Labarai

Tsaro: Kashi 85 na manoman Arewa maso Yamma za su koma gonakinsu a daminar baɗi – Yari

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau Tsohon gwamnan jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari Abubakar, ya yaba wa jami’an tsaro bisa jajircewarsu wajen daƙile ayyukan ƴan ta'adda a yankin Arewa maso Yamma, yana mai cewa, ƙoƙarin da suke yi zai bai wa kaso 85 bisa 100 na manoma damar koma wa gonakinsu a damina mai zuwa. Ya faɗi hakan ne a lokacin da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai a gidansa dake Garin Talata Mafara a ƙaramar hukumar Talata Mafara, a ranar Asabar. A cewarsa, sannu a hankali zaman lafiya yana dawowa sakamakon ba-takashi da sojoji ke yi da ƴan ta’adda…
Read More

Gwamnan Kano ya taya wanda ya lashe gasar musabaƙar Alƙur’ani ta ƙasa murna

Daga RABIU SANUSI a Kano Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya taya Buhari Idris murnar nasarar lashe gasar karatun Al-ƙur'ani mai girma ta ƙasa da ta gudana a ranar Asabar wadda ita ce karo na 39. Gwamna Abba ya miƙa sakon ne ta cikin wata sanarwa da Daraktan yaɗa labaransa Malam Sanusi Bature ya fitar, wanda ya ce Buhari ya samu nasara ne da maki 98.2 kan abokan karawarsa. Gasar, wadda ta gudana a birnin Kebbi, babban birnin jihar kebbi, ta samu halartar manyan malamai da ɗalibai daga ciki da wajen Najeriya. Sanarwar ta ce da yake bayyana…
Read More

Sojoji sun kama wacce ke yi wa Bello Turji safarar alburusai

Daga BELLO A. BABAJI Dakarun tsaro na atisayen 'Fansan Yamma', sun yi nasarar kama wata Shamsiyya Ahadu mai shekaru 25 bisa laifin safarar alburusai. Kakakin dakarun, Laftanal Kanal Abubakar Abdullahi ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a Gusau, babban birnin jihar Zamfara. A ranar 28 ga watan Disamba ne aka kama Shamsiyya tare da mai mashin ɗin da ya ɗakko ta mai suna Ahmed Husaini a yankin Badarawa dake ƙaramar hukumar Shinkafi a jihar. An kama ta ne ɗauke da wasu alburusai guda 764 ƙirar 7.62mm da wasu mujallu shida da nufin kai wa sanannen jagoran ƴan…
Read More

Majalisar Wakilai na neman a raba ofishin Antoni-Janar da na Ministan Shari’a

Daga BELLO A. BABAJI Majalisar Wakilan Nijeriya ta shirya neman tabbatar da ƙudirin da zai buƙaci a raba ofisoshin Antoni-Janar na ƙasa da kuma na ministan shari'a. Haka ma ofisoshin Antoni-Janar na jihohi za a raba su da na kwamishinan shari'a kowacce jiha. Ƴan majalisa Mansur Soro (PDP) da Oluwole daga (PDP) daga jihohin Bauchi da Osun suka ɗauki nauyin gabatar da ƙudirin ƙarƙashin shugaban kwamitin nazarin doka kuma mataimakin Kakakin Majalisar, Benjamin Kalu. Ƙudirin na neman gyara ga sashe na 150 na dokar ƙasa ta 1999 ta hanyar ƙara sakin layi ɗaya da zai bada damar hakan a mataki…
Read More
Ku yi haƙuri – Shettima ya nemi afuwar iyalan waɗanda tsautsayin harin Sokoto ya rutsa da su

Ku yi haƙuri – Shettima ya nemi afuwar iyalan waɗanda tsautsayin harin Sokoto ya rutsa da su

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya bai wa iyalai da suka rasa 'yan uwansu a harin da sojoji suka kai a ƙananan hukumomin Silame da ke Jihar Sokoto hakuri. Harin, wanda ya faru a ranar Larabar 25 ga watan Disamba, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 yayin da sojoji suka kai hari kan sansanin ’yan ta’addan Lakurawa a wasu ƙauyukan yankin. A cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara kan harkokin yaɗa labarai, Stanley Nkwocha, ya fitar, Shettima ya bayyana jimaminsa kan wannan al’amari mai ɗaure kai, inda ya ce wannan wani lokaci ne na baƙin ciki da aka…
Read More
Gwamnan Kebbi ya karrama ɗan Kano, Sanusi Idris, wanda ya yi na ɗaya a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa

Gwamnan Kebbi ya karrama ɗan Kano, Sanusi Idris, wanda ya yi na ɗaya a gasar karatun Alƙur’ani ta ƙasa

Daga USMAN KAROFI Gwamnan Jihar Kebbi, Malam Nasir Idris, ƙauran Gwandu, ya karrama Malam Buhari Sanusi-Idris daga Jihar Kano a matsayin gwarzon shekara a gasar karatun Al-ƙur’ani ta ƙasa karo na 39 da aka gudanar a Birnin Kebbi. Hajiya Zainab Nasare Nasir Idris, matar gwamnan, ta kuma karrama Malama Rumaisa’u Ɗahiru Ibrahim daga Jihar Gombe a matsayin zakaran ɓangaren mata. Duka sun samu kyautar motar hawa, kujerar aikin hajji, Naira 500,000 da kuma talabijin plasma, yayin da Rumaisa’u ta ƙara samun kyautar firji. Wannan gasa, wadda aka shirya domin zaɓen wakilai da za su wakilci Nijeriya a gasar karatun Al-ƙur’ani…
Read More

Shugaba Tchiani na fuskantar suka daga ƴan Nijar bisa zargin Nijeriya da yi wa ƙasar maƙarƙashiya

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban mulkin sojin Jamhuriyar Nijar, Abdurrahman Tchiani na fuskantar suka daga wasu ƴan ƙasar kan zargin Nijeriya da shirya wa Nijar maƙarƙashiya. Daga cikin abin da shugaban ya faɗa a yayin wata hira da shi a ranar Kirsimeti, ya ce Nijeriya ta samar da sansanin sojojin Faransa a yankin tafkin Chadi da sansanonin horar da ƴan ta'adda a jihohin Sakkwato, Zamfara da Kebbi don haddasa tashin-tashina a Nijar. Saidai, Gwamantin Tarayya ta ofishin Mai taimaka wa shugaban ƙasa kan harkar tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribaɗu ta ƙaryata zargin inda ta ce batu ne mara asali dake…
Read More

Shugaban mai’aikatan fadar gwamnatin Kwara, Prince Abdulƙadir Mahe ya rasu

Daga BELLO A. BABAJI Shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin Jihar Kwara, Frins Abdulƙadir Aliyu Mage ya rasu. Marigayin ya rasu ne a asibitin koyarwa na Jami'ar Ilorin a yau Asabar, 28 ga watan Disamba. Kawo yanzu gwamnatin jihar, ƙarƙashin jagorancin Abdurrahman Abdurrazak ba ta ce komai ba game da rashin. A ranar 4 ga watan Nuwamba, 2024 ne aka rantsar da Frins Mahe a matsayin shugaban mai'aikatan wanda da farko shi ne sakataren gwamnatin. Ya kuma taɓa riƙe muƙamin akawon Majalisar Dokokin jihar daga shekarar 2004 zuwa 2007. Sannan ya taɓa zama ɗaya daga cikin jami'an tsohuwar Hukumar Wutar lantarki ta…
Read More

Bikin raya al’adun Kaltungo na ƙara haɗin kai da zaman Lafiya – Mr Meso Dickson

Daga RABIU SANUSI a Gombe An bayyana bikin raya Al'adun gargajiya da ake gudanarwa duk ƙarshen shekara a masarautar Kaltungo dake kuma Karamar hukumar ta Kaltungo a Jihar Gombe a matsayin bikin dake ƙara kawo zaman lafiya da haɗin kai matuƙa a jihar da ma ƙasa baki ɗaya. Shugaban gabatar da taron na bana kuma shugaban rukunin Kamfanonin Mesoto Group, Mista Meso C.Dickson ya bayyana hakan yayin buɗe taron dake gudana na tsawon kwanaki biyu a masarautar. Mista Meso ya bayyana godiyarsa ga Masarautar ƙarƙashin Mai Martaba, Mai Kaltungo Injiniya Saleh Muammad Umar mai tarin albarka tare da daɗaɗɗen Tarihi…
Read More

Bayan shekaru 28, waɗanda aka yi wa allurar Pfizer a Kano sun koka da rashin adalci

Daga BELLO A. BABAJI A shekarar 1996, wani kamfanin magunguna mai suna Pfizer ya fitar wani magani na yara da ake kira da 'Trovan' wanda ya yi sanadiyyar mutuwar yara da dama da kuma nakasa wasu. Bayan shekaru 28, waɗanda suka tsira daga annobar da maganin ya haifar sun koka da mummunan halin da suka tsinci kawunansu. A shekarar ne al'ummar Nijeriya musamman ta Arewa, suka fuskantaci tsananin cutar sanyi da ake kira da 'meningitis'. News Point Nigeria ta ruwaito cewa, wani rahoto da Hukumar Lafiya ta Duniya WTO ta fitar a watan Maris na 1996 ya ce an samu…
Read More