Labarai

An rantsar da shugabannin LPG na Kano

An rantsar da shugabannin LPG na Kano

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano Ƙungiyar masu sana'ar sayar da iskar gas ta ƙasa reshen Jihar Kano, ta rantsar da sababbin shugabannin ƙungiyar Liquefied Petroleum Gas Retailers, ƙarƙashin shugabancin Kwamared Omede Mohammed, wanda zai ja ragamar ƙungiyar LPG ta ƙasa reshen Jihar Kano a wannan lokaci a wani taro da aka yi a makon da ya gabata a birnin Kano.A jawabinsa bayan rantsuwar Omede Mohammed ya yi alƙawarin shugabanci nagari daidai gwargwadon iko a matsayin wanda aka ɗorawa nauyin shugabancin, kuma zai haɗa kai da ɗaukacin shugabanni da shugabannin wannan ƙungiya domin yin aiki na cigaban 'yan ƙungiyar da sauran…
Read More
Yunwa da gazawar gwamnati ne sanadin turmutsutsi wajen rabon abinci — Kukah

Yunwa da gazawar gwamnati ne sanadin turmutsutsi wajen rabon abinci — Kukah

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja Bishop Matthew Hassan Kukah na Cocin Katolika da ke Jihar Sakkwato, ya ɗora alhakin turmutsitsin da ys auku a Abuja, Oyo, da Anambra kan gazawar gwamnati wajen magance yunwa da fatara a Nijeriya.Ya bayyana haka ne yayin isar da saƙon Kirsimeti, inda ya ce duk da samun ‘yancin kai sama da shekaru 60, Nijeriya har yanzu tana fama da cin hanci, bambancin ƙabilanci, da rashin ci gaba mai ma’ana.“Turereniyar da ta faru a wuraren rabon abinci a Okija, Ibadan, da Abuja abun takaici ne kuma shaida ce ta irin yanayin ƙunci da ake ciki,”…
Read More
An yi kira ga gwamnatin Katsina ta riƙa tantance malamai masu koyar da maniyyata

An yi kira ga gwamnatin Katsina ta riƙa tantance malamai masu koyar da maniyyata

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina Shugaban kwamitin da ya lura da aikin Hajji da ya gabata(Amirul Hajj),Alhaji Tukur Ahmed Jiƙamshi ya yi wannan kira lokacinda yake gabatar ma gwamna Dikko Raɗɗa rahoton kwamitin kan aikin Hajji na 2024. Ya ce domin kaucewa matsalolin a nan gaba, ya kamata gwamnatin ta lura da malaman da take turawa domin taimakawa alhazzai wajan gabatar da ibadar su. A cewar shugaban kwamitin,mafi yawan malaman da ake turawa musamman na ƙananan hukumomi su kansu basu san aikin ba. Ya kuma shawarar ci gwamnati da ta ƙara sa ido wajan tantance maniyata saboda akan sami yan…
Read More

Gwamnan Jigawa ya rasa ɗansa kwana ɗaya bayan rasuwar mahaifiyarsa

Daga IBRAHIM HAMISU Gwamnan jihar Jigawa Malam Umar Namadi ya rasa ɗansa mai suna Abdulwahab Umar Namadi, wanda ya bar duniya da yammacin yau Alhamis sakamakon wani mummunan hatsarin mota da ya afku a kan titin Dutse zuwa Kafin-Hausa. Ana kuma gudanar da jana'izarsa a garin Kafin Hausa kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar. Marigayin mai shekaru 24, shi ne babban ɗan gwamnan inda ya rasu ya bar iyayensa da ƙannensa maza da mata . Hajiya Maryam Namadi mahaifiya ce ga Gwamnan na Jigawa wadda ita ma ta rasu a jiya Laraba, bayan ta yi fama da gajerar rashin lafiya…
Read More

Rahoton IMF na 2024 ya cire Nijeriya daga ƙasashe 10 da suka fi tarin bashi

Daga BELLO A. BABAJI Sabon rahoton jami'an Hukumar Bayar Da Lamuni Ta Duniya (IMF) ya nuna ƙasashen Afrika da aka fi bi bashi a shekarar 2024 inda ya bayyana ƙasar Misira a matsayin wacce take da mafi girman kaso a Nahiyar da ya zarce Dala biliyan 9. Rahoton ya nuna cewa a tsakanin watan Janairu zuwa Yuni na wannan shekarar, gwamnatin Nijeriya ta biya sama da Dala biliyan 2.24 na basussukan da ake bin ta wanda ya fitar da ita daga ƙasashen da bashi ya yi musu katutu. Rahoton da kfishin kula da basussuka na Nijeriya ya fitar ya nuna…
Read More
KAROTA ta gurfanar da mutane uku da ake zargi da cin zarafin jami’anta

KAROTA ta gurfanar da mutane uku da ake zargi da cin zarafin jami’anta

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano Hukumar kula da zirga zirgar ababen hawa ta Jihar Kano KAROTA, ta gurfanar da wasu mutane uku, da ake zarginsu da cin zarafin jami'anta yayin da suke tsaka da gudanar da aikinsu. Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar ta KAROTA Nabulisu AbubakarK/ Na'isa ya aikewa manema labarai yace, waɗanda hukumar ta gurfanar gaban kotun sun haɗa da Abubakar Mustapha, Najib Idris, da kuma Faruk Ɗan Alhaji An dai gurfanar da waɗannan mutane a gaban kotun Nomanslands mai lamba 47, dake unguwar Sabon Gari. Bayan gurfanar da mutanen da ake zargin a gaban…
Read More

Tinubu ya yi ta’aziyya ga gwamnan Jigawa kan rasuwar mahaifiyarsa

Daga BELLO A. BABAJI Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aika da saƙon ta'azzarsa ga Gwamna Umar Namadi na Jihar Jigawa bisa rasuwar mahaifiyarsa, Hajiya Maryam Namadi. A safiyar ranar Laraba ne marigayiyar ta rasu, wadda aka yi jana'izarta a garin Kafin Hausa inda nan ne mahaifar gwamnan. NAN ya ruwaito cewa, wata sanarwa daga Fadar shugaban ƙasa ta ce Shugaba Tinubu ya yaba da irin ƙoƙarin da marigayiyar ta kasance tana yi wa al'umma na kyautatawa sadaukarwa inda ya yi kira ga iyalanta da su cigaba daga inda ta tsaya. Shugaban ya kuma yi kira ga gwamna Namadi da sauran…
Read More
‘Yan ta’adda sun kai hari sansanin sojoji a Borno

‘Yan ta’adda sun kai hari sansanin sojoji a Borno

A ranar Litinin, 24 ga watan Disamba, 2024, an sami rahoto cewa wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne sun kai hari kan sansanin sojoji da ke Damboa, a Jihar Borno. Bisa bayanan da Blueprint ta tattara, harin ya auku ne da yammacin daren Kirsimeti, lokacin da jiragen yaƙi marasa matuki, ɗauke da bama-bamai, suka kai farmaki kan sansanin sojojin. Aƙalla sojoji shida sun samu raunuka sakamakon harin, kuma an basu agajin gaggawa a wajen kafin a ɗauke su zuwa ga asibiti domin ƙarin kula. Harin ya fara ne da harbe-harbe daga masu tayar da ƙayar baya, wanda sojojin…
Read More
Hatsarin jirgin sama ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama

Hatsarin jirgin sama ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama

Wani jirgin fasinja mai ɗauke da mutane 67 daga Azerbaijan zuwa kudancin Rasha ya faɗi a kusa da birnin Aktau na Kazakhstan a ranar Laraba, 25 ga Disamba. Rahotanni daga CNN sun bayyana cewa ma’aikatar harkokin gaggawa ta Kazakhstan ta tabbatar da faruwar hatsarin, inda ta ce tawagoginta sun tarar da jirgin yana ci da wuta a wurin da ya faɗi. Ma’aikatar ta ce, “Masu bada agaji na gaggawa sun fara kashe wutar. A halin yanzu, ana tantance bayanai game da waɗanda abin ya shafa, kuma a cewar bayanai na farko, akwai waɗanda suka tsira.” Jirgin yana ɗauke da fasinjoji…
Read More
An yanke wa ‘yan luwaɗi hukuncin shekaru 100 a gidan kaso a Amurka

An yanke wa ‘yan luwaɗi hukuncin shekaru 100 a gidan kaso a Amurka

Daga USMAN KAROFI Wasu ma’auratan jinsi ɗaya, William da Zachary Zulock, sun samu hukuncin ɗaurin shekaru 100 babu yiwuwar beli a jihar Georgia, Amurka. Ma’auratan sun yi laifin yin amfani da ‘ya’yan su maza guda biyu wajen aikata fyaɗe da kuma kirkirar hotunan batsa. Yaran biyu, ‘yan shekaru 12 da 10, an ce sun fito ne daga wata cibiya ta musamman ta Kiristoci da ke kula da marasa lafiya. William ya kasance ma’aikacin gwamnati yayin da Zachary yake aiki a banki. Rahotanni sun bayyana cewa ma’auratan suna tilasta wa yaran yin ayyukan batsa tare da ɗaukar bidiyo da hotuna don…
Read More