Labarai

Gwamna Sani ya ƙaddamar da ayyuka 12 a Kaduna

Gwamna Sani ya ƙaddamar da ayyuka 12 a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamna Uba Sani na Kaduna a ranar Talata ya ƙaddamar da hanyoyi 12 a cikin garin Kaduna. An ƙaddamar da ayyukan watanni goma bayan fara aikin a watan Fabrairu. Da yake jawabi a wajen taron, gwamnan ya bayyana cewa, hanyoyin da aka kammala za su inganta hanyoyin da za su ƙara haɗa kai da kuma samun sauƙi ga mazauna garin, manoma, masu kasuwanci, da sauran masu amfani da hanyar Kaduna da kewaye. Mista Sani ya ci gaba da cewa, sabbin hanyoyin, “za su rage lokacin tafiya, da inganta tsaro, da haɓaka kasuwanci, da kuma…
Read More
 Arewacin Nijeriya bai dogara da wani yanki ba – Sanata Ndume

 Arewacin Nijeriya bai dogara da wani yanki ba – Sanata Ndume

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Sanata Mohammed Ali Ndume, mai wakiltar Kudancin Borno, ya ce Arewacin Nijeriya na iya tsayawa da ƙafafunsa a ɓangaren tattalin arziƙi ba tare da dogaro da sauran yankuna ba. A wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, ya ce duk da cewar kowace jiha da yanki na buƙatar juna domin ci gaba, Arewacin Nijeriya ba zai ɗorawa kowane yanki nauyi ba. Ya mayar da martani ne kan wasu maganganu da ke cewa Arewa ba za ta iya tsayawa ba tare da taimakon sauran yankuna ba, kuma wai ’yan Arewa ba sa son biyan…
Read More
Muna fata ‘yan kasuwa su yi koyi da Ɗan’aggo wajen cigaban kasuwanci – Hon. Sa’idu Uba

Muna fata ‘yan kasuwa su yi koyi da Ɗan’aggo wajen cigaban kasuwanci – Hon. Sa’idu Uba

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano An yaba wa Alhaji Lawwali Dan'aggo bisa irin karamci da ya nuna na soma bai wa waɗanda tun farko suke zaune a wajen da aka gina katafaren rukunin kantuna na ɗan'aggo wani babban a ɗan kasuwa a Kano kuma tsohon kakakin majalisar kansiloli na ƙaramar hukumar Nasarawa. Hon. Sa'idu Uba Ahmad Abiola ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai a Kano. Ya ce babu abinda za su ce da Alhaji Lawwali ɗan'aggo sai dai addu'ar Allah ya saka masa da alkhari, domin ya gina wajen kasuwanci na ɗan'aggo da kyakkyawan nufi na alkhairi…
Read More
Yadda ‘yan bindiga suka sace abincin Kirsimeti a Kaduna

Yadda ‘yan bindiga suka sace abincin Kirsimeti a Kaduna

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja ’Yan bindiga sun ƙwace wa wani magidanci kayan abinci da lemon kwalba da ya saya domin bikin Kirsimeti a yankin Gidan Abe na ƙaramar Hukumar Kachia a Jihar Kaduna. Wani basaraken ƙauyen ya tabbatar wa wakilinmu cewa cewa a ranar Asabar ’yan ta’addan suka kai wa mutumin hari suka ƙwace kayan abincin Kirsimetin. Ya bayyana cewa mutumin yana hanyar dawowa ƙauyen Gidan Abe daga sayo kayan buhun shinkafa da kayan miya da sauransu a Katari ne maharan da ke kan babura suka tare shi da bakin bindiga. Basaraken ya bayyana cewa bayan ƙwace duk…
Read More
Kotu ta wanke mutum 888 daga zargin ta’addanci

Kotu ta wanke mutum 888 daga zargin ta’addanci

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa kotu ta wanke tare da sallamar mutanen ne bayan an gurfanar da su a cibiyar tsaron waɗanda ake zargi da aikata ta’addanci da ke Kainji a Jihar Neja. Daraktan Gurfanarwa na Gwamnatin Tarayya, Muhammad Abubakar Babadoko, ya ce an wanke mutanen ne daga cikin rukuni shida na waɗanda ake zargi da suke tsare a cibiyar. Ya bayyana cewa daga shekarar 2017 zuwa yanzu mutum 1,743 ne aka gurfanar a cibiyar kan zargin ta’addanci. Babadoko ya ƙara da cewa daga cikin adadin, kotu ta yanke wa sama da mutum 200…
Read More
Janye takunkumin haƙar ma’adanai a Zamfara zai bunƙasa tattalin arziƙin Nijeriya – Matawalle

Janye takunkumin haƙar ma’adanai a Zamfara zai bunƙasa tattalin arziƙin Nijeriya – Matawalle

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Karamin ministan tsaro, Bello Matawalle, ya ce, Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya amince da janye takunkumin hana haƙar ma’adanai a jihar Zamfara domin haɓaka tattalin arziƙin Nijeriya. Ministan ya bayyana hakan ne a yayin wani zaman cin abinci da aka shirya wa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC reshen jihar Zamfara a Gusau a ranar Lahadi. Matawalle ya ce, hikimar janye takunkumin shi ne ba da dama ga masu zuba hannun jari daga ciki da wajen ƙasar nan shiga harkar ma’adanai a jihar. Haka kuma kasancewar jihar na da tarin ma’adanai a ƙasa,…
Read More
Zargin ta’addanci: Kotu ta bayar da umarnin gabatar da Shugaban Miyetti Allah

Zargin ta’addanci: Kotu ta bayar da umarnin gabatar da Shugaban Miyetti Allah

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Babbar Kotun Birnin Tarayya, ta umurci Antoni Janar na Tarayya (AGF) da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), su gabatar da Shugaban Miyetti Allah Kautal Kore, Bello Bodejo, a gaban kotu. Mai Shari’a Mohammed Zubairu ne, ya bayar da wannan umarnin a ranar Talata. Ya ce a gabatar da Bodejo a ranar Litinin, 30 ga watan Disamba, domin sauraron ƙarar da ta shafi haƙƙinsa na doka. Lauyan Bodejo, Reuben Atabo (SAN), ya ce tsare Bodejo ya saɓa wa wasu sassa na Kundin Tsarin Mulkin Nijeriya da dokokin kotu. Ya kuma nemi izinin kotu don…
Read More
PCAACC ta karrama matashin da ya tsinci dala 10,000 a Kano

PCAACC ta karrama matashin da ya tsinci dala 10,000 a Kano

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Hukumar Karɓar Koke-Koke da Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Kano ta karrama Awwal Dankode, ma’aikacin filin jirgin saman Malam Aminu Kano, da lambar yabo bayan ya dawo da dala 10,000 da ya tsinta a cikin jirgin sama. Dankode, tare da wasu mutum bakwai, an karrama su a matsayin gwarazan yaƙi da cin hanci a wani taro na musamman da aka gudanar a Kano don murnar Ranar Yaƙi da Cin Hanci ta Duniya. Dankode ya bayyana cewa lokacin da ya tsinci kuɗin, ya ga dacewar mayar da su, haka ne ya sa ya yanke…
Read More
Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu, ya zaftare wa Lamiɗo faɗin ƙasa a Adamawa

Fintiri ya ƙirƙiro sabbin masarautu, ya zaftare wa Lamiɗo faɗin ƙasa a Adamawa

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri a ranar Litinin ya sanar da ƙirƙiro da ƙarin manyan masarautu bakwai, jihar yanzu tana da manyan masarautu 14 kenan. Hakan ya rage wa Lamiɗon Adamawa, Mustapha Barkindo, yanki daga ƙananan hukumomi takwas zuwa huɗu – Yola ta Kudu, Yola ta Arewa, Girei da Hong. Sabuwar dokar kuma tana nufin Sarkin Mubi, Abubakar Isa-Ahmadu, yanzu yana da ƙananan hukumomi biyu a masarautarsa ​​- Mubi ta Arewa da Mubi ta Kudu, daga biyar. Masarautun Adamawa da Mubi, masarautu ne da mafi yawan mutanenta Fulani. Sabbin masarautun sun haɗa da masarautar…
Read More
Gwamnan Jihar Katsina ya ƙaddamar da rabon kayayyakin noma ga manoma

Gwamnan Jihar Katsina ya ƙaddamar da rabon kayayyakin noma ga manoma

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, ya ƙaddamar da rabon injinan noma na hannu guda 4,000, famfunan ruwa masu amfani da hasken rana guda 4,000, da buhunan takin zamani guda 48,000 ga manoma a faɗin jihar.  Taron ya gudana a ranar 23 ga Disamba, 2024, a Dandalin Jama’a na Fadar Gwamnati, Muhammadu Buhari House, Katsina. A jawabinsa na maraba, Kwamishinan Ma’aikatar Noma ta Jihar Katsina, Farfesa Ahmad Mohammed Bakori, ya jero wasu daga cikin ayyukan bunƙasa noma da gwamnatin Radda ta aiwatar don inganta aikin gona. Ya kuma jinjina wa Gwamna Dikko Raɗɗa a…
Read More