Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar tace fina-finai da ɗab'i ta Jihar Kano ta ayyana Zubairu Musa Balannaji a matsayin wanda yazo na farko a gasar gajerun labarai ta shekarar 2024 Da take bayyana sakamakon gasar a ɗakin taro na Malam Aminu Kano dake Mumbayya, Dr. Halima Abdulkadir Dangambo Wanda shugaban kwamitin gasar Malam Ado Ahmad Gidan Dabino ya yi bayani a madadin ta inda ya bayyana labarin 'Bahaushiyar Al'ada' wanda marubuci Zubairu Musa Balannaji ya rubuta a matsayin wanda ya yi nasara Kuma ya zama na farko cikin labarai 50 da suka fafata a cikin gasar. Kazalika, ya bayyana…
Read More

Mun hallaka ƴan bindiga 40 da kama masu aikata manyan laifuka 916 a 2024 – Kwamishinan ƴan sandan Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina Kwamishinan ƴan sandan jihar Katsina, CP Aliyu Musa, ya ce jami'an rundunarsu sun kashe ƴan bindiga 40 acikin shekara guda. Kwamishinan ya kuma bayyana cewar, an kama masu aikata laifuka 916 tare da ceto mutane 319 da aka yi garkuwa da su a cikin lokacin. Kwamishinan ya bayyana haka ne a ranar Litinin a lokacin da ya ke bayyana irin nasarorin da rundunar ta samu shekarar 2024. “Ina so in tabbatar da jajircewar da aka yi na yaƙi da laifuka da rundunarmu ta yi cikin wannnan shekara, jajircewar da muka yi ta haifar da raguwar…
Read More
Ƙaramar hukumar Tarauni ta yi bikin taya daraktoci biyu murnar ritayar aiki a Kano

Ƙaramar hukumar Tarauni ta yi bikin taya daraktoci biyu murnar ritayar aiki a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano Daraktan mulki da Kuɗi na ƙaramar hukumar Tarauni Alhaji Abdulkadir Muhammad Arabu, tare da shugaban sassa na ƙaramar hukumar, Suleiman Umar sun kammala aikinsu a ranar Litinin na tsowon shekaru 35 in da daraktan mulki mai barin gado ya miƙa kujerar daraktan mulki ga ma'ajjin ƙaramar hukumar Tarauni kwamared Bello Hassan Durimin Zungura yayin da Suleiman Umar ya miƙa kujerar sa ta cpo ga shugaban ma'aikata Nazifi Bello. Shima Nazifi Kuma ya miƙa kejarar ta shugaban ma'aikata ga Tijjani Muhammad Lawan sai Kuma ma'ajjin ƙaramar hukumar ya miƙa kujerar sa ga kashiyan ƙaramar hukumar Ahmed…
Read More

Masarautar Fika da ke Potiskum ta yi naɗe-naɗen sarautu

Daga BELLO A. BABAJI Mai martaba Sarkin Fika kuma Shugaban Majalisar Sarakunan gargajiya ta Jihar Yobe, Alhaji Dakta Muhammad Ibn Abali Muhammad (CON, CFR), ya umarci a sanar da ƙarin girma da naɗin wasu daga cikin muƙarrabansa. Mutanen sune; Air Komodo Ibrahim Alƙali (rtd) daga Galadima zuwa Madakin Fika; sai Ali Adamu Fika wanda aka naɗa a matsayin Wazirin Fika; sannan Alhaji Ali Gimba Fika daga Sakataren riƙon ƙwarya zuwa Sakataren Majalisar Masarautar Fika. Wata takarda da Sakataren masarautar, Ali Gimba Fika ya fitar a ranar 30 ga watan Disamba, 2024, ta ce tuni mutanen da aka naɗa suka kama…
Read More
Nijeriya ta samu dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya bayan cire tallafin mai da gyaran haraji

Nijeriya ta samu dala biliyan 1.5 daga Bankin Duniya bayan cire tallafin mai da gyaran haraji

Bankin Duniya ya amince da sakin bashin dala biliyan 1.5 ga Najeriya, bayan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar da wasu sauye-sauyen tattalin arziki, ciki har da cire tallafin man fetur da ƙara wasu haraji. Bashin, wanda ke cikin shirin "Reforms for Economic Stabilisation to Enable Transformation", an fitar da shi cikin ƙanƙanin lokaci, inda aka saki kaso na farko na dala miliyan 750 a watan Yuli, yayin da aka saki kaso na biyu a watan Nuwamba 2024. Duk da haka, matakan sun haifar da ƙaruwar tsadar rayuwa ga ‘yan Najeriya, yayin da farashin man fetur ya ninka sau…
Read More