28
Dec
Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja An kama mambobin ƙungiyar da ake zargin ‘yan tawayen Ambazonia ne a wani otel dake ƙaramar hukumar Takum ta jihar. Dakarun Burged ta 6 na rundunar sojin Nijeriya dake shiyya 3, masu aikin wanzar da zaman lafiya mai taken “Operation Whirl Stroke, sun kama mambobi 4 na kungiyar ‘yan tawayen Ambazonia daga jamhuriyar a Kamaru a jihar Taraba. An kama mambobin ƙungiyar da ake zargin ‘yan tawayen Ambazonia ne a wani otel dake ƙaramar hukumar Takum ta jihar. Sakamakon samun sahihan bayanan sirri a ranar 18 ga watan Disamban da muke ciki, dakarun sun…
