Labarai

Magidanta miliyan 15 za su amfani da N25,000 duk wata – Ministan Jinƙai

Magidanta miliyan 15 za su amfani da N25,000 duk wata – Ministan Jinƙai

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Ministan Jinƙai da Agaji, Nentawe Yilwatda ya ce, Gwamnatin Tarayya na shirin bai wa gidaje 15 da kuma ɗaiɗaikun mutane miliyan 75 tallafin kuɗaɗe. A cewarsa, za a biya kowane magidanci Naira 25,000 duk wata sau uku a shekara. Mista Yilwatda ya ce, matakin wani ɓangare ne na yunƙurin da shugaba Bola Tinubu ke yi na ganin an shawo kan matsalolin da ke tattare da tattalin arziki ga marasa ƙarfi a Nijeriya. "Shugaban wasa ya baiwa shirin fifiko, akwai tsare-tsare da ya kawo don ganin ko hakan zai iya sauƙaƙa wa mutane ƙalubalen rayuwa," inji shi…
Read More
Kwastom za ta ɗauki sabbin ma’aikata 3,927

Kwastom za ta ɗauki sabbin ma’aikata 3,927

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD Hukumar Kwastom ta Nijeriya ta amince da ɗaukar ma’aikata 3,927 tare da ba da ƙarin girma na musamman ga ma’aikatan da suka kware domin magance giɓin ma’aikata da inganta harkokin hukumar. An yanke wannan shawarar ne biyo bayan sake duba ayyukan hukumar ta NCS a shekarar 2024, wanda ya nuna nasarar da hukumar ta samu wajen daƙile fasa-kwauri da bunƙasa kasuwanci mai matuƙar muhimmanci ga ci gaban tattalin arziki da samar da ayyukan yi. Hukumar ta yaba wa Gwamnatin Tarayya bisa gagarumin rawar da take takawa wajen haɓaka farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya, musamman ganin yadda…
Read More
Gwamnan Gombe ya amince da dokar kula da masu buƙata ta musamman

Gwamnan Gombe ya amince da dokar kula da masu buƙata ta musamman

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaha ya sa hannu kan ƙudurin dokar kula da masu buƙata ta musamman, wadda ta ƙunshi kafa hukumar masu buƙata ta musamman. An yi dokar ce domin samar da daidaito da adalci, tare da tsara hanyoyin da za a taimakawa mutane masu buƙata ta musamman a jihar da kuma tabbatar da cewa ana damawa da su. A lokacin bikin sa hannu kan dokar a gidan gwamnatin, Gwamna Inuwa ya sanar da naɗa Ishiyaku Adamu a matsayin shugaban sabuwar hukumar kula da masu buƙata ta musamman da ya kafa. Ya…
Read More
Yadda ɓatagari suka ɗirka wa fadar Etsu na Lokoja nakiya

Yadda ɓatagari suka ɗirka wa fadar Etsu na Lokoja nakiya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Wasu da ake zargi hasalallun matasa ne da ke adawa da masarautar Etsu na Lokoja sun kai wa fadar Sarkin Nupe, Chief Emmanuel Dauda-Shelika, Nyamkpa Iɓ, hari inda suka ƙone kayayyaki da ke gidan da suka haɗa da wata mota. Masarautar wacce ke gida mai lamba 306, New Layout, Lokoja, a cewar Kamfanin Dillancin Labarai na ƙasa, NAN, an kai mata harin ne da misalin ƙarfe 1 na dare a ranar Asabar. Wannan al’amari ya faru ne a daidai lokacin da ƙungiyar ‘yan asalin ƙabilar Nupe ke shirin gudanar da taro karo na biyu…
Read More
DMCSA za ta haɗa hannu da NDLEA don yaƙi da miyagun ƙwayoyi

DMCSA za ta haɗa hannu da NDLEA don yaƙi da miyagun ƙwayoyi

Daga RABIU SANUSI a Kano Hukumar Samar da Magunguna da Kayan Aikin Asibiti ta Jihar Kano, DMCSA ta nemi haɗin kan Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa, NDLEA reshen Kano don yaƙar mummunar ta’adar nan ta ta’ammali da miyagun ƙwayoyi musamman a tsakanin ma’aikatan gwamnati. Shugaban DMCSA, Famasist Gali Sule ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyarar aiki zuwa ofishin NDLEA dake nan Kano a safiyar ranar Litinin. Ya nuna damuwarsa sakamakon yadda shan miyagun kwayoyi ya zama ruwan-dare musamman a tsakanin matasa, a faɗin jihar. Shugaban ya ce za su yi wa dukkanin ma’aikatan…
Read More
Zan hukunta duk wanda ya karkatar da kayan noma – Gwamna Aliyu

Zan hukunta duk wanda ya karkatar da kayan noma – Gwamna Aliyu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwaman Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu ya gargaɗi ga waɗanda gwamnatin jihar ta bai wa aikin raba kayan aikin noman rani da su kauce wa ayyukan rashin gaskiya da "cin amanar da aka ba su". Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ƙaddamar da aikin raba kayan noman rani a garin Wamako na jihar ta Sakkwato a ranar Litinin. Ya ce "Ina gargaɗin ku da kakkausar murya, kada ku ci amanar da aka ba ku kamar yadda ya faru a lokacin damina. "Mun ɗauki matakan tabbatar da cewa an hukunta duk wanda ya…
Read More
Gwamna Abba ya ƙaddamar da cibiyar kula da masu cutar Sikila kyauta a Kano

Gwamna Abba ya ƙaddamar da cibiyar kula da masu cutar Sikila kyauta a Kano

Daga RABIU SANUSI a Kano A wani mataki mai ƙarfi don yaƙar ciwon Amosanin Jini, Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya ƙaddamar da wata sabuwar cibiyar lafiya mai inganci da za ta riƙa bayar da kulawa ta musamman kyauta ga masu fama da wannan cuta. Sanarwar hakan ta fito ne daga bakin Kwamishinan Lafiya, Dr. Abubakar Labaran Yusuf, yayin bikin ƙaddamar da makon kula da lafiyar uwa da jariri na biyu a shekarar 2024 a ƙaramar hukumar Kumbotso. Sanarwar da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar ta bayyana cewa cibiyar kulawar ta musamman…
Read More
‘Yan sanda sun kama mutum fiye da 30,000 tare da ƙwato makamai a 2024 – Sufeto Janar

‘Yan sanda sun kama mutum fiye da 30,000 tare da ƙwato makamai a 2024 – Sufeto Janar

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babban Sufeto Janar na 'Yan Sandan Nijeriya, Kayode Adeolu Egbetokun ya ce jami'an rundunar sun kama waɗanda ake zargi da laifuka daban-daban har mutum 30,313, sannan sun ƙwato makamai 1,984 da alburusai 23,250 a shekarar 2024. Shugaban 'yan sandan ya bayyana haka ne a taron ganawa manema labarai a ranar Talata, 24 ga watan Disamba a Abuja. A wata sanarwa da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ya ce sun bayyana nasarar da suka samu ne domin nuna irin shirin fuskantar baɗi da suke yi. Shugaban 'yan sandan ya yaba da ƙoƙarin jami'ansa…
Read More
Rundunar ‘Hunter Group’ tana gudanar da ayyukanta sau-da-ƙafa a Jihar Katsina – AC Salele

Rundunar ‘Hunter Group’ tana gudanar da ayyukanta sau-da-ƙafa a Jihar Katsina – AC Salele

Daga DAUDA USMAN a Legas Mataimakin Kwamanda na Hukumar Daƙile Aikata Miyagun Laifika ta ƙasa wato 'Hunter Gruop ko kuma Nigerian Forest Security Serɓice a taƙaice reshen jihar Katsina mai kulawa da shiyyar ƙaramar Hukumar Funtuwa, AC Usman Salele Funtuwa ya bayyana cewa a ƙarƙashin jagorancin Kwamandanta na jihar Katsina Murtala Ahmed hukumar tana ƙara samun nasarori a wajen gudanar da ayyukanta na daƙile masu aikata miyagun ayyuka marasa kyau a jihar Katsina da kewayenta gabaɗaya. AC Usman Salele Funtuwa ya bayyana hakan ne a wata zantawar su ta wayar tarho da wakilin Blueprint Manhaja a Legas dangane da wannan…
Read More
Yadda rasuwar Na’ibi Shehu ta girgiza al’ummar Musulmi a Jihar Ogun

Yadda rasuwar Na’ibi Shehu ta girgiza al’ummar Musulmi a Jihar Ogun

Daga DAUDA USMAN a Legas A ranar Lahadin da ta gabata ne al'ummar Musulmin Shagamu da na Jihar Ogun bakiɗaya suka gudanar da taron addu'ar kwana bakwai da rasuwar babban malamin nan na jihar Ogun Marigayi Malam Gambo Shehu Waddu Shagamu. Marigayi Malam Gambo Shehi Waddu Shagamu ya rasu ne a Shagamu sanadiyuar 'yar taƙaitacciyar rashin lafiya. Kafin rasuwarsa shine na'ibin limamin babban masallacin Juma'a na garin Shagamu, kuma ya rasu yana da shekaru sittin da shida, ya rasu ya bar mata biyu da 'ya'ya 16, maza shida mata goma. A cikin 'ya'yan nasa maza akwai babban ɗansa Muktar Hassan…
Read More