27
Dec
Daga RABIU SANUSI a Kano Rundunar 'yan sandan Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin CP Salman Dogo Garba ta yi nasarar gano wa su mashinan adaidaita sahu guda biyu tare da miƙa su ga asalin masu su. Wannan na ƙunshe ne a wata sanarwa da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar ga manema labarai a ranar Juma'ar nan. Sanarwar tace gano ababen hawan guda biyu na da nasaba da haɗa wata tawaga na masu binciken sirri daga cikin jami'an rundunar tasu a wani ɓoyayen guri da ke Ƙaramar hukumar Ɗambatta da ɓarayin suke a ranar tara ga wannan wata na…
