Labarai

Al’ummar Zamfara na cikin haɗari kan faifan bidiyon Bello Turji – Dakta Shinkafi

Al’ummar Zamfara na cikin haɗari kan faifan bidiyon Bello Turji – Dakta Shinkafi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jigo a Jam'iyyar APC a Jihar Zamfara, Dakta Sani Abdullahi Shinkafi ya bayyana faifan bidiyo na baya-bayan nan da fitaccen ‘ɗan ta'addan nan Bello Turji ya fitar na mayar da garuruwa da ƙauyuka Kango a jihohin Sokoto da Zamfara a matsayin wani lamari mai tsanani dake buƙatar ɗaukar matakin gaggawa daga gwamnatin tarayya domin daƙile aniyar shi. Dakta Shinkafi ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Gusau. Jaridar Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa a ranar Larabar da ta gabata ne, fitaccen ɗan ta'adda Bello Turji ya fitar da wani…
Read More
Jigon APC ya yaba wa sarkin Ondo kan bada sarautar gargajiya ga ɗan Majalisar Wakilan Zamfara

Jigon APC ya yaba wa sarkin Ondo kan bada sarautar gargajiya ga ɗan Majalisar Wakilan Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Jigo a jam’iyyar APC ta Jihar Zamfara kuma tsohon mai baiwa gwamnan Jihar Zamfara shawara kan harkokin kasuwanci da gudanar da kasuwanci Suleiman Usman Zumunchi, ya yabawa mai martaba Sarkin Jihar Ondo, Oba Akadri Saliu Momoh kan bada sarautar gargajiya ga Ɗan Majalisar Wakilai Abdulmalik Zubairu, a matsayin "Cif Mayegun of Ikare-Akoko Kingdom" Zumunchi ya bayyana haka ga manema labarai a Gusau a ranar Litinin. Ya bayyana ɗan majalisar tarayya a matsayin shugaba marar gajiyawa kuma wanda ya sadaukar da kansa wajen sanya farin ciki ba kawai ga al’ummarsa ba har ma da ɗaukacin al’ummar…
Read More

Tinubu ya amince da gina jami’ar tarayya a Kudancin Kaduna

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Tinubu ya amince da buƙatar samar da jami'ar tarayya a Kudancin Jihar Kaduna, kamar yadda Mataimakinsa, Kashim Shettima ya faɗa. Shettima ya bayyana hakan a lokacin da ya je gaisuwar ta'aziyyar rasuwar Agwom Akulu na Masarautar Ikulu wanda kuma ɗan uwa ne ga Bishop Matthew Hassan Kuka. Ya kuma ce ana tattaunawa game da samar da asibitin tarayya (Federal Medical Center) a Kafanchan dake Kudancin jihar. Ya jaddada ƙoƙarin gwamnatin Shugaba Tinubu na samar da ci-gaba ga yankin, yana mai bada misali da naɗa Janar Christopher Musa a matsayin Babban Hafsan Tsaron Nijeriya la'akari…
Read More

Da Ɗumi-Ɗumi: Matatar Warri ta fara aiki

Daga BELLO A. BABAJI Kamfanin tace dangogin mai na Warri (WRPC) dake Jihar Delta ya fara aiki. Shugaban Kamfanin Man fetur na Ƙasa (NNPCL), Mele Kyari ya bayyana hakan a yau Litinin, a lokacin da ya kai ziyarar gani da ido a matatar. Ya ce duk da cewa ba a kai ga kammala aikin 100 bisa 100 ba, amma an fara ayyukan tace mai. Ya kuma tabbatar wa masu kokwanto game da aikin matatar kan cewa tabbasa abu ne mai yiwuwa ba kamar yadda su ke ɗauka ba na rashin yiwuwar sa. Hakan na zuwa ne makonni kaɗan bayan matatar…
Read More
NAFDAC ta rufe manyan kantuna takwas kan saida kayan jabu a Abuja

NAFDAC ta rufe manyan kantuna takwas kan saida kayan jabu a Abuja

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Nijeriya, NAFDAC, ta kama sama da buhunan shinkafa 1,600 da aka kiyasta kuɗinsu ya kai kimanin Naira Biliyan 5 a ƙaramar Hukumar Karu da ke Jihar Nasarawa, da kasuwannin Wuse da Garki da ke Abuja. Shugaban rundunar wanda kuma shi ne Darakta mai kula da babban birnin tarayya Abuja, Kenneth Azikiwe, ya shaida wa manema labarai cewa hukumar ba za a ɗaga wa kayayyakin jabun ƙafa ba, haka kuma ta rufe shaguna 8 da rumbun ajiya guda ɗaya a Karu saboda samarwa da sayar da jabun shinkafa ga…
Read More
Turmutsutsu: ’Yan sanda sun gargaɗi masu rabon abinci babu cikakken tsari

Turmutsutsu: ’Yan sanda sun gargaɗi masu rabon abinci babu cikakken tsari

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Sufeto Janar na 'Yan Sandan Nijeriya, IGP Kayode Egbetokun, ya yi gargaɗi kan raba kayan agaji ga jama’a ba tare da saamr da shirin na musamman ba a ƙasar. A wata sanarwa da ya fitar ranar Asabar, Egbetokun ya gargaɗi masu shirya rabon tallafi cewa sakaci a ɓangarensu laifi ne. IGP ɗin ya ce, “rashin ingantaccen tsari” na raba kayan tallafi ga jama’a a wasu yankuna a ƙasar ya haifar da ruɗani da turmutsutsu da bai zama dole ba. A cikin sanarwar da ya fitar ta hannun jami'in hulɗa da jama'a na 'yan sandan Nijeriya, Muyiwa…
Read More
Kotu ta umurci MTN ya biya kwastoma miliyan N15 kan cire kuɗi ba bisa ƙa’ida ba

Kotu ta umurci MTN ya biya kwastoma miliyan N15 kan cire kuɗi ba bisa ƙa’ida ba

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja ta umurci babban kamfanin sadarwa na MTN a Nijeriya da ya biya diyyar miliyan N15m bisa cire kuɗi daga asusun wani abokin kwastoma ba tare da izininsa ba. Hakan ya biyo bayan shigar da ƙorafi da wani kwastoma, Ezugwu Anene ya yi inda ya ce an cire masa kuɗi kan sabis ɗin da bai yi rijista ba. Wannan hukuncin ya fito ne daga kwamitin alƙalan kotun ɗaukaka ƙara mai mambobi uku, wanda Mai shari’a Okon Abang ya jagoranta. Mai Shari'a, Abang ya karanto karar a ranar Juma’a 20 ga watan…
Read More
Turmutsutsun rabon tallafi: PDP ta buƙaci Tinubu ya sake duba manufofinsa na tattalin arziki

Turmutsutsun rabon tallafi: PDP ta buƙaci Tinubu ya sake duba manufofinsa na tattalin arziki

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Jam'iyyar PDP ta ce, turmutsutsun da aka samu a Nijeriya guda uku cikin ƙanƙanin lokaci ya nuna cewa akwai talauci da yunwa a ƙasar, wanda a cewarta yana da nasaba da irin mulkin Shugaban ƙasa Bola Tinubu. Kakakin PDP na ƙasa, Debo Ologunagba ne ya sanar da hakan a wata sanarwa, inda ya ce turmutsutsun da ake samu wajen rabon abinci abu ne da za a iya kiyaye afkuwarsu. "PDP na baƙin ciki yadda gwamnatin APC te ɗaiɗaita tattalin arzikin ƙasar nan tare da jefa miliyoyin mutane cikin ƙangin talauci da yunwa, inda mutane da dama…
Read More
An kama wasu bokaye bisa zargin asirce shugaban ƙasar Zambiya

An kama wasu bokaye bisa zargin asirce shugaban ƙasar Zambiya

Hukumomin ƙasar Zambiya sun kama wasu mutune biyu, waɗanda ake zargin su ''matsafa'' ne da aka bai wa aikin asirce shugaban ƙasar, Mista Hakainde Hichilema. ’Yan sanda sun ce sun kama Jasten Mabulesse Candunde da Leonard Phiri a Lusaka, babban birnin ƙasar. "Aikin da suka ƙudiri aniyar yi shine amfani da layu wajen cutar da shugaba Hakainde Hichilema,” kamar yadda sanarwar 'yan sandan ta bayyana. Mutane da dama a ƙasar da ke kudancin Afirka sun yi amanna da bokaye, inda a lokuta da dama mutane kan rayu da fargabar tsoron asiri. 'Yan sanda sun yi zargin cewa Nelson Banda -…
Read More
Ya kashe abokinsa bayan karɓar kuɗin fansa

Ya kashe abokinsa bayan karɓar kuɗin fansa

Kwamishinan ’yan sanda a jihar Delta da ke Nijeriya, Olufemi Abaniwonda ya ce jami'an rundunar suk kama wasu mutane huɗu da ake zargin su da kashe wani mutum. Cikin waɗanda aka kaman har da asalin wanda ya kitsa kisan bayan ya damfari mutumin kuɗi naira miliyan 30 tare da karɓan kuɗin fansa naira miliyan 20 daga iyalin marigayin. Kwamishinan ’yan sandan ya ce a ranar 8 ga watan Oktoban 2024 ne aka sanar da rundunar ’yan sanda game da ɓatan marigayin mai suna Paulinus Okon, mai shekara 30 a duniya bayan ya bayyana wa iyalinsa cewa zai kai wa abokin…
Read More