Labarai

Sakkwato: Babu hujjar kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba – Atiku

Sakkwato: Babu hujjar kashe mutanen da ba su ji ba su gani ba – Atiku

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Tsohon ɗantakarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya ce babu wata hujjar da za a bayar kan kashe mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba. Atiku ya bayyana haka a saƙonsa na jaje game da ibtila'in da ya auku a jihar Sakkwato, inda hare-haren sojoji 'bisa kuskure' ya yi ajalin aƙalla mutum 10, ya jikkata wasu. Atiku ya ce yadda kuskuren ke maimiatuwa ya sa ake tambayar wane darasi aka ɗauka a baya. A cewarsa, "A ranar 3 ga Disamban 2023, gomman mutanen da ba su ji ba,…
Read More
Ana garkuwa da mata da yara a haramtattun matatun mai – Gwamnan Bayelsa

Ana garkuwa da mata da yara a haramtattun matatun mai – Gwamnan Bayelsa

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Gwamnan Jihar Bayelsa, Sanata Douye Diri, a ranar Talata ya bayyana damuwarsa kan wani sabon salon hada-hadar man fetur, inda ya ce ana amfani da yara da mata a matsayin garkuwar mutane a haramtattun matatun mai. Gwamnan Bayelsa ya bayyana haka ne a wata ganawa da ya yi da sarakunan gargajiya da shugabannin ƙananan hukumomin jihar a gidan gwamnati da ke Yenagoa. Ya ce, jami’an tsaro ne suka gano wannan mummunan lamari kan ayyukan leƙen asiri, ya kuma yi kira ga sarakunan gargajiya da su wayar da kan al’ummarsu illar harƙallar ba ta dace ba ga…
Read More
Yadda ’yan bindiga suka shigo da motocin yaƙi Zamfara daga Libya

Yadda ’yan bindiga suka shigo da motocin yaƙi Zamfara daga Libya

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD A ranar Litinin ne Gwamnatin Tarayya za ta gurfanar da wasu mutane biyar da ake zargi da alaƙa da fitaccen sarkin ta’addanci, Bello Turji, a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja. A cikin tuhume-tuhumen, mai lamba FHC/ABJ/CR/633/2024 da aka shigar a gaban mai shari’a Emeka Nwite, gwamnatin tarayya ta yi zargin cewa, waɗanda ake zargin sun shigo da wata motar yaƙi da kuɗinta ya kai Naira Miliyan 28.5 daga ƙasar Libya. Waɗanda ake zargin da hukumomin tsaron Nijeriya suka kama, za a gurfanar da su a ofishin babban lauyan gwamnatin tarayya a gaban mai shari’a…
Read More
Gwamna Abba ya ziyarci Jihar Jigawa karo na biyu don gudanar da ta’aziyya

Gwamna Abba ya ziyarci Jihar Jigawa karo na biyu don gudanar da ta’aziyya

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya Kai ziyarar ta'aziyya ga gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Umar Namadi bisa rasuwar mahaifiyar shi Hajiya Maryam Namadi da kuma babban ɗansa Abdulwahab Umar Namadi wanda su ka rigamu gidan gaskiya a 'yan kwanakin nan. Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana rasuwarsu da cewa rashi ne mai kaɗa zuciya ba ga al'umar Jihar Jigawa ba har ma da yankin Arewacin ƙasar nan. Ya yi addu'ar Allah ya ji ƙansu ya sa jannatul firdausi ce makoma a garesu. A nasa ɓangaren, Gwamna Umar Namadi ya godewa gwamna Abba Kabir…
Read More

Shugaban Amurka na 39, Jimmy Carter ya rasu

Daga BELLO A BABAJI Tsohon Shugaban Amurka, Jimmy Carter, wanda ya shahara da ayyukan jin-ƙai ya rasu bayan shafe shekaru 100 a duniya. Marigayin ya rasu ne a ranar Lahadi, a jihar Georgia bayan fama da wani rashin lafiya na tsawon lokaci. Gabannin mutuwarsa, Charter ya ƙudirin aniyar kaɗa wa ƴar takarar shugaban ƙasa a zaɓen 2024 Kamala Harris ƙuri'a. Carter ya shugabanci Amurka ne daga shekarar 1977 zuwa 1981 inda ya rasa damar komawa zango na biyu bayan ya sha kaye a hannun Ronald Reagan. Ya kuma samu kyautar 'Nobel Prize' a shekarar 2002.
Read More

An tsaurara tsaro akan iyakar Najeriya da Nijar kan ƙishin-ƙishin ɗin harin Lakurawa

Daga BELLO A. BABAJI Jami'an tsaro sun tsaurara matakan kariya akan iyakar Najeriya da Nijar kan samun labarin harin mayaƙan Lakurawa musamman a yankin Sakkwato. Jami'an Hukumar shige da fice (NIS) sun tabbatar wa al'umma cewa kada su ɗaga hankulansu domin sun ɗauki matakan kariya ga shigowa Najeriya ta haramtattun hanyoyi da nufin haddasa fitina. Wani jami'in hukumar ya tabbatar wa manema labarai cewa NIS da haɗin-gwiwar wasu hukumomi suna aiki tare don shawo kan kowacce matsala da za ta gitta ta kan iyakar. Haka kuma hedikwatar hukumar dake Abuja, kamar yadda wata majiya ta nuna, ta tabbatar da cewa…
Read More
Gwamna Dauda ya amince da biyan kyautar albashi na wata ɗaya ga ma’aikatan Zamfara

Gwamna Dauda ya amince da biyan kyautar albashi na wata ɗaya ga ma’aikatan Zamfara

Daga USMAN KAROFI Gwamna Dauda Lawal ya amince da biyan albashin wata 13 ga ma'aikatan Jihar Zamfara Sanarwar ta fito ne daga ofishin Shugaban Ma’aikata na Jihar Zamfara a cikin takardar da aka fitar a ranar 28 ga Disamba 2024. Albashin wata 13 da aka amince da shi zai kasance na biyu a tarihin Jihar Zamfara, inda gwamnatin Lawal ta biya wannan albashi na farko a watan Disamba na shekarar da ta gabata. Ma’aikatan gwamnati, ciki har da masu ritaya, za su samu ƙarin albashi na kashi 30 cikin 100 na albashinsu na asali a matsayin albashin wata 13. Wannan…
Read More
Yadda shugaban ma’aikatan gwamnan Kwara ya gudanar da lokutan ƙarshe na rayuwar shi

Yadda shugaban ma’aikatan gwamnan Kwara ya gudanar da lokutan ƙarshe na rayuwar shi

Daga USMAN KAROFI Rahotanni sun bayyana cewa Marigayi Mahe, yarima kuma ɗan Marigayi Sarkin Ilorin na 10, Mallam Aliyu AbdulKadir, ya rasu yana da shekara 73. Da yake zantawa da wakilinmu a gidan iyalin mamacin, wani makusanci kuma aminin iyali ya ce,“Alhaji Mahe yana cikin ƙoshin lafiya. A ranar Juma’a, 27 ga Disamba, 2024, mun halarci taron bikin aure a gidan babban limamin Ilorin da kuma a gidan iyalan Belgore. “Bayan haka, mun halarci sallar Juma’a a masallacin Ansarud-Deen dake kan titin Taiwo, Ilorin. Daga nan kuma muka je hedkwatar shige da fice don ɗaukar hoto domin sabunta fasfonsa da…
Read More

Sojoji sun kama masinjan harsasan ƴan bindiga a Zamfara

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Dakarun Birget ta ɗaya, tawaga ta 2 a atisayen 'Fansan Yamma', sun kama wata ‘yar shekara 25 mai suna Shamsiyya Ahadu ɗauke da harsashi na musamman samfurin 764mm 7.62mm da kuma kenson harsasai Gida shida (Magazine 6) a yunƙurin ta na kaiwa sansanin ‘yan ta’addan Bello Turji. Kodinetan Joint Media Coordinating Center Operation Fansan Yamma, Laftanar Kanar Abubakar Abdullahi ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi a Gusau, inda ya ce an kama Shamsiyya ne a ranar 28 ga watan Disamba, 2024 tare da abokinta, wani direban babur mai suna…
Read More